*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Ayi hakuri👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻yau dai sadaqan ruwan sanyi nakeyi zuciyan ku ta sauko🥛🥛🥛🥛🍶🍶🍶*
*Wani lokacin yadda muke so ba hakan bane wani lokacin kuma hakan ne,labarin duniya in akace abu daya za'a na maimaitawa baza mu karbi darasun da yakamata mu san su ba,like yadda ake sawa a films in anyi irin wannan yanayin sai ace cikin bai zube ba ko ace tsorata shi kawai tayi ,but no, no nace wani lokaci akwai muhimamin darasi a rayuwa wanda zuciya bazai bari ka koya ba har sai kayi makan ka ta'adi mai muni""musamman abunda ya shafi kishi da zaman aure .**Fatana fans suyo hakuri majority basu son ciki ya zube..ammma....*.🤒
*Zanso ku biyo ni kawai🤐🤐 kar ku cire rai ciki in da aure abu mai sauki ne.**❤ I lOVE YOU ALOTS mutanen arxiki💯*
*Im proud of ur stimulating and hrt felt comments and debate,grops dayawa pls kar kuce bana gani , nagode🤝🏼🤝🏼🤝🏼**Page▶72*
Duk rikicin nan dake afkuwa xahida na dakin ta tana kan kallon zoben da ash ya bata tana maganan zuci cikin nishadi
Yau burin ta ya cika ya ce zai aure ta finally,
Ko damuwa bata sake yi da tuno akwai jasmine ba, hasali ma yaune rana na farko da ta daga wayar mrs rod.Fuskan ta ba alaman imani amma sai ta sake muryar ta ta kuma bata reason din karya akan rashin daukar wayar tana kwana biyun..
Mrs rod bata damu ba dama tasan ko lpyarta ne
Ta tambaye ta yaushe zata zo abuja
Nan ta hado labarin karya da gaskiya akan halin da ake ciki da jasmine da ashween sannan tace komai ya wuce yanzu sunyi engagement har ya bata ring.Madam hidayat ena ka saka da zahida don murna
take ta soma fade fade yadda zasu shirya mata grand weding ceremony
Amma Zahida na kus da wayar a kunne kamar bata jin ta.A ranta tace tsohuwar munafuka ai ba barin ki zanyi ba,kema zan zo abuja kuma da cikalken shiri na zanzo na yake ki na karbe duk wani hakki na da kike kokarin dannewa muguwa.
A haka suka yi sallama na ta gane kan zahida ba kowa ya cigaba da sake saken sa.
Ash kuwa in tashin hankali na da karshe to yakai wajen ,don kaf sai da ya duba ko ena cikim garin baigan ta baiga mai kammanin ta ba.
Sai Karfe 12 na dare ya bar airpot ya san bazai wuci tace zata bar garin ba amma nan ma shiru
Sai ya hakura ya fito ya cigaba da zaga garikarshe a motar sa ya zauna gefen titi yana jimamin ena zai ganta gashi layin kamal baiya shiga bare ya kwantar masa da hankali karshe kife kansa yayi kan stiring ya cigaba da hawaye.
Jasmine kuwa Tana isa gidan su salma lokacin gaba daya bari jikin ta yake don effects din magani,
Amma sai ta cigaba da dauriya bata bi kan kowa ba ta haura dakin salmaWani rungumar juna sukayi da salma wacce take dan turo cikin ta
Tace lpya kuwa jasmine dis early morning a abuja ena yaya ash?
Bata ce komai ba dan tsaban yadda take ji ajikin ta
Salma Ta dada duban ta a hankali tace ah,ah jasmine ya dai lpyar ki kuwa ?Sai ta tsorata Tayi saurin cewa bayi zanje salma bari naje na dawo tukun
Salma ta dan ja gefe ta bata hanya bata ko lura da stain din dake bayan hijabin nata kadan ba
YOU ARE READING
SO MAKAMIN CUTA
General FictionIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez