*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶86*
Suna isa gida mamy tayi cirko cirko a falo tana jiran shigowar su abban ashrf da jasmine
Shikuwa da suka shigo agaba yasa ta yace maza ta wuce site din sa yana kallo har ta lume ba wanda ya isa ya mata magana.
Ranar rayin mamy ya baci don sosai don taso ayira wuta wuta ne komai ya wuce mata.
Jasmine Gaba daya ranar a site din abban ashraf din ta zauna tsaban tsoro yadda mamy ta birkice ta kasa zama waje daya a gidan ita kawai a fada mata waye uban cikin dake jikin jasmine
Anan ma Ta hana ashraf sakat ta sashi a gaba da bala'i ta daga masa hankali sosai sai da ranshi ya baci har sai da yayi mata kuka kafin ta hakura ta kyale sa
Haka Abba kuwa ya tirje yace sam ba wanda ya isa ya taba jasmine har sai hankalin ta ya kwanta ayi maganan cewar sa kar aje a taba masa jika.
Wannan magana ya matukar bata ma mamy rai musamman da ta fahimci abban ashraf ko ajikin sa bai damu ba..
Shi dai sau daya ya tambaye jasmine din yace mata cikin na waye ne?
Bata ji kunya ba tayi masa bayanin komai sannan tace masa abba wallhy cikin na yaya ne ...
Yace Alhmdullh ,to gobe idan aka tashi magana bana so kiji tsoro ki fada mata komai kinga sai kowa ya huta ko?Jasmine tace toh,anan tayi zamanta sai chan 10.30 na dare ya sata a gaba yace taje ta kwanta a dakin ta.
sannan yayi kashedin kar yaji wani ya daga ta sai da safe za suyi maganan.
Jasmine kam tun a asibiti data ji maganan a bakin mamy ta gode ma Allah yafi abun a kirga a zuciyan ta .Yanzun ma Ta so ace ta gaya ma ashween halin da take ciki amma sai ta nemi layin sa iya nema amma shiru baya tafiya
Cikin daren tayi nafila ta dada nuna godiya ma ubangiji tare da dada nuna masa nadamar ta na kuskuren data tafka da kyautar da ya bata na farko
Tsaban murna hannun ta akan cikin tana shafawa ciikin tunanin mijin ta har bacci ya dauke ta.
Tun safiyan Allah mamy ta zo ta turje a bisa dikkan alamu kamar ko bacci batayi ba,
Ita dai duk damuwar ta yau ita mai zata fada ma Ashween game da cikin?Abban ashraf haka yaki cewa komai ya ringa waina ta har saida aka ci karfe 10 na safe kafin yace ayo zaman..
Jasmine sanye da doguwar riga ta shigo falon abba sai ta zauna a a kasa daf da shi ta sunkuyar da kai kasa.
Mamy sam ta kasa hakuri tace ehem ena jinki ?
Nace Daga ena kika samo juna biyu jasmineJas tayi shiru tana tunanin yadda zatayi bayanin satan hanya ta keyi tana fita har aka samu
Sai mamy tace magana fa nake miki ko sai na tashi na miki dukan tsiya zaKi gaya min?
Sai ta soma kuka a hankali, tace kiyi hakuri mamy dan Allah kiyi hakuri
Mamyn ta tashi ta tsaya a tsaye idon ta har sun kawo ruwa don firgici tace ki kace nayi hakuri?ni ban san shi ba, Bayani kawai zaki min uban wa ya miki ciki agidan nan.
Cikin kuka Jasmine tace zan fada mamy amma kiyi hakuri dan Allah
Tace ni baruwa kawai kiyi magana ena jin ki, nan jasmine ta daure ta tsayar da hawayen ta amma sai ta sunkuyar da kai kasa tace mamy cikin nan na yaya ne don ni bantaba fita da kowa ba sai shi..daga nan tayi shiru
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez