*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*hey Fans, ku saurare taskar brilliant Writers domin jin wani sabon salon fadakarwa da zata bullo da shi mai taken GUGUWAR ZAMANI/*
*if i where u i wont miss it. together we shall make a change, remember u have the power to change the world,bcos change begins from witthin ur hrt,take control . BWAloves u**Page▶80*
Washe gari jasmine da kuzarin ta ta tashi taje ta gaishe da mamy tare da mata bayanin bata samu littafin bane shiyasa ta tsaya bin kasuwa kasuwa har tayi dare.
Mamy tace babu komai jasmine,nasan ai haka kawai bazaki zauna ba
Tashi kije ki huta.Jasmine ta mike tare da cewa mamy nima ena so ena taya mai girki wasu abubuwan,pls may i?
Cikin jin dadi Mamy ta dago ta kalle ta tace why not,kiyi abun ki, ure free d
Dama Naga wai kar na takura ki ne ga karatu shiyasa bana ce miki ki dinga fitowa ai ko hira kyayi ..Tayi murmushi tace, haka ne,
mamy tace to Allah ya miki albarka
Jasmine tayi murmushi ta fita.Mamy a ranta tana murnan jasmine ta fara mancewa da damuwar ta tana so ta sake jikin ta cikin jama'a
A gefe kuma jasmine na kan kokarin share ma kanta hanya ne in da zata samu sakin layi tana fita wajen mijin ta cikin sauki.
Cikin satin gaba daya ta sauya ta zama very active hankalin mamy ya dada kwantawa sosai
Bangaren ash kuwa ya ta kura ta zo cikin satin amma sai ta shaida masa mamy zata je hidiman programe din USAID da aka shirya don bada taimakon gidan sauro ma mata masu ciki.
Don haka itama ranar zata samu daman fitowa ta jima.Duk bayan dogon phone call din da sukayi bayan Sallahr asubhi sai ya bata hakuri yana cewa shine silar jefa su cikin wannan halin
Tun tana rarashin sa har ta zo ta daina ta kyale sa.Ranar alhamis eta ta karbe girkin gidan baki daya , cikin fara'a da sakin fuska,
Gashi kwana biyun da take malangarin a tsakar gidan ya sa ashraf shiga wani mummunan hali game da abunda yake ji a ransa akanta
Bayan ta kammala tsaf sai ta ce mamy, dama ena so ne naje na sake duba littafin ne ko zan ci saa'Mamy ba tayi wani dogon musu ba tace, ba komai kije,nima goben ba na kusa in dai akwai wani matsala sai ki kira ni..
Tace tohm zuciyan ta cike da farin ciki ta tashi ta tafi
Sosai abun ke burge mamy, sai ta soma tunanin ya kamata kwanan nan ta kawo karshen matasalan su.
Da safe ba suyi waya ba amma tun 11am ta kammala shirin ta cikin riga da skirt dark blue wanda yaji kwalliya ya mata kyau sosai,
Ita kanta saida tayi admiring kwalliyar nata ,ga qamshi dake tashi jikin ta sai murmushi take tana karanta sakon sa wanda ya shigo instantly yace yana gida yana jiran ta".
Daga windown ta hango Ashraf ne ke gaban mota da Su mamy,
Ai suna fita
Ita ma ta fito yau ko mota bata dauka ba don tsaban sauri ta kama hanya abunta.Sanye da red longsleeve shirt yake ya dan jin gina kai shiru fuskan sa sai haskawa take lips dinsa har na wani pinkish and oily, ya zuba kasallen ruwan idon sa ma flower vase dake gefe.

ESTÁS LEYENDO
SO MAKAMIN CUTA
Ficción GeneralIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez