page 12

649 29 0
                                        

Alhamdullillah Ya Allah!!!!

          
           NABEELA
*🤍(Rayuwar Aurena)🤍*

BY THE DMKs✍🏻

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻


Page 12

Mallam nashiga uku jiya nan aka zo nima Auren wanan yarinya kuma dagaske suke.

Dama nagayamiki, shiyasa nabaki maganin na Kisa mata Kuma ki tabarta batayi bismillah ba amma kk yi yanzu ba Abinda Zamu iya yi akai.

Mallam yakamata ayi wani abu akai, gaskiya
Ga Yar lale nan a gida ace kuma ita wanan ta tafi ta barta..

Hahahaha bamu gayamiki ba Indai kina son yarki tasamu dama sai kin kawo ta nan.. Rishna Yayi Aikin shi. Koh da kuwa ki bada kudi Aikin bazai yi karko ba harsai kin kawota nan.

Naji Mallam nawa zan baka kawai akashe ta yanda kowa zai rasa bazan taba jure gani tayi aure ba auren ma a birni mallam ka tamake ni..

Hahahahaaha mu gayamaki tun a baya kasheta zai zama mana baba hadari bamu kadai ba harke ma.. Sabida tamai da ubangiji Abin ambato ako da Yaushe kuma bata Wasa da adininta, koh aljani da muka tura mata na bakin jini Ya gayama na akulum saita kona Shi da ayoyin Alkur'ani Indai kina son yarki ta samu saurayi kuma a birni Kiyi yanda muka ce kawai.. Kuma tun yanzu zaki ajiye kudin maganin Afara..

Toh Shikenan mallam duk yanda kace amma ayi kokarin Hana auren nan harsai ya'ta Tayi. Sanan kuma Gobe zan kawo kudin magani.

Karki damu zamu yi abinda ya dace.. Ga wanan ki shafa mata a Kai Hakan zai sa Ya gujeta nawani lokaci bama shiba duk wani Namiji..

Naganshi ruwa ruwa Tayaya zan Sa Mata mallam..?

Wanan ya rage gareki, Duka gashi kanta zaki shafa mawa..

Nashiga uku yanda gashin kanta ke da Tsayi da cika Tayaya zanyi..

Tashi Ki tafi, tashi Ki tafi da gudu, da baya da baya..

Ke Karki ga Anje asibiti an karyata cikin ki dauka kinyi nasara muna nan ciki zai bayyana.. Maza ki tashi Kije kiyi min wanki Dana sa ki... Kina wani rike Jiki Saika ce ni na aike Iskanci..

Toh ba HASSANA.. Bara in sha magani Toh.

Harzan tashi naji salama Sir MAS'OOD..
NABEELA Ya jikin ki..?

Mallam lafiya zaka fado gidan mutane, nan fa ba gidan Yan bariki bane da zaka shigo Kai tsaye..

Hammana jikin Dasauki, yau baka je school bane..?

Naje but I've to come check on you to know how your doing..?

Oh ni HASSANA, Wai Mai Ammadu yazama ne yabar Gidan Shi yana so ya zama Gidan tare gardawa..
Ke bara in gayamaki inda zakuyi Iskanci kuje can dandali ba nan ba. Inbada rashin Tarbiyya ka biyo yarinya har gidansu..

Maza ki tashi Kije kiyi Abinda nasa ki kafin ranki ya bace.

Anjima zan dawo in dubaki kinji koh..

Natashi nafara yin Aiki dake gabana, tunda yanzu Adda ummah ne takoma siyar da kosan.. Harna gama wanki Da wankeke ta shigo rai a bace,

Mama kosen na nan jibge ba kasuwa Gashi har sha biyu tayi... Nifa zan shigo ciki..

Hehehhe Ashe dai bamu kadai bane masu kwante Ashe baki jini Harda jikokin mallamai Hehehhe bata Ida shigowa ciki ba, ba HASSANA tayau kanta da  karfi ta shake Mata Riga dakyar muka kwace ba HADIZA a hanunta.

NABEELA(RAYUWAR AURENA) Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz