Kainuwa.....7

6.5K 523 11
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _Dashen Allah_
( _*A Historical Fiction*_)

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*Na Ayusher Muhd🤸🏼‍♂*

*7*

Magajiya tasa Aunty Lami akan duk wani magani datasani ko wani mai bada magani data sani ta je ta amso mata maganin da zai kawar da wannan cikin, babu makawa sai ta sa cikin nan ya bi shada dan itakam bataga wanda ya isa ya haihu ba a gidan, dan kuwa bazata tab'a iya jurar ganin yaro na yawo a gidan ba a matsayin d'an wani ba, ba nata ba.

Basira tana kwance a d'aki tun safe ta kasa cin abinci, sallamar baiwar ta ce wato lantana yasa ta mike zaune, Lantana ta karaso ta gaidata sannan tace " Ranki ya dade Magajiya ta aiko miki da magani da kuma abinci."

Basira tace " nakoshi Lantana sam banajin cin abinci."

Lantana ta matso tace " Kinsan bazataji dadi ba in taji bakici ba kinga na jiya ma data aiko bakici ba sai dataji ba dadi."

Basira tace " to ke kici mana?"

Idanu Lantana ta zaro tace " so kike a yanken hukunci mai karfi? Magajiya ce fa ba wani ba."

Zata sake magana sai ga Aunty Lami ta shigo ba ko neman izini, tana shigowa ta matso kusa da Basira fuskarta a sake aosai tace " haba 'yata tashi ki daure kici mana, ko so kike hankalin Mai Martaba ya tashi?"

Da sauri Basira ta jijiga kai alamar a'a, Aunty Lami tasa aka kawo abincin da kanta ta bata sai dataga taci sosai sannan ta bata maganin da aka kirashi da sunan maganin dazaisa taji karfin jikinta."

Ta dade a zaune ganin Basira ma baccinta take shara yasa ta fita daga d'akin.

*******
Zaune take gaban Magajiya wacce itama shiru tai tana tunani, can Aunty Lami tace " amma Mai maganin nan na kan tudu ya rainamin hankali, sai fa daya tabbatarmin cikin minti 15 zata fara fitsari akai akai in har naga haka inbata kwana d'aya cikin zai zube dan dama nacene ya bada wanda zai dan d'au lokaci kafin cikin ya zube kar a gane."

Magajiya tai tsaki tace " mai Yaya yakeyi?"
Da sauri Lami tace "ya tafi Daura anso wani maganin."

Magajiya tace " itafa matar nan ga gidan nan?"

Lami tace " ita kuma tace a bata zuwa gobe."

Magajiya tai d'antsaki tace nifa banasan jan abin nan dan ji nake kamar akan bushiya nake a zaune."

Lami ta matso tace " karki damu 'yata....."

Wani kallo Magajiya ta mata wanda yasa tai shiru, kanta Magajiya ta juya gefe sannan tace "kayan abincin dana aika ya karene?"

Lami ta d'aga kai, Magajiya tace " zan aika da wani amma sai hankalina ya dawo jikina." dan dama ta sani da zarar taji Lami ta fara cewa 'yata tasan abu take nema.

Basira kam ta fahimci Magajiya ce kawai ke santa a matan sarki dan su kiri kiri suke nuna mata kishin cikin nan, dan haka duk abinda aka aiko mata daga bangaren Magajiya bata wani kokonto take ci.

Mahaifiyar Sarki wacce ta tsufa itama bata gazawa gun aikoma Basira kayan marmari.

Shikam gogan wato Sarki kullum sai yayi aike sau uku akan a dubo lafiyarta, wannan al'amari ya kara dugunguza hankalin Magajiya dan kuwa an sanar da ita, to ita ke yasa sanda akace tana da ciki baya mata wannan aiken? Tsanar Basira da abinda ke jikinta ya kara tsananta a ran Magajiya.

Yayanta ya dawo d'auke da magunguna kala kala nan ya zauna yama Lami bayanin komai, nan ita kuma ta shiga yin hidimominta.

A ranar da aka fara bata maganin an saka mata shine a cikin miyar kubewa d'anya, san tuwo da takeyi yasa taci tuwon nan sosai, sai dai me? Tunda ta kwanta bacci ta ke juyi a kan gado, tsananin ciwo da mararta keyi yasa tai ta murkusus, da sauri Lantana ta fita ta karasa b'angaren Sarki nan ta aika a sanar mai.

Ranar kwanan matarsa ce ta biyu, ai ko fadamata baiyiba yai waje da sauri, sun iso bangaren Basira lokacin ciwon ya mata yawa dan ta fad'o ma daga kan gado, jini ne ya fara zubo mata wanda hakan yasa hankalinta yai tsananin tashi.

Sai dai tsananin ciwon da takeji yasa ta kasa magana, shigowar Sarki ne yasa ta daurw ta fara kokarin mekewa, da sauri ya karaso ya rungumota jikinsa, hawayene kawai ke zubo mata a hankali take cewa "shikenan cikin nan ya tafi shikenan nikam na baka kunya...."

Hannu yasa da sauri ya toshe mata bakinta sannan ya kara jawota jikinsa, d'aya daga cikin bayin Basira wacce Magajiya ce ta turota b'angaren dan kai mata rahoto.

Da sauri ta zame jikinta tai bangaren Magajiya.

Tana shiga ta zayannema Lami halin da ake ciki, da sauri Lami ta shiga ciki ta sanar da ita, ajiyar zuciya Magajiya tai tace " yau da alama zan samu bacci mai dadi."

Lami ta saki dariya tace " nikuma gobe za'a sallameni ko?"

Kanta ta juya gefe bata amsa mata ba sai murmushin jin dadi data saki.

Basira kam tana jikin Sarki ganin ciwon ya lafa yasa ya kira Lantana yace ta taimaka mata ta gyara jikinta.

Basira tana mikewa Lantana taga yanda jini ya zuba sosai, salati ta shiga yi, Sarki ya kalli gun dan harshima ya b'atashi, Lantana ya kalla ya mata alama da ido akan tai shiru hakan yasa tai shiru itakam Basira hawaye kawai take yi.

Shiru yai bayan sun shiga b'and'aki, ji yai idanunsa na neman canzawa, kallan jinin yai yanajin wani abu na tasomai na bakin ciki, ba shakka yasa rai sosai akan cikin nan, yana nan a zaune Lantana ta fito ta debi kaya ta koma.

Can sai gasu sun fito, kuka sosai Basira takeyi wai tana bashi hakuri, mikewa yai yaje kusa da ita ya jawota jikinsa yace " karki damu Allah zai bamu wani."

Shiru tai batace komai ba, ya daure yai murmushi yace " kishirya gobe insa a maidake gida gun Amadu inkin warware sai insa azo a d'aukeki.

Kallansa tai cikin mamaki tace " akan me?sakata kai?"

Dariya yai sannan yace " wani irin saki kuma? Ai ba saki a auranmu cewa nai dai kije inda zaki samu kulawa sosai sannan za'a dinga d'ebe miki kewa, sai ku shirya ku tafi da Lantana."

Murmushi tai sannan ta sunkuyar da kanta kasa.

Magajiya kam an tabbatar mata ciki ya zube shine ma dalilin tafiyarta gida, nan ta aiko mata da kaya kala kala wai ta kai gida, masu murna nayi masu bakin ciki na yi na tafiyar cikin nan.

Sarki ya cika musu mota da kayan abinci ya kuma bata kudi sosai yace " zai zo sai dai bai san yaushe ba."

Sun shirya sun kama hanya.

**********

Matar Amadu kam bata yarda cikin nan ya tafi ba ita kanta basira ganin cikinta na kara tasowa yasa tasan cikin nanan, sai dai ba yanda zatai ta sanar da Sarki tunda dai ba salula babu kuma wanda zata aika, sai dai ta zauna zuba ido akan sanda zai zo.

Matar Amadu dashi Amadun tunda sukaga cikin Basira nanan suka d'aura himma sosai na kula da ita hakama Lantana sosai take kula da Basira.

_Wannan kenan_

( _Dan Allah kuyi hakuri da wannan wlh yau abubuwa ne suka cud'emin da kyar na samu nai wannan, Nagode kwarai_)

*ABU TURAB TEAM🤝🏼*

KAINUWA....Where stories live. Discover now