*~Based on True life story~*
NABEELA
*🤍(RAYUWAR AURENA)🤍*
BY THE DMKs✍🏻
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻
Page 32
@Mambilla
Oyo Oyo Yan birni bara in shimfida mana tabarma Anan
Ummah mun same ku lfy?
Lafiya lau Hyre ya kk baro min yar lele na
Ummah akwai labari Kai garin dadi na nesa Ummah kinga gidan da WALIYE ke ciki kuwa? Toh ya kusa yafi karfin girma rugan nan gakuma gidaje aciki sanan Nata wani pankacece
Shapti wai wai ta tsula Yo Wai ma hauka akeyi in zauna yar cikina ta tsulamin karya nikuma ina Murna Kai girma ta fadi
Ba HASSANA ki tambaya Wanda sukaje Kema Kisan nafi karfin inyi muku karya
Hyre Kema kk biye mata cigaba ina jikin
Aradu ALLAH Ummah birni tayi wani mota damuka shiga harda kankara aciki Ummah abinci Baja Baja Sai Wanda kk Zaba ga nama Kala Kala harda na dawisu
Hehehhe hakkun tamazugal wai dawisu wanan karya haka
HASSANA kifita cikin idona in rufe Kuma Kisan dacewa ruwa ba Saar kwando bane kina Kara ce tak saide kiga kwalawa sunzo su dibe ki
HADIZA mafashi inki fasa kinraina kanki Waye zaki zo kinama birga banza Yaushe kk yi kudi dahar zaki zo kina min Magana banza
Ummah ki rabu da ita Kisan talauci haka yake sawa baki ga mallam Audu ba kulum cikin tsiya
Hehe hakane Kuma fa Hyre ai Shiyasa koh da Mallam ya zabi masu zuwa birni nace kar ya kuskura ya dibomin dagin tsiya dama Su barbarde
Kinsa ance makashinka yana tare dakai.
Uwar mai zai Kai mu dama Kinsa dai HADIZA Nafi karfin kwadayi dake dashi Ammadu ku karata can da munafinci ku Aradu ALLAH nasake jin kinyi Dani koh daga ke Har Hyre zanyi ligis ligis daku
Hyre tafara Waka '''inda an girma asan an girma tana fada tashige ciki da sauri itama HADIZA tabi bayanta Don tasa hanli HASSANA sarai zata aikata abin da tace'''
Wollah HADIZA hawainiyar ki ta kiyaye Rama ta sabida Har ciki zan shigo in muku duka tsiya Marasa kunya banza
ALLAH ya baki Hakuri mai kashi daya Wanda bata Raina abin dambe
Zaki Ya ba inda nashigo wato nine mai kashi daya? Kin ci saa sauri nake zan fita da kinyi bayani
_Mukus Su ba HADIZA sukayi sabida tsoron abinda zai biyo baya_
Ummah wai Meyasa mallam yakasa miki aiki akan wanan Matan tunfa Muna yara take zaune ki tamiki duka tsiya ace shekaru wajan talatin Haryanzu
Barta kishi takeyi dani sabida daga hyhuwa farkon ta agidan Bayan suna asabe da Sati Biyu shine babanku ya aure ni shine tasamin wanan tsanar
Amma karki damu bayanzu Muna da kudi ba zanyi maganinta ai
Mallam tun dazun nake jiran dawowarka
Don ALLAH laifina ne da ALLAH yaba ma WALIYE miji Mai aziki?
Toh mai Nayi wa HASSANA take ta fadin cewa Sai taga bayamu
Ah lale HADIZA kinci ka alguguma bacin nashi go yanzu da shikenan Sai kuta gulma na
_Cire mayafi tayi ta daura a waist din ta irin ready to fight🤣_
Ammadu girma Ya fadi koh da yake banyi kanka bane an wanke anbaka kasha Shiyasa yanzu Sai abinda Tace
HASSANA Kinsa dalilin dayasa nadawo yanzu? Eh ?
Ina fama da ciwon Kai nadawo na huta Don ALLAH ku barni inji da abinda ke damuna
YOU ARE READING
NABEELA(RAYUWAR AURENA)
Non-FictionWanan Labarin Is based on True life story.. " "Labarine da ya kunshi abubuwa da dama akan Rayuwa da zamantakewa Auretaya" "Labarin Wata yarinya Yar shakara sha shida aduniya wacca ta taso a hanu kishiyoyi mamanta Alokacin da take tunani cewa wahal...
