82

2.8K 210 2
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶82*



Da yamma Tunda aka sanar da mrs rod zahida na babban offishin ta na zahrod fashion designs wato nan inda ta soma ganin ashween.
sai ta shiga shirye shiryen yadda zata tinkare ta da maganan.

Duk da ma  zahida ta riga ta sa dokan kar a sake abar wani mai kama da hidayat ma bare ita ya shiga enda take..

Mrs rod Bata daddara ba washe gari da safen Allah ta zo tayi zaman diris bakin gate tasan dai dole zahida zata zo shigewa ciki so dole zasu hadu.

Tun 7.12am tana zaune ga yunwa na cinta amma haka ta daure ta kai har wajen 9.45am.
A  lokacin ne da wata dankarren ford formatic ta dosu bakin gate

Ko ba afada ma tasan zahidan ce aciki saboda haka da  ta mike tsaye cikin sauri ta bi bayan motar da gudu kamar mahaukaciya..

Daf gate security suka rirriko ta suna cewa madam pls go away, ta fizge cikin dagon murya tana cewa i want to see my doughter, ta kwalla mata kira da karfi tana cewa Zahida, zahida....kamar kanta zai tsage tana kan leke.

Ran kuwa zahida in yayi dubu ya baci musamman da taga yadda mrs rod take hauka tana jan hankalin mutane..

Da ta so ta bari ne a wulakanta ta sosai sannan ta kore ta..
amma kuma sai ta yanke hukuncin fitowa da kanta kawai don jin me ya kawo ta.

Tana tafiyan ta cikin kasaita,ladies suit ne tasa baki da pitch ta sha kyau uwa sarauniyar duniya musamman da ta maka katoton spectaclez baka a cute face din ta...

Cikin rigima da jan aji ta iso batare da tace komai ba aka matsa aka shiga bata wuri.

Ganin hakan ya sa mrs rod dada tunkaro ta da sauri tana cewa ki saurare ni zahida maganan da zan fada miki zai taimake ki..

Zahida na tsaye ba tace uffan ba ga mrs rod agaban ta tana kan maganan tana kai hannu daf zata taba ta sai ta wanka mata wani lafiyayayen mari"

Tace kar ki sake kawo evil hands dinki jiki na you witch,
Wai wayace miki ena bukatar taimakon ki?cioin zare da ido da masifa ta cigaba da cewa
Ohhh i see' haukan ne yau ya taso ta kaina ?mrs hidayat tayi shiru tan bin zahida da kallo,
anan ma
Sai ta dan jawo ta da karfi in a disrespecting and disgraceful way tace hidayat maza ki bar min nan gurin kar ki zubar min da mutunci na don ke bashi kike da shi ba wicked monster, ta karashe tare da tura ta gefe,

Mrs hidayat ta tsaya shiru gashi angama chinchirindo a kansu ana kallon ta,, ranta a bace yake amma cikin zuciyan ta ta kudiri niyyar duk ritsi sai ta fada ma zahida maganan nan amma ya za'ayi tafada wannan  Babban magana agaban mutane?  Take tayi kasa ta zube kan gwiwar ta ta kamo kafar zahida don tasan zahidan tan akwai rauniin zuciya

tuni saita sauya murya kalar tausayi  tace haba zahida ,ni fa uwa ce
duk da nasan na cancanci duk wani wulakanci awajen ki.
Amma ena so ki daure ki saurare ni na gaya miki abunda ke tafe dani dan Allah..
bazan iya fada Anan bane don ena kaunar ki sosai har yanzu yata ki tuna fa nina raine ki na kula da ke pls beauty ki saurari mum din ki mana..

Zahida da tuni abun ya ratsa ta amma sai fiske ta dada daure fuska, tana so ta saurara amma Sai ta kasa yanke hukunci  don sam sam bata jin ko digon yarda tsakanin ta da mrs hidayat yanzu..

Kawai sai ta juya zata  koma ciki abun ta mrs rod tasake dukar da kai kasa tace zahida pls dont go and leave me here ki saurare ni kiji

Zahidan ta ja tsaki amma abun na dada damunta ta sai dai takasa furtawa,
Ko da ta juyo
Bata ce ma mrs komai ba
kawai sai ta sauke bala'in akan mutanen da ma'aikatan da suka taru suna kallon Draman

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now