19

2.2K 227 0
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*This page is for yhu besty..asmeenat zeeyan*

'''My people'😜''
😪😪😪



*Page▶19*

Kusan minti 10  da rasuwar ammy awajen basu sani ba don Jasmine da hjiya hadiza Shiruuuu sukayi ba wanda yace uffan sai abunda zuciyar su ke rayawa

Sannan Allah bai basu ikon duba ammyn ba duk sun dauka hutawa take yi.. Dadin karawa  ma da shike ko kadan fuskan ta bai yi kama dana mutacciya ba

  A gefen ashween kuwa   Zama yayi bayan ya idda nafila ta karshe raka'ah biyu bayan azahar..nan ya soma kawo maganganun ammyn a ransa yana juyawa
Aciki Wanda yafi daure masa kai ma auren nan data ce yayi kuma da jasmine .hmm kaiwa nan ya dakata
   Da sauri yayi kokarin kauce tunanin aransa ya cigaba da neman yardan ubangijin sa akan al'amarin rayuwar su baki daya,

    Bayan kamar minti 10 ya mike ya nifi hanyar asibiti, tun kafin ya isa ward din sai ya kasance
Haka kawai ya tsinci kansa da maimaita kalmar ""La hawla wa la kuwwata illah -billahi,,hasbiyanallh wa neemal wakeel........
don kanshi tuni yake Hargowa ciwo kamar zai fashe idonsa har yanzu basu dawo normal ba
A yanayin daya ke ciki Shikan sa baisan sau nawa ya fade su ba har yayi sallama cikin Dakin da suke

Sosai zuciyan sa ke harbawa kamar zai fita ganin ta a kwance hakan  wani sanyi take gabobin jikin sa sukayi lokaci guda yana maida dukkan hankalin sa kan ta yana tahowa a hankali

    Jasmine kuwa Kallo daya tak ta masa ta dauke kanta zuciyan ta cike da dawainiyar tunanin yadda zai kasance mijin ta nan da sati guda

   Mamy, bacci take yi ne? Ya tambayi hjy hadiza dake gefen jasmine din tana dan lazimi a asirce ita ma

Eh ena ganin hutuwa takeyi'' amma yanzu likita yace zasu zo duba ta suka progress din ta,

  Ai kuwa suna cikin magana ya ke hango likitan ta glass adayan sashin dakin tana zare igiyoyin computer da,, wani irin remorseful look kan fuskan ta,
   Wani irin sara kansa ya sake yi take ya ji jijiyon jikinsa suna kyarma ya soma tafiya a sanyaye gaban ammy kamr wanda baijin komai awajen

Suma tsaye sukayi suna binsa da ido ba wanda ya motsa. ...sai yanzu abun ya zo musu
Gam ya rife idon sa bayan kallon tsawon mintuna 5 daya ma gawar ammy..nan take wasu zafafar hawaye suka sauko masa " ya rusuna daf ya mata addu'oi irin na mamata ,a dabaran ce yadda ba wanda ya ke ganin halin da yake ciki awajen
Sam ya danne zuciyar sa ya ki bari kuka ta kufce masa akan gawar ta
Amma muryansa na matukar karkrwa har ya kammala adduar sa..
  Yana gamawa ya juya ya dubi gabar ya tada kabbara yayi sallah raka'ah biyu,
Ya gode ma Allah ,zuciyansa cike da tawakkali da neman hakuri daga ubangijin sa
Jasmine bari take yi a tsaye idon tabya fiifito magana ya kafe ..haka ma hjya hadiza takasa control sai  innalillhi wa enna ilaihi rajiun take maimaitawa
Kafin ya idar likita ce ta shigo a sanyaye don itama ta san wacece ammy run bayau ba .

  Hakuri doc ta basu sosai sannan ta dada sanar da su ammy ta cika,

     Luiiii jasmine tayi zata kai kasa,
Amma suka riko ta,idon ta dishi dishi nan take jikin ta ya mutu, sai zazzAbi daya rufe ta nan take
' Tangal tangal ta somayi har ta isa gaban gawar ammyn tana mata wani irin kallon ena ma ace mafarki ne in tashi
  Sannan ta kamo hannun ta Gam gam ta rike ta tana bin ta da wani irin kallon razana
Nan ta kife ta soma wani irin kukan zuci......tamkar bata hankalin ta

Ashween ko Dan siririn   Hawaysn sa ya goge ya tashi tsaye ,don bakin sa ya dauke magana tamkar kurma haka ya dawo lokacin
Da kansa ya tashi ya riko jasmine din
Da ta soma fizga tana kwacewa a hannun sa "tana kuka""  ammy kimin magana mana
Please ammy,kar ki tafi ki barni take cewa cikin kuka amma sam bata cikin senses dinta..maimakon abun ya sassauta sai dada hawa take tana maganganu kamar zararriya
Shima dai ya rike ta ne kawai amma shi kadai  yasan meya keji aransa
Da kyar ya daure yace jasmine!!!!!!! da dan karfi"
Nan ta dago ta kalle sa a daburce,,sai charaf suka hada ido da sauri ta fada kirjin sa ta sake wani irin razannan kuka"tare da kankame sa...tana kiran ammy

  Hjiya hadiza ma da kyr ta fice ta isar ma mijin ta sako don a yi a kaita makwancin ta
ita gani take a halin da ake ciki ashween bazai samu gwarin gwuiwar yin komai ba tukkunna,

Dam suka rike juna kamar zasu shige cikin jikin junan su alokacin kowa da abunda yake ji na zafin rashi....a hankali yake rarrashin ta yana dan bubbuga mata baya don ta sassauta kukan nata,
Shikam tuni idon sa Suka Vushe ya makance ce baya so ma ya  sake kallon ammyn
Don ya tabbata komai nashi dai motsi kawai yake amma na karfin hali
....
Jasmine dake hannun sa tayi lumui tana sheshheka Haka har ya mika ta ma mamy dake kokarin shigowa da mijin ta da abokin sa da ashraf .., amma ashween haka ya daure ya danne zuciyan sa  kamr da wasa  yaje akayi niyya aka kammla komai yadda ya kamata
Sannan suka kai ammyn makabarta ...
Nan ma Still hawaye bai sauko masa ba saida ya  sa ta cikin rami da hannun sa
Nan ya ji gaba daya duniya ta juya masa baya, zuciyar sa ce ta soma ce wa
' Yah Allah kai kadai ka rage min yanzu banda kowa' ena rokon ka.. ka mata rahma ka kyutata makwancin ta fiye da yadda ta kyutata rayuwa Ta'
Na rasa uwa,uba da yar uwa da farinciki na gaba daya yau, Allah kai kasan dai dai,kasa chan ya fi mata nan..kaji kanta ya rahmanu
Sannan ya karashe da wasu adduoin..ya share hawayen sa .

Jasmine kam zazzabi ma ya hanata jin hayaniyar masu zuwa gaisuwa tun daga ranar farko
ashwenn bai bari ta sake fitowa ba don bata dawo ba...
Haka ma Kwata kwata  ya raba ta da dakin ta ya kaita wajen sa inda ba mai shiga
don mutane suna mata magana saita firgice ta soma maganganu alaman bata cikin senses dinta har yanzu

Haka suka cigaba da zaman makoki abu kamr wasa
Bayan kwana uku kamal  yayi shirin komawa shima bayan kammala sadakan uku...

Tare suka jera ba wanda yace uffan har saida ya kaisa bakin motar sa
Kallon da kamal ke masa ya sa shi
   Da kyr ya kwakwulo murmushi yace
" saura inkaje kar ka isar ma amarya sako na,im so grateful naga kokarin salma data zo cikin danyen amarci" gashi bamu samu daman halartan biki ba ya karashe da dan fuskan damuwa

Dan karamin scuf kaml yayi don har cikin ransa ya san ashween daurewa kawai yake yana magana
Sosai damuwa ya bayyana a jikin sa da fuskan sa don har yayi fayau kamar mace mai sabon shigan ciki

Yace Kar kadamu ash,bakomai wallhy salman ma ta fahimci hakan "
Dama kuma kaga auren one time ne ba abunda akayi ,abun tsakanin family ne kawai kwana biyu duka duka aka dauka aka kammala
Gashi bata samu ta gana da kawartan ba ma,
Ya jasmine din take yanzu?

Tare da sauke ajiyan zuciya yace " alhmdullhi,
Nasa ta taci wani abu yau dai ..she will be fine
Ya fada cikin sigar tausayi
    Dan dafa kafadar sa kamal yayi
Yace " nasan zaka iya ash, ka kula da kanka da yar 'uwar ka.
Shes all yhu got now
Dan gyada kai yayi yace hakane kamal..na gode
Nan har sukayi sallama
Ya juyo ya nufo cikin gida

    Site din da su haj hadiza suke ya je ya dan leka su enda take sanar masa da yanzun ta baro jasmine din sai amai take amma da jikin da sauki..

    Ba jira shima ya mike ya nifi site din san kwance ya tarar da ita ta rungume hoton ta ita da ammy tayi luf da ido kamar mai bacci....



😔🤝🏼

*surriem*

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now