Kainuwa.....68

5.6K 472 26
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼*

*68*

Khadija ce ta karasa ciki ta zauna sannan ta gaisheshi.
Kallanta yai yace " Khadija meye tsakaninku da yaran can?"

Kallansa tai sannan tai kasa da kai.
Yace " Khadija me kike tunani? Kinaso kicemin yaran da na tsana shi kike so? A ma bar maganar so tunda nasan dama Kina sanshi amma me kike nufi da aurensa?"

Khadija a ranta tace " abinda nasan bazai taba yiwuwa ba kenan."
Amma a fili tace " Ya Abdulmajid."

Cikin fada yace " kinaso ki je gidan sarauta a matsayin kishiyar Gimbiya? Sannan a matsayin matar wancan yaran?"

Khadija ta kalleshi tace " Yaya wai me yasa ka tsaneshi da ya wa haka?bayan bai taba yima komai ba?"

Abdulmajid ya kalleta cikin b'acin rai yace " na tsaneshi, kallansa ma ba san yi nake ba, duk duniya shine mutum na farko dana tsana."

Khadija batasan sanda tace " bayan shine ya kamata ya maka wannan tsanar?"

Yace " mene?" khadija ta kalleshi tace "Yaya please ka dinga sa ruwan sanyi a ranka, in har wannan karamar maganar ta b'ata ma rai ya zakayi in babbar magana ta doki kunenka?"

Yace " babbar magana? Wacce iri kenan?"

Juya kai tai da sauri tace " ina dai fada ne saboda ni banga abin jin haushi a maganar ba."

Abdulmajid ya mike a zuciye yai waje ko zobon baisha ba.

Kanta ta dafe tare da rufe idanunta.
Hisham kam yana d'aki yana cire Babbar riga Umma ta shigo bakin nan nata a washe, tace "wai ya akai ya biyoka?"

Yace " sai ki rufe bakin ai, kin wani baje baki kamar yau kika taba ganinsa.

Kasa tai da kai tana murmushi.

Hisham ya shiga band'aku dan kama ruwa, yana fitowa yai falo inda Abdulmajid yake.

Me zai gani?"

Ba kowa a falon, da sauri ya fito yana kiran Khadija.
Fitowa tai daga d'aki tace " gani."
Cikin tsawa yace " ina Abdulmajid?"

Tace ya tafi.
Yace " ban gane ba?"
Shiru tai dan batasan me zata ce ba.
Waje yai da sauri cikin tashin hankali.
Umma ce ta karaso gunta tace " Me kika ce masa da har zai tafi ba ko sallama? Yanzu khadija bawan Allahn nan bai taba zuwa fa gidan nan ba sai yau, amma ki koreshi? Ta ya ya zaki......"

Kasa karasawa tai, Khadija cikin tausaya mata tace "kiyi hakuri Umma amma ba korarsa nai ba."

Umma tai shiru kafin tai ciki.
Khadija ta bita da kallo cikin tausayawa.

Abdulmajid yana fita yai gida.
Har zaiyi bangarensa aka sanar dashi kiran Magajiya.
Yana shiga ya taddata a tsaye da alama yawo take a tsakar falon.
Shiga yai ya kalleta yace "Umma ga......"
Wani wawan mari da ta sakar mai ne yasa ya kasa karasawa, tace " Uban me kaje yi gidan Waziri?"

Kasa magana yai sai kuncinsa kawai daya rike yana kallanta.
Magajiya ta kara hasala tace " wato bakajin maganata ko? Na d'auka na sanar dakai ba kai ba keb'ewa da yaya? Wato shine har da zuwa gidansa ko? Ka nunamin yafini matsayi a gunka ko?"

Abdulmajid yai shiru, tace " fitarmin daga falo, sannan wlh karka kuskura inkarama magana akan wannan zancen, na fadama."

Abdulmajid yai waje jiki a sanyaye, mota ya fada ya ja ta da gudu yai waje.

Abu Turab na kallan sanda ya fita, ba shakka yasan Magajiya ta haushi da fada ne, a fili yace " am sry, sai dai kaima kayi abubuwa marasa dacewa wanda dolene kaima kaji ba dadi."

Juyawa yai ya koma b'angaren sa.
Har zai zauna ya fito ya nufi bangaren Umma.

Tana zaune tana ta raba cingam ya shiga.

Yace " Umma amma dai harda 'yan katsina zaki aikama ko?"
Tace " kanaso kenan bikinka ya lalace daga biki zuwa gulma, gulmar da zata zama silar rugujewar komai."
Turab ya kalleta yace " Kina tunanin zasuyi zancen anan?"

Tace " Abu Turab kenan, bakasan mutane ba, kai a ido ne zaka ga kamar 'yan uwa ne amma a zahiri ba haka bane."
Kallanta yai sai dai baice komai ba, a kasan ransa shikansa yana san yaga 'yan uwansa.
Basira ta cigaba, kun had'u da Mai Martaba?
Yace " a'a."
Tace shikenan.
Kallanta yai cikin kulawa yace " lafiya dai ko?"
Tace bakomai.

********

Abdulmajid kam bai tsayar da motarsa ba sai a kofar gidansu Mairo, kallan kansa yai a madubi yace " baka da inda zaka sai nan?"

Kofar gidansu ya kalla sannan ya kwantar da kansa jikin sityarin motar ya dade a haka kafin ya tada motar yai gaba.

Yayanta ne ya shigo lokacin taba tsinke alayahu.
Yace " Yauma kin fita kikai?"
Mairo tace " infita zuwa ina?"
Harararta yai yace " wlh ki kiyayi kanki da wulakanta mutum, mutum ma irin Yarima wanda kalma d'aya zai iya sa rayuwar gidan nan ta ruguje, tun dazu bawan Allahn nan yake waje har ya gaji yai gaba."
Baki ta tabe tace " ni bai aikomin ba dan bansan yazo ba."
Ciki yai tare da yin kwafa.
Mairo ta cigaba da tsinke alayahunta, can tace " me ya kawoshi da ranar nan? Sannan bai aiko ba?" tsaki tai tace " damuwarsa ce."

************

Washegari kuwa Magajiya tasa aka kira mata Hisham, yana shiga ta rufeshi da fada kai kace itace uwarsa ba ma yayarsa ba balle kuma kanwa.

Ganin abin ya zo mai wuya yasa yace " Wai Magajiya inada tambaya."
Yaran nan da kike fada akansa na waye?"

Tashin hankalin da ba'a misaltawa.
Idanunta kadai sun isa su nuna maka tsantsan tashin hankalin da take ciki, tace " Yaya?"
Yace " kwarai ni yayanki ne, sai dai abun ya isa haka, akan yaran nan yaje gidana zaki sani a gaba da fada haka? Cinyeshi nai a gidan nawa ko me?"

Kallan mamaki takemai yanzu, yauce rana ta farko da Hisham yake maida mata murtani.
Tace " yaya ni kake fadawa magana?"
Yace " an fada miki d'in, duk yanda naso in kyautata miki na kula bakya gani, yanzu kwata kwata kin zama sai a hankali komai fada, ina Magajiyar da na sani wacce tsoro baya cikin zuciyarta?"

Tace " nikaina bansan meke damuna ba Yaya, sai dai tundaga sanda yaran can ya ce yasan sirrina nakejin kamar komai na rayuwata xai ruguje, yaya ka taimakeni ka kashe yaran nan da uwarsa, ni har itama banasan gani ba shi ba."

Hisham yace " in taimakeki? Duk abinda kike min?"
Tace " amma ai kai kasab burina ko? Dolene mu kawar da duk wata matsala da zata kawo mana kai akan nad'a yaran nan mulki."

Hisham ya kalleta a ransa yace "Magajiya kenan, zanyi duk abinda kikeso saboda d'ana, sai ya hau mulki in shekaki kema barzaho."

Hannu ya saka zai murd'a kofar shiga, abinda yaji ne yasa ya tsaya cak sai jikinsa da hau tsuma saboda tsananin tsoro da razana.

Magajiya ce ta katseshi tare da cewa " yaya."
Kallanta yai bai amsa ba.
Tace " na fasa kashe basira, mai kake gani in muka haukatata?"

Hisham yace " hauka?"
Tace kwarai " idan muka halaka Turab a ranar auransa ita kuma sai musa a haukatata kaga sai ace rashin d'anta ne yasata yin haukar."

Hisham ya sheke da dariya yace " gaskiya Magajiya ba digon imani a ranki, duk duniya kece mutum ta farko danasan yasan salan mugunta, ko shed'an sai dai ya sara miki."

Murmushi tai tace " ni dai yaya ka taimaken ka kyalemun yarona, wannan shi kadai ne abinda nakeson ka dashi, mu samu komai ya kammala, banasan wani abu ya tare mai hawa mulki."

Kafafunsa ne suka kasa d'aukansa da sauri ya dafa bango, dan gaba d'aya jikinsa kaurewa yake da rawa......

*Turab*

KAINUWA....Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang