*~Based on True life story~*
NABEELA
*🤍(RAYUWAR AURENA)🤍*BY THE DMKs✍🏻
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻
Page 78
Wani kara nasaki nayau kan AHMAD sabida tsanani tashin hankali gani jini nata zuba yasani kara gigicewa
NABEELA inda wani Abu yasamu AHMAD tabbas kece sila inji Hajiya MARIYA cikin gaggawa aka dauke shi zuwa hospital
Ni narasa abinda ke sani kuka, kuka nadinga yi ace wani ya mutu ta sanadiya ta sannan gasu ukhtee dasu ma hankalin su duk atashe ga kuma uwa uba My Jaan Sam yakasa cewa komai Ganin inata kuka ukhtee tazo tana bani hakuri Waigawa nayi naga HAMMA'am baya gun..
Watsewa aka dinga yi har yarage sai imu imu bani Nakoma gida ba sai after 9 na dare koh Dana dawo HAMMA baya gida
Kandala Alhajee fa?
Baidawo ba rabon sa da gida tun safai
Jin Haka hankalina yakara tashi kiransa nayi a waya amma bai daga ba har sau biyu Kiran FAREED nayi Don inji ya jikin AHMAD dinUkhtee jikin AHMAD Alhamdulillah Yanzu Haka ma yana gida karki damu kanki Kinji
Toh Alhamdulillah kuna tarai da HAMMA NE?
Nope..!
Toh nagodai na yanke Kiran nakira ya SADIQ please kuna tarai da HAMMA ne?
Nope...! Nifa ina Kano koh kin manta ne?
Oops sorry namanta ne...
Danejo ga jikon nan kizo kisha fa
Inna zuwa ba HASSANA
Wai yanaga duk damuwa a fuskar ki ne kardai ace sabida wannan Dan iska yaron kk tayar da hankalin ki?
A'ah ba HASSANA kawai dai naga banga HAMMA bane kinsa matsalar sa bai kamata ana tayar masu da hankali ba
Kede kiyi a hankali kar hawan jini yakama ki Atoh
Nasan MAS'UDU ba yaro bane yasan abinda yakeyi toh mai na wani daga hankali ki akai?Nafa kira shi bai daga ba
Toh sai akayi yaya watakila yana tuki ne
Hakane kam bara naje na watsa ruwa
Toh. Kifa sha jikon nan fa rashin shan jiko ne yake hana ku hyhuwa da kanku sai an yanka ku.
Toh ba HASSANA..
Har Karfe shadaya HAMMA bai dawo ba nayi kira natura text amma Sam ba reply sai sarfa da marwa nakeyi a gidan tsoro duk ya kamani sabida bansa a wannan Hali HAMMA yake ciki ba.....
@ MAS'OOD
Ganin abinda NABEELA takeyi yasa shi tunawa da Kalman AHMAD nacewa ba sonsa NABEELA takeyi ba kawai ta aure shi sabida tausayin sa
Gaskiya ka fada AHMAD nasan NABEELA tana sonka haryanzu koh Dan wannan abun da yafaru na tabbatar dacewa kai take so bani ba
Kuka yayi Sosai a mota kafin ya tuka kansa zuwa hospital dama yana da patient dazai ma aiki jibi
Duba files ya dinga yi dukda dai hankalin sa Sam baya gun
Dr M. A yau kwana zakayi kana aiki bazaka gida ba
Eh Dr Amnah aikin yana needing more concentration shiyasa banso asamu matsala
In shaa ALLAH baza a samu ba amma yau ya zakayi da my jannah inda ta tashi niman abu baka gun

YOU ARE READING
NABEELA(RAYUWAR AURENA)
Non-FictionWanan Labarin Is based on True life story.. " "Labarine da ya kunshi abubuwa da dama akan Rayuwa da zamantakewa Auretaya" "Labarin Wata yarinya Yar shakara sha shida aduniya wacca ta taso a hanu kishiyoyi mamanta Alokacin da take tunani cewa wahal...