20

2.2K 281 0
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

  Jinjina gare ku yan *brilliants groups da brilliant writers*  musamman *jameela musa* Allah ya dada baki hakurin zama da mu baki daya ameen,

wai ance Shimfidar fuska yafi shimfidar ta barma
*Nasmat yar mutan arkillah* na ji karamcin ki kuma na gode..💋💯🤝🏼



*Page▶20*


A sanyaye ya zauna gefen ta amma sam taki motsawa bare ta bude idon ta
Shima kallon ta ya cigaba da yi gaba daya kamar ba ita ba
Sosai ta zube cikin kwana ukun nan kamr wanda tayi ciwo

  Jasmine ya jikin? Ko zamu je asibiti ne yace yana dan dafa ta kadan,

    Shiru ne ya ratsa wajen da taso tayi pretending kamr tana baccin karya bata ji
Ko tunanin me tayi oho
Kawai sai ta bude ido
Duk da taci karo da nashi bata iya janye wa ba saboda nan ne ta soma karantar halin da shima yake ciki a lokacin

  Wasu zafafan hawaye ne suka biyo bayan kuncin ta,batace komai ba don sosai ya bata tausayi 'nan ta soma tunanin ena ma ace zata iya kula da shi kamar yadda yake dawainiya da ita?
Amma sai dai  tasan abune mai wuya don har yanzu gani take tamkar ammy zata dawo ace mata komai ma mafarki ne

Shikuwa tausayin ta ya sa take ya sa hannu ya jawo ta jikin sa dukan su suna famar sauke numfashi a hankali
Lafar da kanta tayi akan kafadar sa yana dan bubbuga mata bayan ta a  hankali...baice komai ba
Cahn cikin makoshi tace
Yaya, shikenan ammy na bazata dawo ba ko????

Still Bai amsa ta ba Cikin sheshheka ta cigaba
  Kullum en na kwanta bacci ena kallon ta kusa dani
Amma meyasa ammy ta tafi ta barni"?
Sai tafashe da kuka

Lumshe idon sa yayi ,yana kokarin cize hawayen sa da suke hargowan fitowa
Don sosai yake jin zafin kukan nata da abunda take fada 
son ta da tausayin ta gaba daya suka taru suka masa sarka lokaci guda

Cikin azama ya dago ta yana facing dinta ,itako sai kukan ta take abun ta, ya tausar da muryan sa yace ya isa haka jasmine
Am here, Kiyi hakuri kinji ? Addua ya kamata kina mata ba kuka ba,ki tuna fa ba wani son da zamu nuna mata yanzu inba adduan ba' ki daure ok? Ai enson ran mu ne har abada ammy bazata tafi ta barmu ba ko?

Ta gyada kai gwanin tausayi  alaman ta gamsu..nan ta soma goge fuskan ta
Shima ya sa hannnu ya shiga taya ta goge hawayen nata
Yana cewa kinga salma ma tazo har ta tafi baki ganta ba,
U need to get well"ai ko ameen kike ce wa mutane  ammy zata ji dadi achan itama ko

Nan ma gyada  kai tayi,murya dishi dishi tace naji yayah zan na mata nima enaso ammy taji dadi...tace a shagwabe duk dama batasan tayi hakan ba

for d first time ya kwakwulo murmushi yace Alhmdullhi,
Zauna nan ena zuwa bai jira tace wani abu ba ya mike yayi waje.

Sauke ajiyan zuciya tayi ta koma ta kwanta kan sofar da ke dakin nasa
Wani sanyi taji kadan a ranta
lokaci guda taji an rage mata wani nauyin dake kan kirjin ta"nan ta kafe tana dan addu oi kadan kadan  tsawon minti 15
sai dai duk lokacin da ta rufe ido fuskan ashween ke mata gizo

  Cikin wannan yanayin aka turo kofar
Kamar bashi ba ne ya fice dazun haka take kallon sa
   Har ya ajiye faranti mai dauke da plates har guda biyu da glass cup anrufe sa kirif da plain cover dai dai bakin sa ..
   Sai yanzu ta lura da yanayin shi itama kallo daya zaka masa kaga rashin kwanciyar hankali tattare da shi..ya zube ba laifi
Ita kanta tasan dauriya yake don taga yadda ya birkice ranar da ammyn bata da lpya"
ko da ba a fada ba ita tasan rashin ammy yafi masa zafi fiye da ita,

A Gaban ta ya ajiye farantin ya ja gefe sannan yace
"please ki daure kici abinci, sai ta tsura masa ido tayi shiru don har cikin ranta
Tana so tace masa ya zauna suci tare amma ta kasa sa maganar a harshen ta

Ganin bata da niyyar amsa shi yace ""ena zuwa, tare da yunkurin ficewa don ya bata waje ko zata ci ita kadai

  Ita kanta bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba wanda ya sashi kallon ta ba shiri
"
Ya salam ,zuciyar sa ta ambata ya tsugana gabanta
Lpya kuwa Jasmine? ko abincin bai miki bane na canza..
Shiru tayi amma sai ta rage sautin kukan kamar munafuka taki bari ta dago ta kalle shi

Gashi ganin yadda ya tsara fried noodles din ya bata sha'awa sosai
Shima bai sake magana ba saida ya mike tsaye " toh shikenan bari na aiko talatu sai ki gaya mara abunda kike so
Take ya ji saukar lallausan hannun ta akan nasa,. A marairaice take cewa
Dan Allah kar ka tafi yaya,zanci....

Fuska ba yabo ba fallasa   ya dawo ya zauna gefe ba musu yace to bismillihh ,

Amma Taurin kai ya sa ta sakeyin zugum a gaban abincin burin ta kawai yasa hannu suci tare

amma  tayar da  zata fahimtar da shi ne ke damun ta Nan ta cigaba da ya mutsa fuska..

shi kuma yana gefen ta yana  hankare da  duk wani yanayin ta bata sani ba
  amma sai ya ja bakin shi yayi shiru ya zuba mata ido..




Uhum🙌🏾

*wallhy ena mugun godiya  masu comment da followers jazhak Allahu khairan ahsani ,kuma jazhakumullahu fil jannatil firdaus..ena son ku duka*❤💋💯🤝🏼




*surriem*

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now