Kainuwa.......76

6.4K 609 84
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*76*

Washegari.

Da asuba ya farka a kan kasan carpet din daya kwanta, salati yai sannan ya mike tare da kallan kan gadon da Gimbiya ke kwance, karasawa yai inda take ya gyara mata bargon data luluba dashi, sannan ya juya zai fita.

Jiyai ta kamo hannunsa, juyowa yai ya kalleta yace " idanki biyu?"
A hankali ta bud'e idanunta tace " yanzu dai na farka? Masallaci?"
Yace " eh, sai na dawo."
Sakeshi tai sannan tace " adawo lafiya."

Murmushi yai sannan ya juya yai gaba.

Alwala yai sannan ya fita, sun idar da sallah ya fito, jiyai ance " Yarima Turab!"
Yanda aka kirashi cikin rad'a yasa ya juya ba tare da ya amsa ba dan ganin me kiran.
Daga lungu ya hangoshi a tsaye jikin bango.
Turab ya karasa sannan ya kalleshi cikin mamaki yace " Waziri lafiya?"

Hisham ya kalleshi duk ya canza yace " Kaga Khadija?"
Turab yace " bangane naga khadija ba? Wannan wace irin tambaya ce?"

Hisham a rikice yace " Turab?"
Ya fada tare da riko hannayensa yace " ka taimakeni dan Allah bansan inda Khadija tai ba, tun jiya nake nemanta wlh ko barcin arziki ban samu ba."
Turab kallan mamaku yake masa yace " Ni fa nakasa fahimtarka, b'ata tai ko me?"
Hisham yace " da kanta ta tafi, sai dai bansan inda tai ba."
Turab ya kwace hannunsa yace " da kanta ta tafi? Kuma ko kunya kazo kana tambaya ta?"
Hisham yace " Turab na rasa inda zansa kaina, in ta fada hannun mutanen banza fa?"
"wannan damuwarka ce ba tawa ba, kaine ka lalata mata rayuwa ko menene ya sameta, sannan karkaga kaine ka haifesu kayi tunanin duk wani abu da ka aikata musu ba laifi bane, haifarsu kai ba hallitarsu kai ba."
Ya juya yai gaba.

Hisham idanunsa suka ciciko dan shikam yana cikin garari.

Turab tafiya kawai yake sai dai abin zirya yake tamai a zuciyarsa, ina taje? Menene kuma dalilin tafiyarta?"

Har yaje zai shiga bangarensu sai kuma ya juya, Garzali ya kira suka wuce asibiti.

Abdulmajid na kwance yana bacci, sai wata baiwa da Magajiya ta sata zama a gunsa, d'ayan gadon ya kalla wanda da ba kowa, amma yanzu yaga Khadija kwance.

Mamaki ya kamashi yaje kusa da ita, sannan ya dawo inda Abdulmajid yake yad'an tabashi.

Sannan yace " d'an tashi."
Abdulmajid bai bud'e ido ba sai dai yana jinsa.
Turab ya kalli wannan mai kula da su din da aka bari yace " bamu guri ko?"
Tace " to ranka ya dade." tai waje

Turab ya kalli Abdulmajid yace " magana zamuyi."

Abdulmajid a hankali ya bud'e idanunsa ya kalli Turab.
Turab ya zauna kusa dashi yace " ya jikin naka?"
Baice komai ba sai dai ya kawar dakansa.
Turab cikin wata irin murya yace " Nagode Abdulmajid."
Cikin tsananin mamaki Abdulmajid ya kalleshi, sannan yace " karkamin godiya dan ba saboda kai nai ba."
Turab yai murmushi yace " saboda ba saboda ni kai ba shi yasa nake ma godiya."
Abdulmajid yace " mene?"
Turab ya ce " Mu bar wannan maganar, me ya samu Khadija?"
"kana tunanin zan fadama?"
Turab yace " sosai, dan duk duniya yanzu ni kadai ne zaka iya fadama wannan sirin naka."

Wata dariya yai yace " bakai tunanin na gwammace na had'iye matsala ta ba?"
Turab yace " wannan tsarinka ne, zaka iya yadda zakuma ka iya kin yadda, sai dai in har kanaso ka ceto rayuwar mutanen dake kewaye dakai dolene mu had'a kai."
Abdulmajid ya kalleshi sai dai baice komai ba, Turab ya cigaba " haka zakabar matar da ta rikeka ta cigaba da tafka laifufuka? Haka zaka bar mahaifin daya haifeka ya cigaba da aiwatar da laifufuka? Ko kuwa rayuwar kanwarka dake neman tarwatsewa?"

KAINUWA....Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin