Kainuwa.....63

6.4K 500 37
                                    

🕊 *KAINUWA*🕊
......... _ɖąʂɧɛŋ Διιąɧ_
( _*A Historical Fiction*_)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*63*

Kallansa tai tare da yin ajiyar zuciya tace " wai ni Abdulmajid mai na tsare maka ne?"
Kallanta yai sai dai baice komai ba, tace " saboda kai yanzu ko gaida Umma Basira ba na iya yi, na fadama banaso dan Allah ko ana so dole ne?"

Kai ya rangwada gefe ya sakar mata wani lallausan murmushi yace " Mairo inaso inga kina fada, kyau yake miki."

Rasa ma mai zatace tai ta saki baki cikin takaici tace " Dan Allah nidai na rokeka ka kyaleni."

Abdulmajid ya matso hakan yasa tai baya da sauri dan ta san halinsa.
Sai da takai jikin bango sannan tace " matsa menene hakan?"

Abdulmajid fuskarsa a had'e ya sako fuskarsa saicin kuncinta.
Tsoro yasa tasa hannu biyu a kirjinsa ta turashi.
Hannayenta ya rike yace " Mairo sai yaushene zaki daina wahalar dani?"

Gabanta ne ya tsananta fad'uwa, ga dare ne soron ba haske, tace " ban fahimceka ba, wahalar dakai name?"

Jawota yai saura kiris ta had'u da jikinsa gashi ya rike mata hannaye duka, yakai bakinsa saicin kuncinta kamar wanda zai sumbata, da sauri ta runtse idonta cikin tsananin fargaba tare da sa kafa ta taka mai kafarsa.
Ko gezau baiyi ba sai dayai bakisa daf da kuncinta sai kuma ya saki dariya yace " Mairo kinganki kuwa?"

Gabanta sai wani irin fad'uwa yake ta kalleshi, hannayenta ya saki yana cigaba da dariya yace " sry, wlh ba abinda zan miki kawai so nake naga yanda zakiyi."

Lab'enta na kasa ta ciza sannan ta sa kafarta ta kara taka kafarsa da karfi.
Kara ya saki sannan yai baya da sauri yace " Mairo amma dai ke wlh da a india kike da film zakiyi, boss zaki zama."

Harararsa tai tace " Allah Abdulmajid ka kiyayeni."
Kansa ya shafa yace " ba laifi ai in namiji ya kiyayi matarsa."
Ta makamai wata hararar tace " mijin tace kawai."
Ta fada tare da juyawa zatai gaba.
Gabanta yasha da sauri yace " Sai da safe, gobe zan sake magana a fada dan na gaji da jira."

Tana kokarin bashi amsa yai gaba, tsaki taja sannan tai gaba, haushinta ma da mahaifiyarta ta sata ta fito da ai ta ce ko yazo bazata sake fitowa ba.
Tana shiga ta wuce d'akinsu ta fada kan gado.
Ummanta ce ta leko tace " kin dawo?"
Mairo tace " Umma ni dai ko yaran nan ya dawo dan Allah karki kara cewa in fita, ni wlh bana so."

Tace " Mairo shifa aure da kike gani ba wai mutum ne yake zab'awa kansa ba, babu yanda za'ai wani ya auri matar wani, haka kuma babu yanda za'ai wata ta auri mijin wani, duk wanda kika ga sunyi aure to fa dama akwai aure a rubuce a kaddarar rayuwarsu, inhar yaran nan ba mijinki bane cikin ruwan sanyi sai kiga kun rabu bawai fadanki bane zai sa ku rabu."

Mairo ta turo baki, tana san magana taga Umma tayi waje, kara komawa tai ta kwanta a fili tace " Ya Allah!"

************
Magajiya kuwa a daren yau ta tsaya sosai tayi tunanin al'amarin dake faruwa, yanzu ta fahimci Abu Turab bai san sirrinta na Abdulmajid ba, tunda a tunaninta da hankalinsa bazai yi tunanin had'a auren Abdulmajid da Khadija ba in har yasan wannan sirrin, tunda yasan ba abu bane mai yiwuwa.
To wanne ya sani? Maganin nan ta tuno da abinda ya fad'a mata a lokacin, mikewa tai zaune tace " yasan sirrin ba Hajiya magani." da alama wannan shine sirrin da ya sani.
Washegari da sassafe tasa aka kira mata wannan yarinyar, yarinyar ta shigo jikinta sai tsuma yakeyi, ta shiga ta zauna a falon da ba kowa.
Magajiya ta shigo sanye da rigar bacci dan ko wanka batai ba, karfe 6 ne na safe.
Magajiya ta kalleta tace " ina abinda aka baki?"
Da sauri tasa hannu a lalitarta ta d'auko maganin.
Magajiya ta kalleta tace " akwai wanda ya kamaki da wannan maganin?"
Kai ta girgiza alamar a'a tace "ba kowa, ina kuma zuba mata kullum."

KAINUWA....Where stories live. Discover now