25

2.5K 227 1
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Masu comments da masu neman cigaba wannan shafin naku ne*



*Page▶25*

Kallo daya tayi gabanta a  razane ta Fada jikin mamy ta kankame ta tana kuka,

Ashraf Shikam tuni yasan nashi ta kare don ga mayafin ta dumu dumu a hannun sa inda ya rike yana yunkurin biyo ta

Mamy na tsaye tana aika masa mugayen kallo Kamar zuciyan ta zai fashe haka take ji

Me kake yi haka? Meya kawo ka nan ashraf... Cewar ta a tsawace
E' e na ua somayi ya rasa me zai ce""
Itako mamy na rike da jasmine sai dada kulewa take

bazaka fada min ba ? Ta sake daka wani tsawan

Nan ya soma juyi da kai yana kukkuni maganan ma ciki ciki alaman shi fa ancuce shi ya zo ya dauki fansa

a lokacin wani guguwar bacin rai ne ya rufe mata ido
Ba zata ta ture jasmine gefe ta nufi kansa ta dinga kwalla masa mari ita kanta batasan sau nawa ta masa ba sai da ya rusuna kasa ya zuba gwuwar sa

cikin tsawa tace bazan maka baki ba ashraf amma kaje,
Duk wanda yayi nagari don kansa,

Sum sum ya mike ta galla masa harara cikin dacin rai tace
Wawa mara hankali ,mani zaka tonawa asiri?toh ta Allah ba taka ba.FITAAAA ta dada mai nuni da kofa

A hakan ma bata bari ya karasa ficewa ba ta bangaje sa ta janyo hannun jasmine din ciki
Duk tausayin ta sai ya kamata sosai
Gashi sai bari take don tsoro
'mamy rarrashin ta ta shigayi a hankali
cikin ranta tace " yanzu yarinyar nan zatace da ammyn ta tana nan bazata fuskanci wannan wulakancin ba "

A hakan take kan bata baki har jasmine ta soma sasaauta kukan nata har tayi shiru

Nan ta sanAr mata ashween ya riga ya iso yanzu zasu tafi jirgin su ya shirya
Wani gum taji a kunnen ta
Murya a dishe Tace Muje ena mamy?
Ba a gidan ammy zamu zauna ba ?

Gyada kai mamy tayi ta riko hannun ta tace
Kema kikace gidan ammy,
Yanzu kuma gidan ashween zaki koma

Har ta budi baki zatsyi magana mammy tace
A' ah
Kar kice komai, daga yanzu zaki soma neman aljannar ki  wajen mijin ki,
Bana son musu to taurin kai,kinaji na ko?

Wani makallalen hawaye ne ya zubo mata
Ta gyada kai tace naji mamy

Allah ya miki albarka ,kuma fata na zakiyi amfani  da duk abubuwn da muka gaya miki
Sannan ena so na yi amfani da wannan damar na nema wa
Dan uwanki  ashraf gafara,
Kinsan zUciya kowa da irin tasa

Ba tan tama tace a'ah mamy,
Ni kam na fahimce  shi ..nice vam masa adalci ba duk da bason raina na bata masa ba,
Mamy ki dubi Allah ki yafe masa kinji mamy ?
Ta marairaice
Murmushin karfin hali kawai tayo tace bakomai jasmine,

Amma dole ya gane koran sa, babban laifi  kuma zunubi yayi nufin aikata akanki dawani abu ya sameki yau din
Meyake tunanin zan fada ma ashween?

Yamin adalci kenan in yasa naji araina na ci amanar hjy shahida?

A sanyaye ta ce a'a mamy maganan ma ta kare
Kiyi hakuri dan Allah..

Ganim maganan baAi tsaya ba tace ""Toh shiken jasmine ta so muje
Kar kuyi latti

Ba musu ta ja mayafin ta mamyn ta dada lullube mata fuska ta sake feshe ta  turare sannan suka nufo falon da su ashween suke

Dukan su kayi shiru suna kallon tahowar  ta don musamman ashween don sosai yake ganin ta sauya masa kamr ba ita din bace
Shikan Sa ganin ta a hakan ya sashi jin  wani sanyi na daban na ratsa brain dinsa....tana tahowa tananjin dar dar amma ko su daga ido akanta
Duk yadda kamal yaso su hada ido ko don ya tsokane ta amma sam ta tsime ta ki dagowa ma da kyuw bare tayi magana da kowa ...

Gefen mamy ta zauna a kasa inda jelar skirt dintan ya dada bazuwa ya sa ta dadayin kywu sai binta da kallo suke dukan su biyu basu jin ko kunya,

   Nan mamy ta yi gyram murya ta soma musu nasiha ta hada harda kamal din ma kalmashe su saida jikin kowa yayi sanyi
jasmine tuni ta soma tare kwalla a idanun ta,
Yanzun ne takejin tsananin missing din ammyn nata na tsuma zuciyar ta

Bayam ta kammala mamy ta riko ta har mota ta sata
    sannan kamal da mamy suka koma gefe
' taki ta daga kai amma hawayen mamyn ya sata dole ta fashe da kuka
Har  asheewn ya gama sallamar sa da su suka wuce enda jirgi zai tashi

Su biyu ne kacal  awajen  da shike first class ce yana gefe sai satan kallon ta yake don sam taki bude idon ta bare tashaki numfashi da kyu,yadda aka lullube haka take duk da maalyafin sharara ne

Shi dai damuwar sa yaga fuskan nata a sarari,
Gashi tun da suka shiga zamn kurmaye suka shigayi  don tunani kala kala ke yawo akanta wanda ya sa ta dada jin ta tsani komai lokaci guda ita burin ta amaida ta gida

Gefen zahida kuwa karfe 
6 dot jirgin ta ya iso yola
Don haka  bata bata lokaci ba ta shige makaken mansion din ashween da aka debe kusan rabin swamp forest din aka kawata shi

tamkar kana kasar waje haka environment din yake ga sanyin bisihiyoyi sunyi duhu sunyi dark green sai flowers red,purple, pink yellow ,harda wanda ba irin sa a kasar nan duk  sun taru sun haska wajen kamar wani garden...
su kansu  furannin gamshi suke fitarwa cikin sanyin dake ratsa wajen
Tsarin gidan tubarkallah

Amma Abu daya da gidan shine yayi nisa kadan da enda jama"a suke don haka shiru ne ba jin motsin kowa sai maiakata da security

Duk da ma yau ne zuwan ta na uku Anan zahidan ke baza mulkin ta da isarta musamman in ta nace sai ta biyo sa hutu ko weeknd a da chan
  
Musabbabin yin tafiyar ta porland asali don tayi iya kokarin ta taga ko wani ya faru tsakanin su amma sam yaki sai uban wulakanci daya mata
Bori,kuka ,har drowning kanta ta so tayi duk akan haka amma ba abunda ya canza kullum amsar shi daya bazai yi zina ba ta bari sai sunyi aure

Ita kuma wannan ba damuwarta ba ne don ta saba sosai wajen ex mazajen ta da guys din ta da chan
ga jaraban dake matukar damun ta musamman akan kyawawan maza,,

Toh kullum in sukayi akan haka shi yake lallabata sai ranar aka samu akasi ya nuna mata ya gaji  in har bazata cire maganan sexual reltionship  ba  ta rabu da shi, shi ya fasa auren ma,

  a hakan suka rabu taci kuka daga nan sai ta wuce porland don ta samu ta nema ma kanta mafita
shyasa ma ko cummunicating da ita bai yi  amma saboda nacin ta sai ya gwada mata ba fushi yayi ba hea expecting her to make a choice ko zama da shi ba romance ko rabuwa da shi kwata kwata....toh daga ranan ne bata sake ji ko ganin sa ba sai yau da ta yanki draw tazo yola daura da maganan kamal da sukayi dazu.

Daga cikin motar ta tayi Murmushi tana kallon enviroment din gidan tace home sweet home"" nazo nan bazan tafi ba komin tsiya komin bacin rai, sai abu daya daga cikin biyu ya faru

Ko ka biya min bukatu na ko ka aure ni,,
Ta shafa kan pet dog din dake gefen ta tana wani munafukin dariya kamr tare suke maganan...



😂😹hmm kaji wawiya..tooh fah.


*i Love,love yhu my fans*
*surriem*

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now