*~Based on True life story~*
NABEELA
*🤍(RAYUWAR AURENA)🤍*BY THE DMKs✍🏻
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻
*Dedicated to SADY🥰 much love sister, NABEELA tace nagayamiki Tana jin dadin shawara da kk bata😊kina bata karfin gwiwa sosai*
Page 28
Wani numfashi mai nauyi naja kafin nafara sauke ajiyar zuciya a hankali nafara bude ido na ina ganin Shi na fashe da kuka Don ALLAH karka kashe ni kayi hakuri Karka cutar Dani, bazan sake kuka akan Hammana ba..
Shhhhhhhhhh Baby na stop crying I'm here for you Hushhh MAS'OOD na Raye bai mutu ba Karki ji tsoro kinji Babyna
Ya Hakuri Don ALLAH karka kash... Bai Bari nakarasa ba ya Rufe min baki da nashi saida yaji Nafara dawowa daidai kafin ya sake ni.. Look who is here NABEELA sister MEEMAH ce.
NABEELA ya jiki? Kidaina kuka yayanki na Raye kuma ya kusa dawowa gareki Kinji koh?
Toh Addah MEEMAH Don ALLAH inason in biki Gidan ki Inajin tsoro Sosai.
Haba baby tsoro wa kk ji kuma bayan ina nan?
Kidai ce kawai kina so Kije kiyi Hutu, na barki Kije kiyi ma sister MEEMAH sati daya Kinji
( su Mr JMK ana tsoron kar a tona mai asiri Hardawani Nabar ki kije🤣)Nagode.
Bara Inje gida Indawo dama kanin mijina ne ba lafiya nazo dubashi shine AHMAD yake ce min Kema baki da lafiya kuma Wai Bai garin yau ya iso shiyasa Bai gayamin ba.. Bara in koma in miki girki da kaina in kawo miki.
A'ah addah MEEMAH ni tare Zamu tafi tsoro nakeji Nide mu tafi.
Toh AHMAD Zamu iya tafiya koko sai mun jira?
Bara Anty FAEEZA Tazo muji
AISHA Gaskiya Tayi Abinda ya dace bacin ita da ba asan mai zai same NABEELA tunda Kinga ni inacan Abuja bansa abinda ke faruwa ba sai kirana tayi tana kuka wai Tana tunani NABEELA ta mutu. Nace Tayi saurin kaita asibiti ni zan biyo jirgi in dawo rana Thursday Ina ji shiyasa take jin tsoro ta dauka ranan Dana zo musu salama zan tafi injiyo Labarin MAS'OOD koh yana Raye koko ya mutu shine hala Abin ya kara gigita ta
ALLAH sarki aiko an gode Haka ake so zaman lafiya gashi ita da kanta ta kawo ta asibiti.
Good morning NABEELA Ya jikin ki?
Duk kin gigita mijinki dazun sai sunbatu yakeyi yana I don't want to lose you NABEELANayi murmushi nafada a zuciyarta Ashe yana tsoron in mutu?
Zamu iya tafiya yanzu?
Eh zaku iya Saide ga medications inta nan AHMAD yasan komai
Saida muka koma gida na kwasa kayana muka wuce gidan Addah MEEMAH
Sai yau nake sanin dadin yan uwa da ace ina da yaya koh kanwa nasan Haka Zatayi min kamar yanda Addah MEEMAH ke min harta wakan saida tayani kaini bayiYau jina nakeyi kamar wata yar sarki komai yimin akeyi
Nagode Sosai addah MEEMAH ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah ya sa kifi HakaAmin Kanwata su Meenal da Ummah suna hanya.
Addah ina su Hydar suke ban gansu ba
Suna school amma sun kusa dawo waAddah dagaske ne ba ansa inda Hammana yake ba?
No. Sadiq yace an tura su ya MAS'OOD wata kasace training sai ake tunani koh plane insu ne Yayi crash Ashe bana su bane.
Toh meyasa ba asamu Shi a waya.

YOU ARE READING
NABEELA(RAYUWAR AURENA)
Non-FictionWanan Labarin Is based on True life story.. " "Labarine da ya kunshi abubuwa da dama akan Rayuwa da zamantakewa Auretaya" "Labarin Wata yarinya Yar shakara sha shida aduniya wacca ta taso a hanu kishiyoyi mamanta Alokacin da take tunani cewa wahal...