*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶74*
Tun tafiyar ashween mamy ke kuka sosai a dakin ta dama dauriya kawai tayi don aganin ta hakan ne kadai zaisa ta karbe ma jasmine yancin ta nan gaba.
Abban ashraf ya shigo baice uffan ba ya dawo gefen ta ya zauna.
Dama yana cikin masallaci ake hayaniyan amma da shike itace ke da alhakin su duka biyu sai ya zuba mata ido yaga kalar nata hukun cin.
Kuka take yi kanta a kasa kamar wacce tayi laifi sai yace kiyi hakuri hadiza kukan ai ya'isa haka
Its so obvious that u cant hurt sumone witout hurting urself,
Ni aganina hadiza anya harshen ki baiyi tsauri akan yaron nan ba?Wai Duk akan ya kawo wata mata cikin hidiman ...gaskiya banji dadin kalaman ki ba .
Na dauka zaki bi abun a sannu ai ashween yaro ne
na tabbata ko shahiida na raye yau bazata taba furta masa haka.kiyi tunani daiNan ta dago murya a sanyaye tace nasani alhj,na sani.
Amma kuma hakan nayi niyya nafi so nagaya masa hakan shyasa kuma na fada.
Kaiwa nan ta tashi ta fuce abuntaGirgiza kai kawai yayi yace toh Allah ya kyauta
Gefen ashween kuwa a lokacin Ya turo kofar ammyn ciki da karfi idon sa sun rufe baya ma ganin gaban sa sai ya soma tahowa enda shimfidar ammyn yake nan ya zube gwuwir sa a kasa yana kan kuka mai cin rai.
Koran sunan ta yake Tamkar a gaban ta yake.
Yace" dan Allah ki dawo ammy nasan zaki saurare ni,come bak to me mother i ne..e.d you.
Nan ya cigaba Ya fada ya sake maimai tawaHar ya kife kansa akan gadon"bai fasa ba can kasan makoshi yake cewa ke daban ce ammy nasan ba zaki taba rabuwa da ni ba har abada kina so na ,ke kadai kika san ena kaunar ku baki daya kuma bazan taba butulce miki ba bare na ci amanan ki,
Bakin sa har na rawa yace i love her ,ena son jasmine ammy ki zo ki fada musu, pls come bak bazan iya rayuwa na a hakan ba
.
Babu ke babu jasmine banda farin ciki
today i feel so guilty an scared
Ki taimaka min ki dawo mana
,.. sai ya lumshe ido yana dada matso zafafan hawayen sa yana jan katifan da hannun sa cikin tsananin tashin hankali da firgici bai masan meya keyi baA Brain dinsa Ya rasa maganan wanne daya cikin jasmine da mamy zai dena tunawa don ya samo sauki ma zuciyan sa.
Duk da ma yasan maganan mamy yafi masa ciwo amma har yanzu yana jin tsananin bakin ciki kufcewar jasmine a rayuwar sa.
Wani Bacci mai nauyi ne bazata ya dauke shi a wajen a tsugune kan gwiwar sa.
Cikin baccin yake jin yadda ake shafo suman kansa ana calming dinsa amma Allah baiyi zai iya juyawa ya ga waye ba ne
Tsaban yadda yake jin dadin yadda ake calming dinsa sa shafowar kan ya sa shi jin dama dama a ransa.
Amma sai ya shiga cikin zulumi to waye yake rarrashin sa haka.Sai ya budi baki yace ammy na ke ne?shiru baiji an amsa ba.ya dan ja ajiyan zuciya yace pls come back to me mother ki zo ki saurare kice mamy ta bani mata ta wallhy ena son ta ... Bayan nan shiru yayi kamar wanda aka ce masa yayi
Chan kuma sai komai ya dauke masa kamar film firgit ya bude idon sa yaga sarari ashe shika dai ne ba kowa
Wani perfect silence ne ya dada ratsa dakin aka barshi da rarraba ido a tsugune a kan kafar sa,
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez