21

2.3K 209 5
                                    

.

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

  '''

Kadan daga cikin amfanin APPLE DA PEAR ( AVOCADO) wa ya mace
#👉🏿babban aikin su yafi la'akari da kara wa mace sinadarin fibre a jikin ta,wanda kowa ya sani abinci ne mai muhimmanci ma mahaifar mace,zai gyara shi,zai tace shi sannan ya mikar da sassan jijiyoyin jini da ke tattare da shi nan kaji mahaifa na aikinsa  da kyuw ba matsala ba magani, mahaifa yana samun kashi 99% na karfi da lpya wa macen da ta lamunci cin wayannan fruits din musamman pear(avocado) don yafi apple dauke da sinadarin fibre...sannan suna gyra jikin mace su sa tayi fresh suna hana fitowar gurajen fuska..''' ....
*tested and trusted*
 
👉🏿 _ga yadda fruits yake amfani ajikin mutum ya samu sakamako cikin sauri da inganci_
*# yafi kyu kaci fruits on empty stomach lokacin bakomai a cikin ka misali da safe bayan ansha ruwa sai a yayyan ka su a ci 20..30.45.minutes atleast kafin kaci abinci mai nauyi*
*Note-cin fruits bayan an kammala abinci yana da hatsari saboda reaction din wasu sinadarin sukan iya zama poison ma lpyar wasu sassan jikin mu ko za'a ci a bada lokaci kadan koda 10 mints ne*
#Nagode.



*Page▶21*


Suna zaune a haka Bayan kamar minti 5 ya dube ta yace ci mana? Zai huce fa,

Nan ne ta daga transparent glass din da aka rufe  abincin ta ajiye gefe
Shi dai baice uffan ba don fruits din ya so ta soma sawa a cikin ta
Nan ta soma chaka spoon kamar mai jin tausayin abincin tana juyawa
Dan kadan ta deba tana kaiwa baki tayi jefa da spoon din ta rike bakin ta
Tana yarfa hannu alaman ya kona ta,

Sorry ,ya fada tare da dauko ruwa ya mika mata
Gyada kai tayi ta karba

tana kallon sa shima ya taba abincin da spoon yakai bakin sa, sai dai shi ana shi baiji wani zafin da zai kona mutum ba
Gani tayi ya jawo stool ta gaba ya zauna yana fuskantar ta,..
A sanyaye ta ajiye goran  ruwa shi kam lokacin har yayi ready da sliced banana and strawberry a spoon yana jira ta bude bakin ta,
Da farko Kamar bazata karba ba ,amma kan kace wani abu ,abu sai tafiya cikin ta yake ham ham har ya rage saura pieces biyu a plate din
" take ta soma jin dan karfi ajikin ta fiye da na da ,don dama hikamar sa kenan
Yasan Banana da berries na da sinadarin sa mutum  farin ciki da warware jijiyoyin damuwa a kwakwlwa.

    Yana kawo cokali na kusa da karshe  ta girgiza  masa  kai alaman bazata karva ba,
Yi hakuri yace ba yabo ba fallasa,
Nan tace na koshi da wannan kai kaci mana...

Muryan data sa tayi maganan ne ya so ya bashi dariya amma sai ya kimtsa yace
Ni bana jin yunwa jasmine wannan naki ne,so just eat

Da sauri ta shiga make kafadarta kamr baby tana cewa ai nima ba yunwa nace enaji ba ka ke bani abincin
Tunda naci kaima sai kaci ai,,

Murmushi ne ya kufce masa
Amma sai ya fizge a dabarance zaiyi magana yaga ta  dau spoon din ta kwaso sauran banana da beries din
Tana yunkurin mika masa a baki..
Wani kasalallen kallo ya bita dashi ba musu ya bude bakin sa ya amsa
    Har wani ajiyan zuciya tayi cikin sauri ta sake dauko na karshen bai ma gama na bakin sa ba ta sake dura masa,
Sannan taji dai dai

   Dan kadan ya kurba drinks din ta ya ajiye
Sai wani kallon sa take ,ba daga ido
Cikin haka har ya kai ga a hankali ta soma tunanin shi din bana ta bane,zuciyar sa na wata ce ba ita ba "duk da ma tasan zAsuyi aure nan da kwana kadan 
Tabbas zahida ce a zuciyar sa ,
Take ta soma jin wani zafi aranta mood din ta ya sauya
To meye sa ammy zata takura ma yaya ya aure wacce bai so?  Auren alkawari kenan zaiyi da ni?tace Wayyo Allah Na shiga uku

Ni kenan an raba ni da soyayyar yaya ashraf har abada ba wanda zai so ni kenan sai dai nawa soyayyar yaya ash ya zamo min makamin cutar da kaina?

Wani dada langwame fuska tayi ta cigaba""Ammy ke kika hada wannan abun
Pls come back ammy na, yay ash bani yake so ba kikace ya aure ni kuma wallhy ena son sa bazan iya jurewa ba....nan wasu zAfafan hawaye suka biyo kan kuncin ta,.again

""Jasmine... ya fada a dan tsawace
Wai meye haka ne dan Allah ...kukan nan bazai kare bane?
Wai ko so kike kiga na bar miki gidan kafin .....

Jin hakan daya fada ma ya kara dada hura mata zafin dake ranta
Luf tayi da kanta akan cinyarta tana kuka abun ta,
Iya surutu da fadan yayi amma sam taki kulasa karshe da kansa ya hakura ya koma kan sofa ya same ta

   Daf da ita ya zauna ya riko ta ,fizgewa take alaman tayi fushi"don itakam kishin sa ne da tunanin matsayin da zAta koma awajen sa in sukayi aure ke damun ta  yanzu

kan sa ne ya dada kullewa har ya soma tunanin ko don fadan daya mata ne  ya sata ke fushi haka.

Bai hakura ba  Cikin lallashi ya raba kanta da kan cinyar ta ya jawo ta jikin sa,
Yadda taji ya rungume ta yasa ta sauke karamin numfashi
Sai wani zirr take ji a brain dinta Musamman data ji ya kwntar da murya yana bata hakurin laifin da baiyi ba

   Da kyar tayi shiru ta dena kukan amma tana lafe kan kirjin sa shikuma ya jingina da sofa idonsa a lumshe
Jin ta shiga Wasa da dan yatsun sa yasa yace".me ya saki kuka jasmine ,nine?

Dan shiru tayi chan sai tace bakai bane

Da sauri yace to waye ne?
" Nan ma ta shiga muhawara da zuciyan ta """tunda aure na zaiyi
In fada masa ena son sa in yaso yaa san yadda zaiyi dani ?No' ai shi baya sona to meyey na fada masa? Ai sai ya raina ki ,,,wani bangaren yace
Shifa na miji ne zai ma iya auro ta daga baya,na rasa soyayyar yay ashraf na rasa na yaya ash? Tabbbb kenan na cutu ?

.. nan ta budi Baki da azamanta ba  kunya tace
Yaya ni bana son....au. ..
Sai maganan ya dauke mata chak a baki ganin yadda ya dago ta ya susutar da oily eyes dinsa ya zuba a nata

Ehem? Baki son meye jasmine ki fada min
..
Cikin dauriyar da batasan zata iya ba tace bana son auren nan
Ni yaya ashraf nake so"
Nan take hawaye suka biyo baya

Wani irin mugun duka kirjin sa yayi lokaci guda idon sa suka rine
Kamar ya wanka mata mari haka yake ji don kishi....amma sai ya danne zuciyar sa yayi calming din kansa ya riko hannayen ta,kamr baiji komai ba

Toh Kiyi hakuri bani nace zN miki dole ki aure ni ki bar ashraf din naki ba,
Ammmy ce, ko kin manta ke kika amsa mata kin amince? Ko zaki karya alkwarin nata ne?

Cikin jin kunyar abun da tayo ta sunkuyar dakai ba tace uffan ba,
Zuciyan tane ke cike tam da haushin kasa danne tunanin ta a kowani lokaci inta na gaban sa..

Chan ta budi baki Murya dishi dishi tace im sorry,

yaya naga wai kaima kanada wacce kake so ne ai kuma fa aure zamuyi

Nan ya tari numfashin ta shima yace
Haka ne,enada wacce nake so
Amma ke bazaki so ki cika ma ammy burin ta bane?

Duk da amsar ya kona mata rai
Haka ta daure ta gyada kai ta koma ta kwanta jikin sa

Shiru ne ya ratsa wajen,kowa da abunda ke masa zafi
   Ganin zai iya jefa kansa matsala ya sa ya kauda tunanin tan

Nan ya takura ta suka ci noodles din
Har yayi nasara hankalin ta ya dan kwanta kafin ya fice a dakin

🙂😌


*suriem*

SO MAKAMIN CUTATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang