*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*NI Dai a bar taheerr yaci uban sa, besty ba wani tausayi abunda ka shuka ....tam😪😪*
*Godiya marar adadi for all those surayyahms LOVERS da nake gani in many groups witout even thy knowledge ,those that choose me personally and think am a perfectly writing model ...may Allah love u the way u love me ameen.🌹*
*and Am gratefl to everyone that dosnt even know me but yet believe in me.ilsmuch🌹*
*Page▶78*
Bayan mutuwar mr fadhul a Nan lagos Ashween ya zauna yayi duk abunda ya kamata akan bison mr fahdul shi da aminin sa kamal,
Bai bar victoria island ba sai da akayi sadaqan uku,
Kafin nan an mallaka masa duk wasu takardu,IDs,da duk wani abunda ya shafi mr fahdul.Nan ya kama hanyar abuja a zuciyan sa ba abunda yake kawowa kamar da ace a hannun sa jasmine take da sai yayi kokari ya kawo ta taga mahaifin ta ido da ido, ko da kuwa gawar san ne..
Gefen su zahida kuwa yanzu aka soma rayuwa, tuni ta soma jambade akan arzijin mahaifiyar ta ta tana shirin kafa kanta ,..
Sai dai sun rike amanan juna sosai da su jabir da jamal, duk da basu tare yanzu kowa yayi alkawarin ba zasu taba rabuwa ba ko don mahaifin su.
Cikin kwana ukun Zahida Ita kadai ce yanzu a mansion din rodriguez ,
gaba daya duniyar ta samu a tafin hannun ta, ita take mulki sai abunda ta ce ,a fuskan ta akwai annurin cikan buri da sanyin zuciya.
Amma sam cikin zuciya ba haka yake ba,Tun da tayi juyi taga ita kadaice ga kuma dumbin arziki da mulki sai take jin rashin kwanciyar hankali,
she knew deep within her heart she is not happy, sai tana jin ta very lonely and left alone.Hakan ya sa ta ke yawan zama shiru ta rasa meke mata ciwo.
A gidan mamy kuma ,Ganin jasmine din ta warke yasa Hajya hadizan kaita gidan wasu matan larabawan sudan masu gyara irin na amare,
tunanin ta tunda akan kishiya zata zauna tana so amata gyaran da karya wani namiji ya ce zai raina ta.Jasmine bata san duk wannan shirin na miye bane ita dai ta kwantar da hankalin ta ne don abun yanzu yafi karfin ta.
Yau aka soma auna ta wajen gyaran sai mamy tace musu a gida za'a na mata saboda har yanzu da aure akanta ba zaiyu tana fita ba.
Nan aka gama biyan su a kayi komai akan in suka shirya zasu soma aikin su.
Abban ashraf ne ke jan motar sai hj hadiza da jasmine a baya...
Dai dai wannan lokaci ashween ya dosu kwanan anguwar su mamy.
Duk hankalin su baya wajen amma ita kam tuni ta sa ido tana leken sa kamar ta hadiye ranta don murnan ganin sa..
Ganin ta sakankan ce ta juya baki daya,ya sa mamy tace jasmine? Me haka ne, yau kuma wani sabon salon zama ne kika samu
A razane ta dan ja jikin ta sai ta kasa amsa wa tana mutsu mutsu,
Abban ashraf na shiru sabida shima ya gansa ta madubin motar sa,amma sai ya kau da kai.
Suna kaiwa bakin kofar gate a lokacin ash ya dan iso daf ,nan ne itama ta gan sa
Sai ta dafe kai tace tsaya nan abban ashraf kar ka shiga gida dan Allah,
Ba musu ya ja suka yi parking
Kowa ya fito ..Ashween ya tsuguna a al ladabce ya gaishe da Abban ashraf
Wanda ya amsa masa cike da girmamawa da tausayi
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez