Kainuwa...72

6.2K 572 63
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*72*

Turab ne ya kalli likitan sannan yace " kana nufin kafarsa bazata dawo dai dai ba?"
Kansa ya girgiza alamar a'a yace " ba wai bazata dawo daidai gaba d'aya ba, sai dai dawowarta daidai din abu ne mai wahala, a yanzu inya warke zamu had'ashi da sanduna dan taimaka masa gun tafiya, idan har Allah yayi sai kaga a hankali kafar ta warke in yana samun kulawa."

Turab yai godiya suka mike, kallan Sabi'u yai bayan sun fito yace " Sabi'u muje ka kaini gida, sai ka d'auko Khadija ka kawo asibitin ta zauna jinyarsa, ni akwai abinda zanyi."

Sabi'u yace " wacce muka kaifa?"
Turab yai murmushi yace " kana tunanin zai sake a gun yarinyar da yake so?"

Gaba yai daga fadar haka, mota suka shiga ya kaishi gida, akan inya d'auko Khadija sai ya maida Mairo.

Magajiya kam ana zaune a waje dan an fito waje wajen wani had'aden kwalliya ta sarauta da aka zagayen gun dashi, matane manya ke ta kid'an kwarya na ruwa, sai gaishe gaishe akeyi.

Turab yana shiga ya wuce bangarensa wanda yanzu komai nashi an kwashe daga bangaren, wanka yai sannan ya bud'e drawer da ya ajiye wata shadda a ciki dan dama ya ajiye ne saboda zuwa bangaren Amarya da ita, jawota yai tare da kallan d'ankwalin daya biyo bayan shaddar.

D'ankwalin Khadija ne, sawa yai a aljihunsa dan yau zai maida mata d'ankwalinta, inhar ya maida mata kuwa to yana nufin komai na alakar dake tsakaninsu ta tsaya kenan.

Fitowa yai daga bangaren, rawani yasa akamai, sannan yasa a d'aukomai dokin da Sarki ya bashi.

Had'aden dokin da mai martaba ya bashi ya hau, yasha ado na ban mamaki, Turab ya hau kai sannan ya nufi inda ake ta mai hawan dawakai.

Yana Isa masu busa suka canza salan busarsu aka saki wani kiraki.

Magajiya tana zaune labari ya iso mata na hawan da Ango yake yi.
Kallan yan aiken tai tace " Turab ne?"

Sukace sosai ma, duk da dai rawanun dayai bazai bari mu tabbatar shi bane amma ai kowa yasan Ango ne.

Tsaki tai a ranta tace " zancen banza kenan, Ango? Ai Abdulmajid ne angon."

Yana gama hawa dan ba dadewa yai ba ya nufi inda Magajiya take.

Aiko mata akai akan d'anta yazo kwasar gaisuwa.

Murmushi ta saki tace " ace ya shiga ciki ina shigowa."
Nan aka sanar ma Turab.
Ciki ya shiga ya samu guri ya zauna.
Magajiya ta mike cikin yauki ta nufi ciki.
Murd'a kofar tai ba tare da ta kula ba saboda bayansa ya juya tace " Ango kasha kamshi, dafatan yanzu ka hakura da aura........."

Juyowar da Turab yai tare da cuge rawanin ne yasa ta tsaya cak da maganar, jitai wani abu tundaga tsakiyar kanta har kafarta.

Turab ya tako cikin isa ya karaso inda take, hannu yasa ya tura kofar d'akin data rike da karfi bai cire hannunsa daga kai ba yace " Kina mamakin ganin wanda ya kamata ya mutu ne a tsaye a gabanki?"

Magajiya ta kakaro murmushi tace " me kake nufi? Kaine Angon mana, ko akwai wani aure da akai da ban sani ba?"

Turab ya girgiza kai yace " ina fa? Ai ni kadai ne a gidan nan aka d'aurama aure yau sannan aka Wani asibiti."

Magajiya tace "asibiti kuma? Me kake nufi?"

Turab idanunsa ne suka canza kala ya juyo ya kalleta yace " sa mayafi mu fita."
Tace " mene?"
Yace " abinda kikaji shi zakiyi."

KAINUWA....Where stories live. Discover now