Kainuwa......8

7K 493 25
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼*

*8*

Shiru shiru ba sarki ba labarinsa wanda hakan ya kara d'agama Amadu rai gashi lokacin Basira cikinta yakai wata 9, ganin kar Basira ta haihu ba tare da sarki yasan komai ba yasa Amadu ya shirya tsaf ya nufi garin Zariya a akuri kura.

Sai yamma liss suka isa, gidan Sarki ya wuce.

A b'angaren Mai Martaba kuwa aiyuwa sun cab'e mai a fada wanda ya rasa yanda zaiyi, yaso ya aika aje q dubo Basira sai dai Barde ya bashi shawara akan ya kara jinkirtawa ganin kar a gane tsananin san da yake mata wanda kan iya jawo mata tsangwama in ta dawo.

Yau ma kamar kullum yana zaune a fada ana ta fama kawo kara yana hukunci, wasu kuma neman taimako suka zo yi wasu kuma sulhu da dai sauransu, ganin yamma tayi sosai yasa ya sallami kowa akan a dawo gobe, shigowar bafadansa ne yasa ya kalleshi, bafadan ya sanar dashi zuwan Abokin nasa kuma sirikinsa, nan ya bashi izini da sauri.

Amadu ya shigo kansa na kasa sai daya gaidashi tukunna, Sarki ya nemi a basu guri, suna fita ya kalli Amadu yace " Amadu ka jini shiru ko? Wlh al'amura ne suka c'abe min gaba d'aya.

Amadu yace bakomai sannan ya d'ura da cewa " dama zuwa nai na sanar dakai Basira ta shiga watan haihuwa."

Mamaki ne ya kamashi wanda sai da ya bayanna a kan fuskarsa yace "Haihuwa kamar ya?"

Amadu yai murmushi yace "ai cikin bai zube ba."

Mikewa yaga Sarki yayi da sauri ya shiga matse hannayensa yama rasa mai zaiyi can ya matso jusa da Amadu ya d'agashi tsaye ya rungumeshi kam yace " Basira ta kusa haihuwa kenan?"

Amadu yai murmushi yace "kwarai kuwa dan tama shiga watan, haihuwa yau ko gobe, nima sai da Matata ta sanar dani ta kula Basira ta kusa haihuwa sannan nace to ya zama dole yanzu kam inzo in sanar dakai."

Abin mamaki kwalla ne ya taru a idan sarki hannu ya d'aga ya shiga godema Allah.

Abin mamaki fadawa da bayinsa dake waje nan a ka fara zamewa kadan kadan an tafi kai gulma (lol.....)

Sarki yace "aikam yanzu dakai zamu tafi muje in d'aukota."

Amadu yai dariya yace " kai da kake fama da aiki sai dai ka tura kawai a d'aukota."

Shiru yai yana tunani can yace " ka kwana anan zuwa gobe zansan yanda za'ai."

Magajiya na zaune zance ya zo mata, tashin hankalin da ba'a kwatantashi, ba shakka tashin hankalin data shiga ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi tunani tana tsaye jitau jiri ma na neman d'ebanta, Hisham kam ba kanta dan kuwa magana ra baci, tsantsan tashin hankalin da ya shiga ya wuce misali.

Gun Magajiya ya taho a sukwane, sunyi jugum jugum su biyu a d'aki, can Magajiya tai d'an ajiyar zuciya sannan ta kalli Hisham tace "duk laifinka ne, kaine ka tabbatarmin maganin nan ba karya ko wasa a ciki."

Hisham yai shiru can yace " duk ba wannan bane abinyi yanda zamuyi yanzu shine abinyi."

Magajiya tai shiru tana tunani, Hisham yace " bafa zai yiwu mu bari a haifi yaron nan ba in ma mace ce da sauki to amma ina muka sani?"

Magajiya cikin kufula tace " aikin gama ai ya riga ya gama kanaji ance ta shiga watan haihuwa?"

Da sauri Hisham yace " to sai me? Ai ko haifarsa tai sai mu halakashi."

KAINUWA....Where stories live. Discover now