55

4.7K 236 2
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶55*



Kusan mintina 20 suna zaune sai soyayar su suke faman sha tana kan zuba masa rigima gashi dama sunyi mugun missing juna a dan kwanaki da suka wuce suna fada.

Su biyu ne a dakin amma kamar ba su nan don ciki ciki suke maganan su kamar wani zaiji su
Ashween gaba daya ya wani bada hankalin sa kamar yana deban lectures tana rike da hannun sa shikuma ya  dan tallafo kansa daf  fuskn su na kallon juna

Yayi nisa bai jin komai  ji yayi ta dan tsame hannun ta cikin nashi da dan sauri ta juyo tana kallon  bakin kofa

Ido hudu tayi da karime dake bin zahida da tray din abinci,

dama a gidan  kowa da yadda yayi speacilising a fannin girki,
Ita karime ba irin counry food da bata iya ba har dana gargajiya ita oe dafa musu in bukata ta taso
don har catering clases ashween ya sata lokacin farkon zuwan ta gidan duk dama bai cika zama ba

ita kuma cook nana ta san kan continental dishes da kayan kwamulashe amma sai dai bata da hayaniya sosai kasan cewar ta tadan manyan ta kadan kuma bazaura ce.

Ashween Bai juya ba yana zaune daf da jsamine ,har zahidan ta iso tayi tsaye a kansa .
Baby ga break fast din,

Yace ok, nan karime ta ajiye gaban sa akasa tayi saurin ficewa ta basu guri

Bai jira ba ya shiga budewa yana gani ba laifi pepper chicken ne wanda yaji komai da komai gwanin sha' awa  sai akayi dan  french mosaic na breadi wanda yaji koyi sai tea wanda aka hado masa kayan qamshi, mint da kayan yaji,

Wai a hakan duk sun kure a daka ne wajen girkin don muddin jasmine taci zata samu qwari ta warke.

karime ce tabi ta ruda zahidan tun a kitchen tace mata ai sanyi ne ke damun jasmine shine  take barbaran namiji ,
sabida haka Ta san maganin ta yanzu zata warware in aka hado mata breakfast mai kayan yaji yaji..

Jasmine Kallon abinci tayi sai ma taji ya fice mata akai, don tasan bata bukatar wani abu daga wajen su biyu har cikin ranta.

Ya kalle ta tare da kashe muryan da baisan ma yayi ba yace 'oya tashi haka food is ready,ya dan zare mata ido yace
Kar kice min kuma ba zaki ci..

Tayi shiru ta shashantar da fuska
Tana son tayi magana amma sai ta kasa yi

Tuni zahida ke aiko mata bomabaman harara   
Ita dai Tayi musu tsayuwan babakere ne tana jiran taga me zai faru

Ganin ya nace sai taci ya sata  dan dole ta amince zata tashi da kanta taci
Ai kamar da wasa jasmine tana danyin yunkuri zata mike ta sake wani uban kara sai da dukan su suka farga suka kalle ta

Zahida tace lpyar ki kuwa jasmine?

Ta shagwabe ko ta kula ta ta dube sa da fuskan kuka  tace yaya ni zafi nake ji bazan iya tashi ba Allah..

Sai da yaji wani dum a ransa yace o.m.g yau jasmine zata kunna min wutar fitinan anan wajen kenan

Sai yayi saurin waskewa cikin kulawa ya ce sannu,sorry.. sannu kinji,

Zahida ta danyi tsuka ta kau da kai sai can tace baby wai nikam faduwa tayi ne? Naji tana cewa zafi take ji meye ke mata zafin?

Dama Zuciyan sa sam ba a kwance yake da presncw din zahidan ba ba don yasan inba sakalci irin natan ba ma yadda jasmine ke narke masa tana shagwaba yaci ace ta dago wani abun.
amma sai Ya mata shiru bai amsa tambayar nata ba can kasan makoshi yace eh

SO MAKAMIN CUTAOnde histórias criam vida. Descubra agora