Kainuwa....40

6.4K 450 13
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*40*


Magajiya ce kicinged'e a kilisarta da alama tunani takeyi duba da yanayin da take ciki.
Jin muryar Hisham ne yasa ta katse tunaninta tare da bashi izinin shigowa.
Hisham ya shigo sannan ya zauna kusa da ita, ya gaidata.
Magajiya tad'an ja numfashi bayan sun gama gaisawa tace " Hisham dole ne sai mun kawar da Abu Turab daga gabanmu, domin na kula in bamuyi wasa ba Mai Martaba zai biyo mana ta bayan gida, da farko ya had'a Turab da 'yar sarkin kano sannan mun fahimci yana gani, sannan gashi zamansa a asibiti manyan masu mukamai sunje dubashi sun kuma dawo da yaban d'abi'arsa."

Hisham ya kalleta yace " Magajiya nikaina abin nan ya damen, me zai hana mu raba shi da du......"
Wani mugun kallo ta bugamai tace " so kake ka lalata mana shiri irin sanda yana jariri? Duk badadan kaje kayi shirman kona musu gida ba me zaisa Basira tabar gidan nan? Da cikin ruwan sanyi zamu turashi barzahu ba tare da an fahimci komai ba, dan haka karka kuskura ka kara gigin daukan hukunci ba tare da ni na sani ba."

Ba shakka yaji haushin kalamanta a ransa, sai dai a fili cewa yai " shikenan."
Tace " nayi tunani sosai na fahimci Basira itace lagwan yaran nan, in har muka sata a tsaka mai yuwa to fa Turab zai zamar mana tamkar akala."
Hisham yace " Na d'auka Turab muke hari ba wata Basira ba."

Tsaki tai tace " kai matsalata dakai kenan, kwakwalwarka gaba d'aya bata ja, kai kana tunanin yaran nan ba wani abu bane?"
Hisham yace " to nawa yaran yake?"
" nawa yake amma har ya nemi ja min masifa nida Abdulmajid? To bari kaji in fada ma, wlh wannan yaran in ba munyi da gaske ba reshe ne xai juyi da mujiya."

Tacigaba " so nake kasa a samomin guba amma mara karfi."
Cikin mamaki yace " guba kuma? Wace iri?badai Basira zaki kashe fa ita ba?
A fusace tace " wai meyasa in na fadi abu ne yaya sai kace sai na fadama dalili? Kasa a samo abinda na fadama, sannan ka tabbatar kasa anba wannan yarinyar da muka saka a bangaren basira data saka a cikin abincin da za' a kawo min?"
Idanunsa ne suka firfito yace " bangane abincin da za'a kawo miki ba? Kina nufin kece zakici gubar?"
Tace " wannan ba damuwarka bace in har kanaso mu d'aura Abdulmajid akan mulki to kawai ka dinga bin abinda na umarceka ba tare da tambaya ba."

Daurewa yaiyace "to."
Tace " gobe zasuzo gaisuwa, dan haka ayau zaka samo gubar ka kuma aika da ita a daren nan."
Yace to, mikewa yai ya fito yana mamakin me take shirin yi.

Yana fita ta mike, sannan tai murmushin mugunta.

**********

Shikam Abu Turab bayan ya iso yana gun Mahaifinsa sun dade suna tattaunawa game da bikinsa da kuma wasu al'amura na sarauta da mahaifinsa ya nemi shawarar d'an nasa akai.

Sun yanke shawarar komawarsa garin kano a wannan sati, in ya dawo kuma sai a tura kayan gaisuwa da na lefe a saka rana.

Bayan ya fito ne ya nufi gun mahaifiyarsa, duk inda ya wuce mutane sai tayashi murnar warkewa sukeyi har ya isa.

Basira tasa an mai girke kala kala kana ganinta zakaga tsantsan farinciki a fuskarta.
Bayan sun gaisa ne tasa aka jera mai abimci kala kala, Abu Turab yai murmushi yace "Umma kenan sai kace wanda na bar garin?"
Lantaba Tace "ai Uban gidana inaji da kai mace ne in kai aure binka zatai."
Dariya suka saka, nan ya fara zuba abinci.
Basira tace " Magajiya ta shirya walima na kusa da zamuje gobe na murnar warkewarka."

Kallanta yai sannan ya baida kansa kan abincin yace " she is trying hard."
Basira tace " magana kai?"
A'a, amma su waye zasu gun?
Tace "hmm daga dai mu matan Takawa da shi Mai Martaban sai kai da Abdulmajid, amma bansan ko da wasu ba."

Yace "hmm."
Basira tace " tace insa ayi abinci daga nan, nafi san kowa in mai abincin danasan yafi so, saboda taro ne akayishi saboda d'ana."

Zuciyarsa d'aya dan bai kawo komai a ransa ba yace " to, amma karki wahalar da kanki Umma."
Tace " wace wahala bayan ba ni zanyi girkin ba?"
Murmushi yai ya cigaba da cin abincinsa.

Sai daya gama ya mike ya fito, bangaren kakarsa ya nufa wacce ta tsufa sosai gashi batada lafiya, yana tafe su Garzali na bayansa.

Sam bai kula da ita ba wacce ta shigo gidan na sarauta dan kawo ma Abdulmajid sakon da mahaifiyarta ta aikota ta kawo.

Sai da suka kusan junan su sannan suka ankara da juna.
Kallanta yai sannan ya d'auke idanunsa ya cigaba da tafiya.
Wani sanyin dadi ne ya kamata ta karaso da sauri tace " Yaya."
Tsayawa yai sannan ya juyo ya kalleta fuskarnan a d'aure.
Murmushi ta saki tace " Yaya baka taba ganina ba ko? Nice Khadija, ahhh nasan kasan muryata, hmm Alhamdulila yau Allah ya amshi addu'a ta."

Kallanta yakeyi kawai sai dai zuciyarsa ta karaya sosai, Khadija ta share kwallarta data taho tace " Yaya Allah ne kadai yasan farincikin danakeyi ganin idanunka sun bud'u da izinin Allah bud'ar idanunka zai kawoma alheri masu yawa a rayuwarka."
Ta karasa maganar cikin rawar murya dan kuka na neman kufce mata.
Sama ya d'an kallan kadan yana neman dake zuciyarsa dan tabbas kalamanta sun ratsashi.
Kallanta yai yace " nagode, sai dai inaso ko a hanya muka hadu ki daina nuna kin sanni, banasan inzama mai jawo miki bakin ciki shiyasa nake fatan ki cireni daga ranki ki kuma daina damuwa dani."

Kai ta jinjina ta na kokarin share hawayenta da hannu tace " naji yaya, zanyi abinda kace."
Kallan mamaki ya mata dan bai yi tunanin abinda zatace kenan ba.

Khadija ta kara share hawayenta tace " kasan meyasa zan rabu dakai yaya?"
Kallan ta yai baice komai ba.
Ta cigaba " saboda ka daina murmushi in kana tare dani, ka daina fara'a, ko farin ciki kakeyi daga kaji muryata sai inga farincikin nan ya tafi daga fuskarka."

Hawayenta ta kara sharewa tace " kaine mutum na farko dana taba so, banaji zan kara san wani haka, ba kuma naji zan daina ma fatan alkairi da yima addu'a a rayuwarka sai dai bazan taba yarda inzama nice sillar bakin cikinka ba, bansan dalilinka na canzamin hala ba, sai dai ba yanda z........"

Hawaye ne suka taho sosai wanda ta kasa karasawa, jiyai gaba daya daga tsakiyar kansa har zuwa 'yan yatsun kafafunsa sun amsa, shikansa sai dayaji idanunsa suna neman canzawa na yanayin kawo ruwa.

Kallansa tai sannan ta kakaro murmushi tamai sannan ta juya ta fara tafiya.

Kasa motsawa tai daga inda yake, su Garzali na gefe duk da basusan me tacemai ba amma sun fahimci yana bukatar keb'ewa.

Abu Turab kallanta yakeyi har sai da ya dena hangota sam ya kasa motsawa, yafi minti 20 a haka kafin ya taka kamar wanda aka tsuma a ruwa ya karasa bangaren kakar.

Jikinta kam ba sauki duba da yanayin tsufan datai, bai dade ba ya taso.


D'akinsa ya nufa ya shige ya kwanta rigingine, rayuwarsu da Khadija ya shiga tunowa, wasu kananan hawayene suka zubo ta gangaren idanunsa, mirginawa yai ya kwanta ganin tunaninta na neman addabarsa ya mike zaune da sauri ya bud'e cikin drawer dinsa ya dauko d'ankwalinta har yayi kamar zai yadda sai kuma ya fasa ya d'aga can kasan kayansa ya saka shi.

Ya koma kan gado ya kwanta........

Khadija kam tana fita ta wuce gida dan kuka kawai takeyi, sam bata kula da Hisham ba dayake tsaye gefen kofar shiga gidan shi da su Galadima.

Hisham ya kula da kukan da takeyi sai dai ba damar magana saboda bayasan a ganta tana kuka.

*TEAM ABU TURAB 🤝🏻*

KAINUWA....Where stories live. Discover now