15

3K 241 1
                                        

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

I just published "part1page16" of my story "SO MAKAMIN CUTA". https://my.w.tt/oQgZpZyw6N



*Page▶15*




Zaman su ke da Wuya
Hajiya hadiza tace ena sauraron ki ,
   Wani dogon numfashi ta ja sannan tace
   A Shekaru 18 da suka wuce, anyi wani hamshakiyar mata da mijin ta ....nan labari ya soma...

"Daga nesa ake hango bishiyoyi a jere tsaf cikin layi gwanin sha'awa Waje yayi luf luf,ga sanyi mai niima na ratsa ko ena,
Akasarin mutane 40 ke faman aikin su bisa tsari a wani makeken gonan yayan tufah na zamani  wato hydbrid plantation
 
Duk da komin wajen dai dai yake amma hakan bai hana ma'aikatan nan cigaba da kimtse kimtse da gyare gyare ba

   Wayyo Allah na"asabe daya daga cikin ma'aikatan tafada tana rike kugun ta dayan hannun ta durkushe akan gwiwar ta
Gashi Sai diga take da zufa..

Subhanallhi" as..a..be
Meya faru kuma ?
Dan Allah ki mike kinji asabe saura kiris madam rod ta karaso..cewar wani dattijo daya zo kanta mai suna mlm habu

Malm habu cikin yanayin damuwa yatallafo ta yana cewa
  Sannu  asabe  .ki daure

Haka ma Yawancin sauran maikatan ke fada
Asabe  Nishi take fitarwa kadan kadam
Sannan ta tsaya ta cize bakin ta don radadi azabar data keji a cikin ta amma sai ta cigaba da aikin

   Faruwar haka da mintuna 5 motocin alfarma kirar prado formated na suka soma tururuwar shigowa wajen
  Kuuuuuuu cikin kowa ya soma wasu a bayyane wasu a asirce
"" Gata nan...Sun iso fa ku gyara
Babbban cikin su yake rada musu a hankali yayinda kowa yayi tsuru tsuru bisa layi na kallon yadda ake jera parking ana saukowa

Turawa ne guda uku tare da hajiya hidayat rodriquez mai dauke da juna biyu kimanin wata takwas
Sai karamr yar mijin ta ZAHIDAH wato yar marigayiya first wife na alhji abdul fatah rodriquez

  Gefe kuma Sai jamal da jabir da wata baturiya wacce uniform din jikin ta ya bayyana matsayin ta na nanny mai kula da su ..
Masha Allah"tubarkallah
Daga hajiya hidayat har yayan cikin ta wato jamal da jabir kyawawa ne  farare tas kamar an zana su da hannu
kyawun su irin na bugawa a jarida

sai dai duk da hakan zahida ta so da tsere musu 'karama ce kimanin shekara 10 amma  sosai body structurn ta yake dauke hankali
yar das das ce kamar model ga suma kamar balarabiya,
tana makale a hannun alhj abdl fatah cikin customised gown dinta sai rigima take tana yauki
Don a duniya bata jin ita ba sarauniyar kyawu bane
Sosai take mugun ji da halittar ta bugu da kari da matsayin ta wajen mahaifin ta na yar sa ta fari.

Atakaice yaran rodeiquez Dukan su abun kallo ne gwanin sha'awa suna tahowa cikin shigar su na Qasaita da kwarjini

Jamal? Hjy hidayat Tace cikin muryan ta daya yi kama da na turawa
'Kuje wajen dad dinku let me show dem around' bata jira ya amsa ba ta juya tabi bayan turawan nan
   Nan ta soma bin lungu da sako na gonar tana musu bayani cikin harshen turanci
Sai dai zuwan su wajen ko amsa gaisuwar ma'iakatan ta batayi ba bare ta musu kallon arziki

  Daga chn gefe su zahida da kannen ta suke hira " oh my' ta yamutsa fuska sosai tana cewa
Jamal,dubi waccan mummunar matar wai ahaka suke aiki anan din? Cewar zahida

'hhhh c'mon  sis meya hada muni da aikin gona kuma yace yana bin asabe da kallo da bata ma san sunayi ba
Cikin yatsine ta dubi jamal din tace
Kalan ta sa fruits din ma suki fitowa da kywu suyi muni ka duba dai kagani shes so ugly ..tafada a wulaknce tana tuf da yawu
Kasan me?
In nice eta bazan taba nuna wannan fuskatan awaje ba ..kai munin yayi yawa.

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now