Page 77

362 36 8
                                    

*~Based on True life story~*

          
              NABEELA
*🤍(RAYUWAR AURENA)🤍*

BY THE DMKs✍🏻


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻



Page 77

Yau akayi ukun addah WALIYE da kyar mukayi convincing ba HASSANA tabi mu Abuja akan cewa in ALLAH ya sauke ni lafiya saita dawo

Yau Saura sati daya bikin MEENAL da AKHY anca KD muka sauka daman kaya mu na can

Ba HASSANA muje daki sai ki samu kiyi wanka ki ci abinci

A'ah Danejo ina laifin abani abinci in ci in yaso sai nayi wanka daga baya
Wai ma natambaye ki wacca wanka kuma banda wanka da mukayi a can

Wanka gajiya nake nufi

Gajiya kuma? Abinda iska ne ya dauke mu wannan gajiya kuma nide akawo min abinci naci nifa rabona da Inci in hantse kwana uku kenan

Toh shikenan Badamuwa bara naje nakawo miki

Da yafi Yo hauka ma akeyi dazan wani biye ma yan birni inyi wata wanka gajiya bayan ciki bai dauka ba toh koh naci na hantse ba wani wanka da zanyi ehe..

Ganin ankawo mata rice and chicken stew ta yashe baki ALLAH sarki Danejo Sannu da kokari duk wannan abinci nikadai?

Eh ba HASSANA..!

Bismillah Gaskiya yan birni Suma ba a baya ba wanja girki Jiba yadda mai yayi shanana a sama miya
Danejo inna baki labari rabona da shan wannan just din tin bikin ki da wannan Dan iska yaron Waye ma yake da suna?

Mr JMK!

Mainene kuma Jemeke ? Ya koma Arne ne?

A'ah ba HASSANA sunan sa AHMAD JMK

Ga sunan mai daraja amma shi Sam bai biyo masu sunnan ba naji dadin da kk rabu dashi kk aure MAS'UDU yaron kirki ga kunya ga sannin daraja mutane

Uhmmm ba HASSANA naga kin ciye koh na Karo miki ne?

Karo mai ?

Abinci...

Abinci kuma? Saikace wata jaka? Inna laifin kice zaki karomin Kazan amma kin wanni cemin abinci?

Toh bara naje nakaro miki

Toh kefa? Inna naki abinci?

Jiran shi nakeyi yazo sai muci

Shi wa?

HAMMA..!

Lallai Danejo cikin fari ne ajikin ki fa keda yakamata kina jin kunya mijin naki amma shine kk shishige mai hobdijam yaran zamani Sam ba fulantaci

Ba HASSANA nifa bana iya cin abinci ni daya shiyasa muke ci tarai

Inye samu waje ah Lallai bashaka Danejo
Maza ki dibo abinci ki zo nan kici ina fatan dai ba daki daya kk kwana ba?

Daki daya ne

Ohni HASSANA naga abinda yafi karfina Yanzu kina numfi daki daya kk kwana dashi? Ba kunya bama tsoron ALLAH hobdijam toh daga yau Salan ya murkushe ki dake da abinda yake cikin tab indai kinaso yaron ki yafito da kunya karki sake zuwa dakin da yake ki kwanta ai wannan rashin kunya ne Dan Fari ne fa acikin ki

Toh ba HASSANA.. Yanzu tunda kin Gama ki shiga kiyi wanka

Yo hauka ma akeyi dazan shiga wannan tukunyar nayi wanka nifa bara kiji koh da bikin da mukazo alwala nadinga yi sabida da girmana bazan kwanta a wannan tukunyar inyi wanka ba banda ALLAH na tuba yan birni halin yara suke dashi inani ina wanka cikin dauda Inayi dauda nadawo jikina duk kafito wanka Kata maikon dauda kawai

NABEELA(RAYUWAR AURENA) Where stories live. Discover now