*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶79*
Bayan kwana biyun ashween har airpot ya raka zahida..
daga nan shima ya bar garin abuja ya shigaba da harkokin sa har kusan 2 months bai leko ba Har Sai dai ya tabbata ya dan sassauta makan sa yawan tashin hankalin da yake shiga akan tunanin jasmine, kafin sai ya sa ranar zuwa abujan.Kafin nan rayuwa yanzu ta kasance ma jasmine kullum tana kullawa tana warwarewa ita kadai
Don Cikin watannin sosai ta kuma haskawa ,tayi kyau ta yi fresh tasha gyara kam barakallh,sai ramar da ta dan yi ya dada fidda shape din hips da boobs dinta suka bada shape mai mugun kyau ma jikin ta bisa kan tsari.
Ko ashraf ma saida maitan sa yayi mummann tashi amma jasmine ta sauya hali na kamar da chan ba,
Dan Yanzu da kyar abu ke bata mata rai bare tayi hawaye.Ashraf Tun yana ganin zata biye masa har dizgin da ta ke masa ya sa ya hakura Ya shareta shima
Cikin kwanakin Da tunanin ash ya ishe ta sai ta soma fita da kanta tana neman sa a gurare daban daban ko zasu hadu wata rana amma babu shi ba mai kaman sa,
Tasha zuwa gidan ammy amma ko ena a kulle ne gashi in banda spare key din dakin ta babu wani abu kuma a hannun ta.
Gashi salma ma ba ta kulata ba,
Ta samu dai sun yi magana ta tex a cikin watanni biyun don sau biyu ta amsa mata sakon ta daganan har yau kuma basuyi waya ba.Duk ta damu musamman da tayi ta duban hanya ko zata ga ashween din ya sake zuwa amma shiru.
Taje ukraine ma har sau biyu makaranta nan ma tayi tsammanin ko zai biyo ta amma shiruTun tana danne abun har ya soma bata haushi,ga shi kullum ta tuno zahida kishi sai yayi kamar zai kashe ta ,sosai tayi fushi da shi duk dama bata san takamammen me zatace ya mata na laifi ba.
A cikin detention office kuwa mrs rod ta gama hayagagan haukar ta..
Tace sam makiyan ta ne suka hada ta da yaran ta.Mrs rod Ta shiga wani mummunan hali a zuciyan ta na musamman ba don ma kudin ba kadai
,rasa yayan cikin ta ma yayi mugun taba zuciyan ta,
Tace tasan dai zahida bata da wayo ba zata taba iya tona mata asiiri haka kawai ba sai dai in zuga ta akayi.
To waye? Kullum sai tayi ma kanta wannan tambayaGashi cikin wata biyun gaba daya media sunyi facali da ragowar mutuncin ta a waje,
Dama bata da komai cikin kaso don haka wani karamin flat din ta ne ke jiran ta da motar guda daya tall ,Bata damu da wannan ba saboda akwai kudin rodriquez wanda ta sace a bank achan switzland.
Amma tasan inta kuskura ta taba za a iya sake karbewa a danka ma yayan ta.Yanzun dai ta qudiri niyyar muddin ta fito sai ta nemi munafikin daya hada ta da familyn ta ya tarwatsa mata rayuwa.
tace kisa Kawai ta yanke a ranta zata yi ma duk wanda yake da hannu a cikin tonawar asirin ta
Tun Ranar jumu'ah ashween ya shigo abuja,.
Da shike salma tana cikin watan ta na bakwai har a ana neman shiga na takwas
Wajen su ya wuni ,suna ta shagalin shirye shiryen sabon babyn da salma zata haifa nan ba da dadewa ba,Gaba daya in ashween yana wani abun sai salma tana tuno da abunda ya faru,domin kuwa har yau tana jin haushin rasa na shi babyn da yayi...
Ba yadda kamal baiyi da ita ta kira jasmine ba amma ita ma taki sam ,tace bata jin yin hakan ne duk da ma she is no longer holding her,
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez