*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶67*
Tun kafin Ash ya dawo dakin jasmine ta daddafa ta kimtsa kanta tayo sallah
Sai dai tanayi ne amma jikin ta har rawa yake tsaban zazzabin da ya rufe ta
Anan kan daddumar tayi dukunkune waje daya ta kwanta kamar wanda ruwa ya kwaso ta.Yana shigowa ya karaso daf da ita ya dan dago ta
A hankali ya maida ta kan kafar sa ta kwanta tana maida wahallen numfashi,
Gaba daya duniya tayi masa zafi har yanzu bai jin zai iya yafe ma kansa da halin da jasmine ke shiga ciki akan sa ba.Ya dade yana kallon ta yana shafo fuskan ta a hankali ita ma tayi shiru tana kallon sa
cikin zuciyan sa fall yake da tausayin ta gaba daya idon sa suka ciko da hawaye amma sun kasa saukowa.
Ganin damuwar dake kan fuskan sa ya sa ta daure ta kamo hannun sa da niyyar zata rarrashe shi, bata ma bude baki ba ya soma zubda hawayen a hankali,sai tayi yunkurin tashi cikin firgici zatayi masa magana ya ce no princess,kar ki tashi kwanta kawai doc ya kusa karasowa
Pls, kinga baki jin dadi ko?
bakin ta har na bari tayi yunkuri
Tace masa no, im fine,ya girgiza mata kai wani hawayen na kan droping yayi mata alaman bai yarda ba
itama sai ta langwame masa jiki cikin sanyin murya tace yaya shine kake kuka ko? To me na maka,?ai Ba laifi na bane nake ciwon kayi hakuri mana.ta karashe da muryan kuka.Sai Ya danyi smiles hawayen na shi na dada zuba yace i know,ba laifin ki bane princess komai laifi na ne...pls forgive me kinji? i just hate to c u like dis.
bata ce komai ba ta sa hannu ta share masa hawayen tana turo baki cikin dauriya ta shagwabe tace one more tears frm u and i wll neva forgive u.
Yayi murmushi ya dada rungumo ta yace ro shikenan.. anything for u gal.A haka suka jira likita har ya zo ya dan duba ta,allura kawai ya bata sannan ya musu bayanin
Effect din maganin ne kawai yayi saura amma zai washe kafin ta tashi a bacci,
Sannan a tabbata an bata well balanced diet bayan ta tashi saboda ya raba ta da shi a hanyar jinin ta yace komai zai dawo normal in sha Allah.
Ash yay godiya,..sannan doc ya fice.Tun da aka mata Allura idon ta keyin dishi dishi kamar ta shawu,
Ya kama hannun ta tana kwance kan gado chan ta soma surutu tana ce masa i love you,yayi shiru yana rike da hannun ta yana kallon ta da wannan kalmar a bakin ta har ta yi bacci.Sai yayi kissing forehead dinta ya gyara mata kwanciya yace i love you more princess.sannan ya fita.
Kafin nan zahida ta nan har yanzu a sume
Ga Hannun sa har yayi layi a wuyan ta wajen yayi jajir dabn da fatan jikin ta.Bibiyan hanya karime take yi amma shiru har karfe 12 rana bata ga zahida ba.
Shine ta yanke hukuncin shiga dakin anan ta samu ta taimaka mata har ta farfado a gigice tare da wani irin kuka
'kukan kawai take yi tana cewa shikenan mumy ta cuce ni na shiga uku ash ya rabu dani,
Bata ji bata sauraran kowa ta haukace ta zauce ko tsayawa sauya kayan jikin ta batayi ba shiga dura zage zage tana cewa wallhy bazata tafi ta bar gidan ba dole sai ya aure ta
sosai hauka ya soma bayyana mata lokaci guda tana fincike fincike tana fashe fasheHankalin karime yayi mugun tashi don bata taba ganin irin wannan tashin hankali ba.
Haka tayi har ta gaji ta koma ta kwanta a kasa ta cigaba da kuka tana kiran sunan sa tana cewa "pls dont leave me Ash i love u..ta nayi tana maimaitawa
Har zazzzabi mai zafi rufe ta,
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez