Kainuwa....42

6.3K 470 45
                                    

..🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*_Wannan shafin naku ne 'yan Zauren BieBie Isa, tnx alot 4 ur support....Much luv_*

*42*

Abu Turab ya shiga bangaren mahaifiyarsa, ba kowa a falon sai Lantana dake zaune jugum.
Tana ganinsa ta mike ta gaisheshi, kallanta yai yace " Umma fa?"
A hankali tace "tana d'aki."
Juyawa yai ya fita, dayake magrib ta duso massalaci ya nufa.
Ana idar da sallar wasu dan gulma tun a cikin massalacin suke yan gulmace gulmacen maganar, mikewa yai ya fito.
Bangaren Mahaifinsa ya nufa.
Jakadiya tana ganinsa ta iso gunsa ta gaidashi.
Kallanta yai yace " Mai Martaba fa?"
Tace " Yana ciki, a ma iso?"
Kai ya d'aga mata alamar eh, har ta fara tafiya sai ta dawo gunsa tace " Hmm nikam Yarima naji abinda ya faru, sai dai kuma hmm tuba nake ranka ya dade amma ni nasan akwai alamar tambaya a al'amarin nan."
Gefe da gefe ta kalla tace " Sai dai neman Allah ya fitar da ku lafiya."

Kauda kansa yai daga kanta dan shi sam bayasan harkar gulma tunda kuwa yaga yanda take wani juye juye yaji ransa ya baci.

Juyawa tai, bata dade ba sai gashi ta dawo tace ya shiga.
Abu Turab ya shiga.

A zaune ya tadda mahaifinsa sanye da tabarau, rike da wata takarda da alama karantawa yakeyi.
Abu Turab ya shiga sannan ya kara gaidashi.
Sarki ya zare tabarau din ya kalleshi yace " Turab ya akai?"
Abu Turab ya kalleshi yace " Abba, na tabbata kasan Umma bazata aikata wannan laifin ba."
Murmushi yai sannan yace " bansan komai ba Turab, bansan ko zata aikata ba ko bazata aikata ba."
Kallan mamaki Abu Turab yamai yace " Abba."
Sarki ya kalleshi kallo wanda bazaka tana fahimtar yanayin da mutun yake ciki ba yace " Abu Turab ba dai so kake kacemin in yarda da Basira ba, bayan a gabana Magajiya ta fadi?"

Abu Turab cikin mamaki ya kalleshi yace " Amma......"
Katseshi yai yace " In har kanaso in yarda da Mahaifiyarka to inga evidence wannan shine kadai abinda zan fadama."

Abu Turab yai shiru" nagode." Kawai abinda yace kenan yai waje.
Mai Martaba ya bi bayansa da kallo cikin tausayawa a fili yace " Abu Turab dolene sai ka yaki weakness dinka, Magajiya ta riga tasan Basira tace lagwanka, tunda nake bantaba ganinka cikin damuwa kamar tayau ba.

Abu Turab yana fita ya nufi bangarensa, sam ya rasa dalili zuciyarsa ta kasa bashi wata mafita, kwakwaran tunani ma ya kasayi, mahaifiyarsa kawai yake hangowa lokacin da ta kalleshi cikin wani yanayi, kallo d'aya yamata ya fahimci tsantsan tashin hankali karara a idanunta.

Wannan rana ta zame musu ranar tashin hankali, Abu Turab da Basira.
Magajiya kuwa ta daina amai sai dai har alokacin bata bude idanunta ba a haka a ka kwana, khadija ce ta zauna a gunta.

Washe gari da safe yana zaune a d'aki Garzali ya kwankwasa mai kofa.
Mikewa yai ya bud'e, kallansa yai yace " Garzali ya akai?"
Garzali yace " Sabi'u ne ya zo Ranka ya dade."

Bai koma ciki ba kawai ya jawo kofar d'akin ya fito falo.
Garzali yabi bayansa.
A zaune yaga Sabi'u.
Kusa dashi ya karasa ya mikamai hannu sukai musabaha.
Sabi'u ya kalleshi cikin kulawa yace " Mutumina are u okay?"
Murmushin yake ya masa yace " ya akai da safen nan?"
Sabi'u ya kalleshi yace " maganar Gimbiya Bilkisu ce."
Kallansa Abu Turab yai yace " ta fasa aurena?" Murmushi yai yace " nasan haka zata faru ai."
Sabi'u yace "no ba haka bane." Ya fada yana girgiza kai.
Abu Turab ya kalleshi sai dai baice komai ba.
Sabi'u yace " nemanka takeyi."

KAINUWA....Where stories live. Discover now