51

2.6K 209 1
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*littafin BABA MAI KOSAI*
Daga alkalamin marubuciyar bandariya da nishadi *AZUMIN ILU,ILU a BIRNI* da *HAKURI Da MASOYI*
wato *maman mamy* mai buhun nishadi,cikin salon ta na taskar bada dariya tazo ma na da *baba mai kosai* .ku biyo mu mu jibgi kosai ba wasa🤒😸

*Ena ta jira ena hange kar ku bari wannan lokacin yazo ya wuce ku ni naga draman don nayi harsashen soyayyan dake tahowa littafin HARSASHEN SO* daga alkalamim shaharariyar kamilar marubuciyar zamanin nan wato mrs *MEELAT MUSA*
ku zo muje mu leko 🤒🖊

Allah ya ba mu lpya dani da fans dina da dukkan yan uwa musulmi, mom khadie da ja'afar Allah ya dada baku sauki!



*Page▶51*

Kan gado ta koma ta na sauke numfashi duk haushin ta har yanxu bai ce mata komai ba amma kuma ai gashi ya dawo tare da zahida .

Wato wacce ya damu da ita kenan yaje ya nemo itakam ko oho.ta dan tabe baki tayi karamin tsuka

Nan cikin juyin nata taji an bude kofar,
Salma tace ke meye haka kin wani tafi kin barni nikadai

Tayi shiru ta sake yin juyi alaman tana fushi
Nan salma tace ikon Allah jasmine bana son iskanci fa kowa ready ya ke
Ke kawai ake jira aci abinci,

Tace too, sai yanzu kuka san dani awajen
Ai dama hade min kai kukayo,ke kuma
Har da wani gaisawa da ita ta karshe tana harar salman

Salma ta fashe da dariya
Tace daya daga cikin halin ki da nayi missing a wajen ki kenan
To ni dai bani da lokacin ki ehe, ki tashi muje muci abinci yaya ash ne fa yace ki sauko

Ta turo baki tace yaya ash? Toh bazan zo ba ya mutu mana in banzo na ci ba.
Bude baki salma tayi tace laaahhhh jasmine mijin kin ne zai mutu ?

Ta dada turo bakin tace eh mana, ai kina kallo bai ko kulani ba daya zo gidan kuma fa ahakan yafi sati fa awani wajen ni bansani ba.

Salma ta tabe baki tace to yi hakuri mana uwar gida ran gida....kemabai baki kula shi kuma kinga ai basu  zauna ba
Pls tashi muje kar ki kashe min su da yunwa

Nan ta tashi tana turo baki tace toh muje
Amma wallhy darajar yaya kamal yaci, indai dan su biyun nan ne sai dai su mutu ba zan zo ba

Haka dai salma ta ke lallabata har ta sa ta sake shiri ta gyara make up ta sake feshe  ta da turare mai dadi mai sanyi
Jasmine Duk Tana yi tana turo baki tana ta kukkuni har suka sauko.

Su kamal  sun zauna ready amma Ba wanda ya taba abincin don komai fresh aka jera yadda ashween yake so,

Ita kanta zahida Allah Allah take ayi serving din su tsaban hidiman tadi ta manta da chan kafin yaje abuja itake serving dinsa abinci na munafurci a gidan

Cous cous ne da garnished miyan oguleaf wanda kayi shi kamar pepper soup amma ba abunda babu aciki.

Sai sukayo fresh carrot and ginger drink mai kamshi komai an jere su gwanin sha'awa

Suna tahowa Sai yauki jasmine take musamman da taga ya dan  kalle ta farkon hada idon su

Nan salma ta dan ture ta alaman kar ta zauna sai tayi serving din su duka
Ba musu ta soma aikata hakan

Zahidan gaba daya sai satan kallon ta takeyi don bata so haka ba .

But kamal ya dauke mata kai da hira ba yadda ta iya dole tayi missing wannan chance din

Nan jasmine ta shiga serving dinsu gwanin sha'awa as matan gidan
Kowa ta sa masa tana zuwa kan zahida ta sa hannu ta karbe serving spoon din tace no thnks
Zan sa da kaina

Jasmine Ko ta amsa ta sake mata spoon ta juya abunta dama bakin cikin hakan take ji aranta
Tuni tayi tsiinin baki ta zo gefen salma zata zauna
Nan ma salma ta mata ido alaman kar ki sake ki karaso nan wajen zauna gefen mijin ki jor

Har ta soma sauya fuska zata bijire amma Lura da   yadda taga zahidan ke satan kallon sa ya sa kawai tabi shawaran salman ta zauna

Tana zama Sai da ya dan juya ya kalle ta cikin mamaki don baitaba tunanin zata ma zauna kusa da shi ba

Wajen shiru Kowa santi yake, ana hira jifa jifa,
Ita dai zahida she is not so comptble saboda gani take bakin salma da jasmine daya tunda taga kamar friends ne

Hiran ma in bawai kamal bane ya kwakwulo ba mai cewa kowa komi a tsakanin su ukun awajen

Ashween kam, ba a magana don sosai ciwon kewar matar sa ya motsa musamman daya ji ta daf da shi,
Dama ya dade bai ganta tana cin abinci gaban sa ba ,sai yanayi kamar baya kallon ta amma in reality yafi kowa gani da yaba kwalliyar nata a zuciyan sa.

Ana kammalawa haka salma ta sa ta agaba suka soma clearin don tuni salma ta yada cewa ai jasmine ne tayi musu dinner,kamal ko sai yabawa yake har da cewa taci kyautar car.

Karamin tsuka zahida ta ja aranta don duk hankalin ta bai kawo yar wannnan yarinyar zata iya dafa food haka ba don taci sosai ba karya,

Zahida ta dubi ashween dake zaune shiru tace baby,i need to talk to you

Wannan abun ba karamin kona wa salma rai yake ba amma sai ta bisu da kallo
A ranta tace hmm i wonder how jasmine take zama a gidan nan da wannan fitsarriyar mata dube ta fa,msww

Nan kamal yace mata itama mrs, bafa inda zakuje hirar yau damu za'ayi

Tayi murmushi ta amsa don taso ace sun koma daki ta tambaya jasmine meke faruwa?

Su ukun suka zauna wajen ana hira, kamal sai tsokanan jasmine yake don ya fahimci ba a dai dai take ba,daurewa kawai takeyi ana hirar da ita

Kusan minti 20 sai ga Ashween ya fito daga site din zahrod,
Wani abun ya sake gullin ta Ta kalle shi, tayi saurin kau da kai nan ta mike tsaye tace salma tashi muje mu kwanta bacci nakeji

Kamal ne yayi saurin goyan bayanta yace tohm gudnite,
Salma tace Allah ya tashe mu

Ashween dake jin su Sai ya tsaya yana kallon su duka
A ranshi yace kaji min mutanen nan sai kace hirar munafurci ena wajen zuwa ana tarwatsa taro ko..hmmm

Salma kam  kamar Allah Allah take su cige daga ciki,
Bayan sun kimtsa sun dawo sun zauna kan gado
Hakan salman ta sata a gaba tafada mata meke faruwa,kuma wacce xahida? Don ita tunda tasan jasmine tace yanada gf amma bata san wacece sabuwar ba inba tania ba

Nan jasmime ta zauna ta bata labarin komai duka abunda yake gudana
  Duk dama kafin tagama salma ta rarrashe ta yafi sau 30.don idon ta har sunyi ja  tsaban kuka.

Shiru salman tayi don Labarin sosai ya sa jikin ta yayi sanyi.

Ta sani sarai a yadda tasan jasmine da soyayyar yaya ash abune mai wuya ta zauna da kishiyar waje acikin gida musamman a wannan yanayi

Amma kuma a wani bangaren salman ta fahimci abubuwa masu dama a ranta sai tayi shiru tana nazari

Nan ta cigaba da bata baki ta rarrashe for the last time
tace mata suyi bacci ta kwantar da hankalin taa insha Allahu daga gobe matsalan ta akan su zahida ya kare..




*To Allah ya kaimu gobe muna jiran salma*🤒




*surriem*

SO MAKAMIN CUTATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang