Kainuwa......33

5.7K 469 29
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*33*


Hisham ya iso Zariya cikin tashin hankali, ana magrib yana shiga bangaren Magajiya.
Zaune take gefenta kuma Khadija ce tana duba mata wasu kayayyaki, Abdulmajid kuma na gefenta na hago.
Hira sukeyi da Abdulmajid sama sama, itakam Khadija bata sa musu baki a zaune kawai take tana aikin da aka sata.
Can cikin hirar tasu ne Abdulmajid ya kalli Khadija yace " ke dama inada magana dake."
Kallansa tai batace komai ba.
Fuskarsa a had'e yace " haryanzu baki daina zuwa b'angaren Abu Turab ba ko? Kina mace ko kunya."
Magajiya ce ta kalleta tace " Khadija me kenan?"
Kanta ta maida kan kayan tace " meye amfanin ma in naje tunda ba kulani yake ba?"
Dariya Abdulmajid yasa yace " kinji kunya wlh, kina mace kina bin namijin da baya sanki."
Zatai magana Hisham ya banko kofa cikin hanzari.
Jin yanda a ka bugo kofar yasa duk su ukun suka maida ha kalinsu kan kofar.
Hisham na shigowa ya kalli Khadija yace " bamu guri."
Mikewa tai tsam dan dama ba san zaman takeyi ba sai dai jikinta ya bata ba maganar arziki zasuyi ba.
Tana fita ta tsaya a jikin kofar d'akin.
Hisham ya kalli Magajiya cikin tashin hankali yace " Magajiya!"
Ita kanta hankalinta ya tashi ganin ita data aikashi maganar aure kano? Ya dawo mata a haka?"
Kallansa tai tare da tattara hankalinta kansa.
Yawo ya had'iya sannan yace " yaran nan yana gani Magajiya."
"Yaro? Wani yaro kake nufi kenan?"
Yace " yaron nan mana da baya gani."
Idanu tad'an juya tace "wai wani yaran kake nufi? Nibansan wani yaro ba."
Abdulmajid ma yace " wani yaro kake nufi Kawu?"
Hisham yace " Yarancan Abu Turab."
Dariya Magajiya tai tace " Waziri? Ko dai gajiya ta fara ratsaka ne? Me kake san fada takamaimai?"

Hisham ya kallesu cikin wani yanayi yace " Wlh da gaske nakeyi, yarancan Abu Turab idanunsa garau suke."
Abdulmajid ya mike tsaye yace " ni wlh na dauka maganar arziki zaka fada ashe tsokana kazo da ita, ni nayi masallaci."

Hisham ya kalli Magajiya yace " Magajiya na taba miki karya akan harkar dana san bazata amfanemu ba?"
Wannan lokacin kam ta kalleshi kallan nutsuwa, Abdulmajid ma ya ja ya tsaya.
Khadija kam da baya da baya ta juya tai waje cikin tashin hankali, me kenan?

Hisham ya kalli Magajiya sannan ya kalli Abdulmajid yace " dayaje kano a garau yaje musu."
Magajiya ta kanne idanuwanta tace " ban fahimta ba."
Nan Hisham ya zayane mata kaf abinda ya faru na zuwansa.
Tashin hankali karara ne ya bayyana a idanun Magajiya, kallansu tai cikin tashin hankali tace " ku bani guri."
Nan suka mike suka fita.
Abdulmajid ma bangarensa ya wuce cikin d'emuwa da rashin sanin abinda zaiyi.
Shi kuma Hisham yai waje.
Magajiya ta kasa zaune ta kasa tsaye ba shakka in har hakan ne lalai kaf duniya ba wanda ya taba rainamin hankali irin yaran nan.

Kwallawa wata mai kula da ita tai, cikin hanzari ta iso.
Bata ko juyo ta kalleta ba tace " kiramin Abu Turab."
To tace kawai tai waje itama.

Abu turab yana zaune kan sallaya tilawa yakeyi cikin daddadan muryarsa, yau ko masallaci bai je ba dan bayasan ganin kowa.

Garzali ya mai sallama, sai daya kai aya sannan ya amsa mai.
Garzali ya matso ya tsugunna sannan ya sanar dashi sakon Magajiya.
Ya dade kafin yace " ace mata ina zuwa."
Nan yai waje.
Sai dayai sallar isha'i sannan ya mike ya fito, Garzali ya mikamai Sandarsa wacce Lantana ta kawo.
Amsa yai sannan yai gaba Garzali yabi bayansa.

Bayan an mai iso ya zauna a kilisarta sannan ta shigo cikin takamarta.
Idanu ta kafa mai har ta zauna shikam fuskarsa a had'e take yana zaune kansa a kasa.
Bayan ta zauna ne ta kalleshi tace " Abu Turab ka iso?"
"Barkanki da warhaka Umma Babba."
Murmushi ta sakarmai sannan bata amsa ba tace " kiranka nai in baka wani labari."
Shima bai amsa mata ba dan lalai ji yake bazai iya kallanta ba saboda tsananin tsana.
Magajiya tacigaba " Wani dan tsakone kurma ya taso karkashin kulawar kura, ita kurar dama tanada nata d'an hakan yasa ta had'asu duka ta rike, a kwana a tashi sai kurar nan ta tsufa, ta fahimci dole tana bukatar barma d'anta mukaminta a daji.
Kasan abin mamaki?"
Abu Turab ya d'ago suka had'a ido, bai d'auke idanunsa daga cikin nata ba yace " bazai wuce wannan d'an tsakon kurma yace shi yake san aba wannan mukamin ba."

Ta kuramai ido itama tace "Haka! Ashe ka harbo jirgin, sai dai kasan wani abun tsoro a labarin?"
Kallan ban fahimceki ba ya mata tace " Tun daga sanda Kurar nan ta fahimci kudurin wannan d'an tsakon har yau ba wanda yasan inda wannan d'an tsakon yake."

Wani lalausan murmushi ne ya bayyana a fuskar Abu Turab yace " sai dai ban fahimci abu d'aya ba a labarin, d'an tsakon dama can kurma ne ko kuwa yayi hakan ne da saninsa ya noke bakinsa?"

Idanun Magajiya ne suka d'an canza sai dai da sauri ta maida fuskarta cikin yanayin hankali a kwance tace " hmm wannan shine abinda ya sa kurar nan dana sani."

Gani tai ya saki wata yar karamar dariya har hakwaransa suka bayyana ya kalleta yace " Tuba nake Umma Magajiya, na saki a duhu danai na nuna miki nidin bana gani."

Wannan karan kam duk yanda taso ta b'oye bacin ranta ta kasa, karara ya nuna a fuskarta.
Abu Turab ya rangwadar da kai yace " umm ya zamuyi yanzu?"
Tace da me kenan?
Yace " dan banaji zan iya yafemiki."

Kallo tamai cikin mamaki tace " bakaji xaka iya yafemin kamar ya kenan?"

Fuskarsa ce ta canza idanunsa sukai jaa, ya kalleta yace " bazan taba yafe miki ba daga ke har yayanki, abinda yama yayan mahaifiyata da matarsa da ke da kika umarceshi a sanadiyar kokarin rabani da duniya da kukai kuka jamusu mutuwa, ni Abu Turab in har Basira da Abdussamad sune suka haifeni sai na sa an muku hukunci daidai da laifinku."

Wata muguwar dariya ta saki, wanda ya sashi tsayawa yana kallanta tace " kai a suwa kenan?"
Yace " a wanda yake da damar zama Sarki."

Ta ja tsaki tace " Shekaruna d'aya da mahaifinka, hakan na nuna nid'in batayau bace, ba kai ba hatta mahaifinka bai isa yaja dani ba."

Abu Turab ya d'an juya bakinsa sannan ya had'a lab'ansa yace " well, shi daban nid'in daban, mu zuba mu gani."

Tace " shikenan mu zuba mu gani, na baka sati biyu kacal, ina zaune anan zakazo gwiwowinka biyu ka nemi gafarata."

Yace " ina fatan hakan ta kasance."
Kallan juna sukai, kansa ya saukar kasa ya juya kansa gefe tare da d'aukan sandarsa yace " Umma Babba nagode ni zan wuce, ki huta lafiya."
Kallan mamaki tamai, gani tai ya sa sanda a gaba kamar makaho.
Idanu ta kuramai har ya fita, ta murmusa tace " hmm a kashi 100 na baka 40, ba laifi ka iya b'oye fuskarka da abinda ke ranka, ko dayake d'an Abdussamad ne."

Fuskarta ta kuma had'ewa tace " kai har ka isa? Kamar ni? Kamar ni Magajiya ka rainan hankali?"
Kwafa ta saki.
Abu Turab kam na fita ya juyo ya kalli bangarenta sannan ya juya ransa a b'ace.

*********

Itakam Khadija ta shige d'aki ta kwanta akan gado, me ke faruwa? Ya Turab yana gani? Anya kuwa? Ta yaya? Yaushe?
Itakam ta kasa yarda da abinda taji, ba dai wani sharrin zasu kullama bawan Allah ba?
Da sauri ta mike zaune tace " dole in fadama Yaya gobe akan abinda sukace."

*TEAM ABU TURAB🤝🏻*
.

KAINUWA....Where stories live. Discover now