Kainuwa....87

7.2K 598 107
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyan littafin nan gabaki d'aya, ina godiya kwarai da kaunar da kuke ma littafin nan, nagode da hakuri dani na rashin posting akai akai da kuke, ni kaina ba hakan naso ba.
Always love u.......

*86*

Wani irin ihu Magajiya ta saka da karfi tace " ABDULMAJID....."

Mikewa tai a zuciye ta isa inda yake, ta d'aga hannu zata zabgamai mari, da sauri Turab ya tsaya a gabanta.

Kallansa tai idanunta duk sun kada sunyi jaa, kallan juna suka shigayi, tana mai wani irin kallo wanda ba komai a ciki sai tsantsar kiyayya.
Mai Martaba idanunsa a rufe kawai suke saboda jin abin yake kawai yana mai yawo akai.
D'akin yayi tsit kowa da abinda yake sakawa a ransa, wani dogari ne ya shigo da gudu ya tsugunna, Barde ya kalleshi yace " lafiya kai kuma?"

Cikin in in na yace " mai kula da kofar gidan mai martaba ne na cikin gari."
Galadima yace " to ya akai?"
Bakinsa ya shiga motsawa ya kasa magana, Basira tace " ya akai Hadi?"

Da sauri ya ya maida kansa kasa ya sa kuka, Turab ya kalleshi ganin yanda yake kuka yasa Turab ya matsa daga gun magajiya ya taho inda yake yace " Hajiya......"
Wani kuka dogarin ya saka, da sauri Sarki ya bud'e idanunsa wanda gaba d'aya sun yi jaa, mikewa yai yana kokarin takawa baya yai da sauri dogarawan dake bayansa suka tareshi, kallansu yai sannan ya kwace jikinsa ya koma ya zauna saboda jirin da yakeji, Dogarin yace " Allah yama Hajiya cikawa yanzun nan......"

Inalilahi wa ina ilaihi raji'un......Abinda kowa dake d'akin ya shiga fada kenan, Banda Magajiya wacce take tsaye, sai Sarki wanda gaba d'aya yaji kansa ya kulle ya kasa tunanin komai.
Turab ya karasa inda yake da sauri yace " Abba!"
Idanunsa ya sauke akan Turab cikin tsananin tausayawa, ba shakka lalai bai cancanci mulkin nan ba, lalai laifinsa ne na kyale Magajiya tun farko ta dinga yin abinda taga dama.
A hankali ya fara karanto inalilahi a ransa, kallan Turab yai sannan yace " jeka zauna."
Turab ya mike ya koma gun xamansa.
Gaba d'aya d'akin yayi tsit kowa ya koma gun zamansa, Sarki ya mike tsaye tare da zare rawanin kansa ya ajiye akan teburin dake gabansa, sannan ya tako a hankali har zuwa inda Magajiya take gaba d'aya kana kallanta kasan a tsorace take, kallan ta Sarki yai ya dade idanunsa na kanta sannan ya kalli Hisham, sannan ya maida dubansa kan Abdulmajid, haka yabi kowa da kallo d'aya bayan d'aya.
Akan Barde ya tsaya yace " Barde jeka taho da gawar Hajiya."
Nan barde ya mike.
Sarki ya kalli Magajiya sannan yace " kafin in sallaci gawar Hajiya inkaita makwancinta inaso in sanar da abu d'aya kafin in yankema Matarnan hukunci, daga wannan lokacin na ajiye mukamin mulkin Masarautar Zazzau, sannan na d'aura d'ana Abu Turab a wannan matsayi, wannan matar a d'aureta da kaca itada d'an uwanta Waziri a rufaffen d'aki, sannan bazan yanke mata hukunci ba d'an da take neman ganin baya, wanda ta makantar dashi bayan neman ajalinsa, wanda ta ke neman halaka masa rayuwa a koda yaushe shine zai yanke mata hukunci da kansa, sannan na umarceshi da yanke mata hukunci mai tsaurin gaske."

Ya juya ya fara takawa kallo d'aya zakamai kasan lalai yana cikin tashin hankali.
Matan sarki ne suka mike suka bi bayansa.

Sunje zasu fita daga kofar Magajiya cikin karaji tace " KAI ABDUSSALAMAD!"

Gaba d'aya d'akin kowa juyowa yai ya kalleta tace " mene? Kaba Abu Turab mulki? Inji uban wa? Inji uban wa? Kana tunanin ni Magajiya zan yarda wannan dan tsinaniyar yahau mulki? Mafarki kukeyi daga kai har yan d'akin nan, indai har ni inada.........."

Kasa karasawa tai jin muryarta ta sarke, duk yanda tai gun yin magana ta kasa, tsugunnawa tai da sauri tare da rike wuyanta, a hankali kowa na d'akin ya fita wannan abu yafi komau yi mata ciwo, balle tana kallan Abdulmajid Khadija ta turashi a kekensa sunyi gaba, ga magana ta tsaya cak.
Masu tsaro ne sukazo inda take rike da kaca, Hisham aka fara sawa kaca, kallan Magajiya yai yace " Allah ya isa tsakanina dake, shawararki itace tasa zuciyata ta rikid'e gaba d'aya, sannan maganarki bazata taba d'aowa ba wannan rana itace rana ta karshe da kikai magana da bakinki, domin kuwa inbaki mantaba da gubar da kikasha danyima Basira sharri, a lokacin dana amshi wannan gubar dama ansanar da sharad'inta, bata fita duka a jiki sannan kar babba wanda ya wuce shekara 45 yasha wannan gubar sannan duk sanda ran wanda yasha gubar nan ya baci sosai to xata cigaba da mai illa ta cikin jikinsa, sannan idan tai nisa xata jawo kurmancewa, sannan zata nakasa gab'obin jiki."

KAINUWA....Where stories live. Discover now