Kainuwa......2

9.4K 604 16
                                    

🕊 *KAINUWA* 🕊
_........Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*Haske Writer's Association*

*Na Ayusher Muhd*

*2*

Shiru Sarki yai yana nazari bayan fitar abokinsa, baiyi zato ba sai jin muryar Aminin nasa yai a kusa dashi alhalin ya dauka ya tafi.

Amadu yace " Amma Mai Martaba ba matanka hud'u ba?"

Idanunsa ya bud'e ya saukesu akan Amadu sannan yace " Amadu kaje ka sanar da Barde ya kaika gida, ni kuma gobe zanzo."

Jin haka yasa Amadu ya fita jiki a sanyaye, Mai martaba yai shiru tare da maida idanunsa ya rufe, ya dade a haka kafin ya bud'e idanunsa sannan ya kira wani bawansa ya sanar dashi akan ya kira masa kaninsa wanda suke uwa da uba daya.

Bai dade da fita ba sai gashi ya dawo shi kuma kanin nasa Kamal na biye dashi a baya.

Yana shiga ya saki fuska tare da cewa " Mai Martaba ina can ina hawan doki ka aika a kirani, Allah yasa ba matsala bane."

Abdulsamad ya tattara hankalinsa kan kaninsa yace " Kamal yanzu ace na baka mata zaka aura?"

Kai ya d'aga mai alamar eh sannan yace "ko ma wace iri ce in har ba mara da'a bace ko wacce ta lalata tarbiyarta da darajarta a waje ba."

Sarki yai shiru kafin yace " in kuma d'aya daga cikin wacce ka lissafo baka so ne fa?"

Kamal yai murmushi kafin yace " maganar gaskiya zan aureta in har umarnine daga bakin Sarki sai dai in har umarnine daga bakin yayana bazanyi ba gaskiya."

Ya dade yana kallan Kamal kafin ya saki dan kasaitacen murmushi yace " ya! kaje gun d'an naka?"

Kamal ya washe baki yace " Abdulmalik yana can yana bacci amma yau kam zai yi kwanciyar gajiya, ai yau kowa na cikin farincikin magajin sarki."

Sarki ya kara fad'ada murmushinsa yana jin dadin kasancewarsa uba kafin ya sallami Kamal.

Bayan fitar kamal ne yai shiru yana tunani ( _a yanda tarihi yake mata guda hudu ne kamar yanda musulunci ya umarta mana sai dai akwai kwarkwara wanda suke zama matan sarki in anci garinsu da yaki ko kuma makamancin haka sannan su wad'an nan basu da gadon sarki in ya mutu_)

Lalai yau ya yanke hukunci ba tare da yasan mafita ba sai dai yayi hakan ne saboda tunanin kare mutuncin aminin nasa.
Matarsa ta karshe ko ince Amaryarsa wacce ya aura a waccan shekarar ita yake tunanin rabuwa da ita badan komai ba sai dan rashin san auransa da takeyi shi kansa yasan tauye mata hakki mahaifanta sukai gun bashi ita, yarinyace 'yar shekara 9 mahaifinta yayane ga sarkin Daura wanda sunyi hadin auren ne a san ransu, ace shi yana shekara 40 amma an bashi yar shekara 9 ai kowa yasan hakkinta aka tauye shi yasa ko tunanin nemanta bai taba yi ba.

Da wannan shawara ya mike tare da ba bayinsa izini akan yanasan a kira Magajiya zuwa turakarsa

**********

Magajiya kam tana zaune sai shigowa ake yan suna ana mata barka, ba amsa wa take ba sai kai kawai da take kadawa cikin isa da takama, tayi shiga na alfarma dan Magajiya 'yar gayu ce, ta iya kwalliya ta kuma iya sa kayan alfarma.

A ranta wani irin nishad'i takeji tabbas tana cikin tsantsan farin ciki dan saura kiris burinta ya cika, wannan burin nata kuwa bai wuce ace d'anta Abdulmalik ya hau mulkin garin na Zazzau ba.

Wata baiwar ta ce ta iso kusa da ita ta rada mata a kunne sakon Sarki, idanu ta juya tare da d'an yin karamin tsaki a ranta, itafa batasan takura akan mai shi baxai zo inda take ba sai dai ace wai taje? A duk sanda akace mata taji turakar sarki ji take kamar tafi karfin a dinga sata a bu.

KAINUWA....Where stories live. Discover now