page 57

442 36 10
                                        

*~Based on True life story~*

          
              NABEELA
*🤍(RAYUWAR AURENA)🤍*

BY THE DMKs✍🏻


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

~Wanan Labarin is based on True life story~✍🏻



Page 57

@ Mambilla

Wai ke kam HADIZA wai mai ke damun ki ne haka duk kin lalace saikace ba ke ba Aradu ALLAH bacin  na miki kallon tsab da sai nace bake bace

Hehehe Yo dole kinga ta a haka.. Matar da ta gama siyar da duk wani kadarorin ta wai zata yi kudin jigir ta tafi amurika niman WALIYE in banda abin HADIZA inata ina zuwa amurika ke ni koh hajji nan da Tace taje ban yarda ta je ba

HASSANA ya ishe ki haka  Aradu ALLAH in bahaka ba zan sauke miki duk abinda ke kaina

Hehehe sauke shi nace in ba ki sauke ba kin Raina kanki kinji koh

Haba HASSANA bai Kai ga haka ba

Toh ANDE wai ma hauka akeyi ace wai da lafiya na da komai wanan matsiyaciyar Matan tana gayamin magana Sai kace ni na cinye mata kudi zuwa amurika.. Nan nan Ammadu yasani da Hyre zuwa kano gidan WALIYE Amma akace mana basu dawo ba
Amma da yake matan nan bata da mutunci bata gada mutunci shine zata dinga gayamin magana

Ayi Hakuri HASSANA abin bai Kai haka ba..

ANDE kinji ki zo mushiga daga ciki

Oh wani munafinci za a Gila mata ah bashaka toh sai ayi mugani

ANDE dama Aramin kudi zakiyi dubu Ashirin zuwa karshen wata

Hehehe Yau kece da tambaya Aron kudi? Ah lallai bashaka abin mamaki duniya kenan tayi maki juyin mage

ANDE kinji nasa gona na a kasuwa Kuma ance Sai karshen wata

Toh badamuwa ki aiko anjima

A'ah yanzu ma Sai na biki na amsa

Toh shikenan

Yau wa gari ya waya anzo ana mana birgan banza da na hofi akan kudin iska

HASSANA ya ishe ki bawai gazawa nayi ba kudin ne baya hanuna Shiyasa kinji koh

Toh ina kudin suke? Kowa yasan babu duk birga ce da dashi ai baza a siyar da kadarorin ba hehehehe ALLAH nagodai

Toh an siyar in daice nawa ne bana wata katuwar ba

uban wa kk kira da katuwa eh? kinfa san halina wollah yanzu nan na murje ki a banza

Haba HASSANA ai girma yazo ai bama zai Kai ga haka ba Kuyi Hakuri Don ALLAH kinga mallam na kwance ba lafiya kar kusa shi cikin damuwa Kuma

Haba ANDE Kema Kisan Bazan biye mata bale mu tada mallam daga barci

Toh ki ma biye kigani in ba karyaki ba Yo hauka ma akeyi da za ace da lafiya na da komai wanan matsiyaciyar Matan tana gayamin magana Sai inyi sololiyo ina kallon ta kuma maganar mallam da kk yi kin damu dashi ne? Yaushe rabon da kije ki dubashi tunda yafara ciwon nan eh... Sai kinga mutane kifito kina mirsisi da ido kamar an murje gyada wai ke mai tausayi koh

Aradu ALLAH kifita idona na rufe

In naki fa? Mai zakiyi eh HADIZA? Nace mai zakiyi?

ALLAH ya baki Hakuri

Amin. Ai nadauka Magana zakiyi da kinji ki a kasa wollah

ANDE muje toh kinji

Toh HASSANA sai ALLAH ya kaimu ALLAH ya bashi lafiya yasa kaffara ce amin



NABEELA(RAYUWAR AURENA) Where stories live. Discover now