*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'__Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶71*
'Zahida ta fito Ba kowa a wajen sai mai gadi da driver suna hiran su
Ba takalmi a kafanta sannan idon ta sun kafe sunyi ja zir da hawayen bakin ciki da kunci..jikin ta na bari tana kyarma ta kira su a gagauce ta ce ma driver ena zata samu hot acid?
Ya gwalo ido cikin mamaki yace madam babu anan kusa gaskiya
Sunayi suna dar dar don yanayin ta ya nuna alaman ba lpya baTace toh kaje ka bude gareji ka bude motar uban koma waye
Ka hado min ruwan batir yanzu tafada da commanding voice.Cikin tsananin tsoro dukan su sukayi shiru suna kallon ta basu motsa ba
Cikin Wani razannanen tsawa tace me kuke jira ne?look na baku 10 mints in ba haka ba harbe ku zanyi yau a gidan nan .ta ja gefe ta tsayaBa musu suka bar wajen
Kowa jikin sa na bari hanjin su na kuka don tsoroDuk sun sani cewa ruwan ba3 wani bin ma yafi hot acid illa domin kuwa zallan concentrated sulphuric acid ne wanda ko ma ginin block aka zuba sai ya narke ya zube kasa bare mutum..
,a yanayin zahida ko da ba'a fada musu ba sun san ba alheri za'a aikata da ruwan bat3n ba
Nan driver ya shiga kunce kunce ya soma hada ruwan ba3
Ganin yadda abun ke watso musu wani mummunan wari mai hatsari ma numfashim dan adam ya sa mai gadi yace wallhy wallhy nikam zan kira oga
Don Ba zan iya wannan aikin baDriver yace ka rage murya kar taji ka
Kayi sauri kayi hakan don nima bansan me zance ba in wani abu mummana ya faru.Nan mai gadi ya boye bayan bishiya ya ci kirar ash bai daga ba
Chan hikima ta zo masa sai ya tura masa tex massage.Suna gama hada ruwan ba3 ta karbe bata ko sauraran zafi da hargowan da yakeyi sai ta ajiye a dai dai kan step daya raba site din gidan
Ta kamo hanya ko ajikin ta sai sauri take ta tayo dakin jasmine.
Idar da sallar ta kenan ta zauna tana lailaya cikin ta duk hankalin ta ya koma kan yaushe ashween zai shigo don tana mugun jin missing dinsa.
Zahida ta banko kofa tayi Wani munafikin murmushi ta bangaje kofar sai dayayi kara
Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hankalin taJasmine ta mike tsaye a dan razane tace mata lpyar ki?
Dariyar hauka ta bushe da shi gashi kafar ta ba takalmi kanta ba dangwali sai uban hawayen takaici da ya bushe a fuskan nata.
Tace " yi min shiru munafuka karuwa, yar iska mai raba gindin ta a titi, yau ni zahida zan koya miki tarbiyan da uwar ki bata baki ba
Jasmine tace ahayye, kaji masu neman motar kano a china'wani tarbiyan ne dake wai goggo yaga gaban liman ?kije dai kiyi makarantar tarbiya ma kanki dan yanzu kece tababbiya,jaka.jahila anan wajen...
Zahida Ko sauraran wani magana daga bakin ta batayi ba tayi wuf ta chakoma hannun ta ta damke su duka biyu damka mai tsanani
Da shike ita kanta zahidan ba acikin hankalin ta take ba ta riga ta harba dokin zuciya wani karfi take ji da shi ma masifa..
Jasmine ta soma kokuwar kwace kanta a hannun zahida amma kamar bata komai
VOUS LISEZ
SO MAKAMIN CUTA
Fiction généraleIta ta fara tsanan shi a duniya,ta kuma kashe wanda ta fara kaunar sa,me kake tunani nan gaba da Allah ya sake hada su a wata duniyar da bata da abun kauna face shi? #yasmin #Ashween #zahida rodriguez