*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶65*
Yanxu Jasmine ita kadai ce a gidan ba zahida bare kuma Ashween,yau satin sa biyu kenan achan porland
Itama Dan dolen ta tayi hakuri ta danne missing din nasa tana karatun ta sosai a gida,
shikan sa bai samun lokacin waya da ita sai dare.Tana cikin juyin ta a daki salma ta kira suka cigaba da hirar su, enda take dada mata godiya akan taji dadi sosai da shawarwarin ta,
Gashi yanzun zahida da kafarta ta bar mata gidan ita kadai ba wani tashin hankali.Salma tace ai dama nafada miki ,abun duk hakuri ne da juriya kedai kiyi kokari kiga hakan ya kasance har abada,ya samu ya rabu da ita kwata kwata har ki dawo masa one and only,
itama matar akwai shegen rashin zuciya da naciya salma ta karashe cikin karaman dariya
Jasmine tace hmmm barta kawai salma,ai wallhy ena dai dai da ita yanzun.
Hirar da suke yi kenan, salma ta dada karfafa mata gwiwa har suka katse wayarDaga gidan mrs rod chan abuja,
Zaune take gefen zahida tana rarrashin ta tace beauty wai meye sa kike da taurin kai ne haka?
Na gaya miki ga abunda yace still har yanzu baki sauko kin sa ranar komawa yolan ba?Dan tears dinta ta goge tace mum,Yanzu kin goyi bayan ya dinga min irin wannan cin fuskar ena kallon sa ko? I told you wallhy da ido na gani he's becoming too intimate da yarinyar nan,i just hope he's not fooling me.
Madam hidayat ta dan murmusa tace c'mon zahida, kishi karya rufe miki ido mana
Ash fa ya gaya min abunda ya faru kece ma baki da gaskiya, ba ance ta baki hakuri ba meyasa kika ki hakura.?He even told me dat kina raising masa voice da haka zaki cimma burin naki?
Xahida Tayi shiru chan tace " u wont understand mum,
Nikadai nake jin abun da nakeji a gidan
I think Ash is into dat girl, mum wallhy son ta yakeyi.Mrs rod tace da Allah kimin shiru, ena nuna miki gabar kina hanyar arewa kishi hauka ne ?
Ni yanzu abunda nake so dake ki tattara ki koma yolan tunda yace shi bazai zo nan ba.
Atleast ki samu ma ki danyi relax a gidan dis week zai dawo daga porland .
Ba sai kuma na fada miki ba u know what to do ko?Ta dan turo baki tace haba mum, wallhy nagaji kawai nike nan ya dinga cutar dani ena gani amma kullum ace na saukar mai da kai na bisa..
Ta watso ma ta harara tace "Just shut up zahida.
Toh shikenan sai ki zauna anan ki rike girman kan kin har saiya auri wancan din sai ki sauko.Nan ta fashe da kuka tace mumy ki daina gaya min haka dan Allah,ash ni kawai zai aura
Mrs rod tace ,aikin vanza ai baki sa niyya ba.to mezance miki yanzu?,look just get up girl kije ki lallaba sa ki samu kiyi amfani da maganin nan in the next 3 weeks a soma maganan auren ku..
Sai ta gyada kai kalar tausayi tana goge hawayen ta ta ce toh naji mummy gobe zan koma yola,.
Tace good for u.oya tashi ki kimtsa kanki bana son kukan nan ..sai ta fice ta barta.
Ashween ya gama zakuwa ya dawo wa matar sa don kwana biyun gaba daya sha'a warta na mugun damun sa..duk dama video call din za'ayi kamar ba za'a gama ba, da kuka da komai suke rabowa kan ayi bacci amma still yana Allah Allah yaji shi a nigeria.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
SO MAKAMIN CUTA
Художественная прозаIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez