*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
👏🏻my people.💯🙌🏾
*Page▶35*
Zahida Dakin ta ta nufa da gudu tayi banging kofar da karfi ta zube kasa ta kife kanta tana numfashi sama sama
Abunda bata son ji a rayuwan ta kwata kwata ranar shi takeji aranta
Kuka ne ya kufce mata sosai, don kuwa bakin cikin dan uwanta jamal, da na maganan da sukayi da mrs hidayat din suka taru duka suna mata zafi
Sai kuma ace ta dawo ta tarar ga wannan al'amrin su ashween din??
Buga kanta tayi da hannun ta kamar wacce ke neman seta notin brain din ta da suka doma kwancewa
Tayi lakwas zuciyan ta ya cunkushe Gaba daya ta rude ta rasa me zata dauka guda daya, wai meye ashween ya keyi da wannan yarinyar,?
Ta tambayi kantaSai dai Kafin zuciyan ta ya bata amsa,nan taji ya zura key ta waje ya bude kofar ya shigo
Maimakon taga alamar saukar da kai ko ya lallaba ta sai ma ya daure fuska tam ya harde hannu yana hucin karya,Duk da abun da ke mata zafi a lokacin Mamaki ne ya sata mikewa tsaye tayi galala tana kallon yanayin sa,
Ko ajikin sa 'kallo ma ya bita da shi ba kunya yace wai meye hakan kikeyi ne zahida? Lpyar ki kuwa
Ai bata bari ma ya kara budan baki ba tace, i shud be asking you dat ash,
Lpyar ka kuwa? Kace min yarinyar nan causin dinka ce but u almost kissed her.
ni sam bana fahimtar relationship din ka da ita, and i hate it.. tafada cikin ihu da bacin rai,
Ido kawai ya zuba mata har ta gama, ya dake kamar abun bai taba zuciyan sa ba ,don harga Allah ya san zahida tana cikin tashin hankali don kusan kalar kishin su daya yake da jasmine din sa in sunayi idon su a rufe take.
Maganganu take tana cewa ' Dama Allah Allah kakeyi kaji bana nan a gidan nan ka manne mata, baka ganni ba baka neme ni ba,sannan na kira waya kaki ka dauka..wai wannan din wace irin cousin ce haka are you two in love?
Bai amsa ba, itama
Bata gaji ba, sai uban bori take tana ruwan kuka ta ma ki zama waje daya, tace in dama hado ka akayi da ita don tazo ta kwace min kai wallhy ba ta isa ba,karya take yi.. ure mine.
Duk wanda yace zai raba ni da kai kuma sai na...Ya datakar da ita a tsawace yace, Zahida!!!!!duk wanda yace zai raba mu zaki kashe shi ko?ohhh i see.dama dagan gan kenan kika kashe min tania,huh? Ya karashe a tsawace
Ai Tsit tayi kamar an kashe generator,ta na zare ido tana kallon sa
yadda taga ya kunno kai yana tahowa kanta fuska ba alaman rahma 'ya dada tsorata ta sai bari take,
Ai ba shiri ya jawo ta ya hada ta da bango yana kallon rinannun idanunta da har sun soma kumbura tsaban fitinan kuka,Yace' Zahida, ta dago sukayi ido hudu"
Nace ba zaki taba jasmine ba, are we clear.?
Dan dolen ta ta gyada kai cikin sauri,tace eh,
don muryan da yasa yayi maganan tasan ba wasa a cikin ta.Nan ya dan sassauto ya sake ta yace sai ki cigaba da haukar da kikeyi, na lura duk maganan da nake fada miki a banza kike daukar sa ,kinsa jaraban kishi a ran ki kina zubar da girman ki gaban karamar yarinya wacce akalla kin bata almost 10 to 11 yrs.whts is wrong with u zahida?
Har kina cewa kin tafi ban neme ki ba,ai da kin damu dani zaki gaya min kin fice agidan nan ba dai da kikaje kika dawo ba and now
U wanna know why kullum nake manne da ita?
Nan ma tsit tayi ta dukar da kai kasa
Yace Saboda ke kinki kula min da ita ne kin nuna min baki son ta,kin tsane ta, and Wht do u expect?
Na zuba ido na barta ta mutu don ke ko me.Bai fasa ba ,Wani uban harara yabi ya watsa mata yace look woman,in fa bazaki iya zama anan ba ki tattara ki tafi gidan ku am tired, haba da Allah .bai jira tayi wani motsi kwakwarra ba
Kaiwa nan ya fice a fusace ya bartanan tayi tsuru tsuru ta ma rasa gane mai guda daya ke mata zafi,
'"Hmm lallai hausawa sunce ciwon da baka iya gani ko tabawa ya fi ciwon da kake gani kiri kiri zafi.Ranar gaba daya zahida ba ta je ko ena ba anan ta kwanta abun duniya ya bi ya dame ta
'
Shi kam tuni ya shirya ko dakin jasmine din baiyi ba ya tafi office abunsa.*Hhhh hege ashween😂*
*Need ur pryers friends ciki na na ciwo😪😪 sai dare zamu hadu insha Allah*
*surriem*
![](https://img.wattpad.com/cover/154404985-288-k381767.jpg)
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez