*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶22*
Hakan rayuwar su ya kasance a gidan
Yau ana saura kwana biyu kacal da cika sati da rasuwar ammyHjy hadiza da har yanzu bawai jimamin mutuwar ammyn ya sake ta bane amma hakan ta daure ta soma shirye shiryen auren jasmine da ashween kamr yadda ammy ta bukata
Bangaren Ashraf kuwa ba yadda baiyi ba don yaji shirin meye mamyn shi keyi amma sam taki gaya masa komai
gashi ya jira jin amsar jasmine har ya gaji ya zuba mata ido, don shi mutuwar ba wai ya damesa chan chan bane.Toh amma ba yadda ya iya a dole Mutuwar ammyn ya sa shi dakatawa da maganar don yasan yanzu jasmine bata hankalin ta sosai ,
tunanin sa tunda yanzu ba wanda zai tsawatar masa mutuwar ammyn ai tamkar an share masa hanyar saukin samun nasarar auren ta neDuk lokacin da ya tuno ashween kuma gani yake kamar bai isa ya hana shi jasmine ba
don karara yake nuna gabar sa a fili da shi.Gefen Ashween kuwa yana iyakan bakin kokarin sa wajen kula da jasmine duk da cewa kullum sai tayi kokarin ballo maganan bata son auren nasu, a duk lokacin data fada hakan kuwa shima sai ya nanata mata itama cewa akwai wacce yake so kuma ba ita ba ce.
Duk da Abun na matukar damun sa don iya sanin sa jasmine dinsa shi kadai take so to meya faru?
Yana cikin wannan halin wayar sa ta buga kara ganin kamal ne ya sa
Bai bata lokaci ba ya dauka
bayan sun Gama gaisuwar su
Ya tambayesa salma,don yanaji jasmine din ke complain rashin samun layin ta kwata kwataNa kamal yace ' wallhy akasi aka samu amma zansa ta neme ta kafin nazo,
Mekake nufi kafin kazo ita bazata zo bikin kawar tan bane?Uhumm mubar wannan maganan tukun,, zahida fa zata kashe min aure jiyan nan da kyar na kalmaso salma"duk ta bi ta isheni da kira wai layukan ka basu shiga in kaji ta tamkar zata tashi sama.
Dan Karamin tsuka yaja sannan yace
Ai nafada mata bana bukatar disturbance bata ji ne kawai,
Kuma kaga bana son tasan ammy ta rasu before she starts thinking odawise..don wallhy yanzu yadda nakejin kaina zan iya mata illah.Ohh my god ash, Hakane nasan baka bukatar ganin ta ,toh amma
Tace min dai nan da kwana uku zata dawo nigeria kuma zata shigo yola
ranar jummu'ah nan agidan ka zata sauka kamar yadda ta sabaCikin halin ko enkula yace ""Kyaleta tazo mana ,ai ena dai dai da ita
Nan suka dan taba hirar su kafin ya tashi ya nufi dakin sa,
Ko minti biyar baiyi ba yaji turowar kofa dakin sa a hankali tare da sallama,jasmine ne a tsaye
A ladabce ta gaishe sa,sai kallonta yake don kuwa hijabin data sa bakaramin kyu ya mata ba,
Light make up ta danyi wanda ya sa ta dada fresh,tayi so cute and innocentDan lokaci ya dau yana starring akanta Chan ya ce, ena fata lpya dai ko?ko kina bukatar wani abu ne.
Tace, Dama mamy ne ta aiko da driver ni zan wuce
Wani garas yaji maganan a kunnen sa don har wani ciwon kai ne ya soma masa a take,
Uhum, toh Allah ya kiyaye inkinje ki gaishe ta..taKe care
Ya fada ba yabo ba fallasa
Dan karamin murmushi ta mayar masa tace toh yaya,sannan ta juya ta fice ,Saukar ta kawai ya keji daga steps amma sai yaji kamr ya rugo da gudu ya bi bayanta su tafi tare
tunanin sa kawai kar ashraf yace zai kula masa ita a bayan idon sa,
Tuni ya zaga jikin windown ya cigaba da kallon ta
daga sama yana gani har ta lume cikin motar suka bar gidan
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez