*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶81*
Ranar da suka dawo daga ukraine kamar zai mata kuka dan zaman su acan tare kullum yana jin duminta ya ke ganin kamar kar ta koma gidan mamy kuma...
Ko itama bata ji dadi ba amma haka take yin dauriya ta lallashe shi don farin cikin daya ke sata in suna tare kullum abune wanda take jin tana mugun bukata kamar yadda rai yake bukatan numfashi .
a ranta tace, im not ready for any trouble ne kawai da wallhy en nazo wajen miji na bazan koma ko ena ba sai dai ayi min duk abunda za'ayi..
Yanzun bata kaunar abunda zai sa yayi nisa da ita ne shiyasa take bin komai a sannu sannu da mamy.
Ita ma zahida wani aikin ne ya sata dole ta bugo waya ta sanar da shi zata l dawo nigeria urgent cikin garin abuja washe gari sai tayi 2days kafin ta koma.
akan lallai yazo ya same ta anan din,don duk a tunanin ta har yanzu yana chan lagos ne.
Mrs hidayat,ena fatan kinzo da cikakken shirin ki kinsan wannan malamin ya gabata wajen aikin so, bana son sanya ta wajen ki..cewar kawar ta magajiya
Mrs rod tace,tabbas na shirya mana,jiya fa gwalagwai na na siyar ma sake hada wasu kudi,ta cije baki cikin dacin rai ta kuma cewa ke me kawai baki san yadda nake bukatar aikin nan ba ma ashe.
Magajiya tace,hmmm shikenan ta shi muje nikam ai mai sauki ne
Ba bata lokaci suka kama hanya tafiyar minti 50 kafin suka iso wajen.Gida ne na almajirai da gardawa manya bakake kirin kirar maguzawa sai dai kowa na harkan gaban sa
Daga gaban gidan zaka gani kamar wani abun arxiki ake yi aciki
Amma kana zaga wa baya nan zaka soma ganin safaran manyan motoci da jifajifai ana zuwa ana tafiya.Suma mra rod sai suka zauna akan layi cikin wani zaure har aka iso kansu.
Suna shiga ciki
Mrz rod jiki na bari ta tsuguna gaban malam dake zaune akan buzo idon sa yayi baki kirin,ta zuba gaisuwan ban girmaYa dube ta closely kamar mai karanta wani abu a disturbed face dinta sai ya tuntsire da dariya marrar dadin ji
Nan Suka kalli juna da magajiya
Baki na rawa tace malam lpya dai ko?Yace kunsan doka na ai ba sai an mun bayani ba na gane matsalar ki...
Tayi lamo cikin yanayin jimami tace toh malam ka taimaka min mana,
Sai yayi dariya ya nuna mata wani bakin kasko alaman ta zuba masa kudin aikin sa.
Ba laifi mrs rod ta zaro bunch 500k ta ajiye su..Sai ya cigaba da zane zanen sa akan kasa yana buge buge..
Kusan minti 15 yanayi yana dagowa yana kallon ta da wani irin fuska mai tsoratar wa..
Hankalin ta ya dada tashi sai suka kasa magana tsaban fargaba ita da magajiya
Malam ya dago ya cire nadin kansa tare da dauko wani bakin ruwa a kwarya ya ce zo ki wanke hannu da fuska..
Ba musu tayi hakan ,sai ya mika mata dan karamin madubi yace dubi nan" tana kai idon ta maimakon taga fuskan ta sai ta ga na barister saminu
Wani irin shock ta shiga tace kan uban nan..bura uba saminu?
Malam ya danyi dariya ...yace shine karamin alhakin da ya shiga rayuwar yarinyar ki kwanan nan don ya tono asirin ki..
VOUS LISEZ
SO MAKAMIN CUTA
Fiction généraleIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez