77

2.8K 201 2
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶77*



Gefen Jasmine kuwa duk da abubuwan dake damun ta dan dolen ta
tayi hakuri tana cin abinci normal
kuma ta soma dan sakewa har su dan yi hira sama sama da mamy "inda take fada mata za a soma gyara mata jikin ta tunda ta samu miscarriage,mamy tace ita da kanta zata kaita a dada kimtsa ta sosai ko dan taji dadin jikin ta.

Duk ana yi ne Sai dai zuciyan ta fall yake da son jin dalilin da ya hana ashween bai zago ya duba ta ba yau har sati biyu kenan...

Gefen mrs rod kuma ana neman karfe 8am na safe ba taga an fara kiran sharia'r ta ba sai ya sa ta shiga wajen judge tace ' mr judge dan maliki, ya dai an barni ena ta jira meye ne haka?

Yace calm down mrs rod
Na gaya miki Akwai muhimman abunda nake jira akan case din nan naki ne
Ki bani minti 20 za'a kira

Tace ince dai lpya ko?
Meyasa baka sanar da ni akwai jira acikin harkan nan ba.

Yace mata kar dai kimanta aikina da tsari
Kotun ne ta sauya lawyer mu da mai bincike da tantance  case, amma kinsan ai duk munyi maganan wannan dake ba matsala ko?

Tace of cous, yanzu shi ake jira kenan

Alkali yace eh,pls sit down and stay put, kar ace muna hada wani abun dake kinsan ansamin ido..

Ba tace komai ba ta juya ta zauna ta tare da harde kafa.

Ko minti 5 bata yiba da zama saiga shi comitten sharia sun soma shigowa

sai tana binsu da ido tana murmurshii tana Allah Allah minute of success dinta ya zo
Har wani lumshe ido take don farin ciki..

Ana kan shiga sai ga lawyer mai bincike da tantacewa ya dosu,shima ta bishi da ido tabbas wannan bata san shi ba,sannan fuskan sa ba wasa ko fara'a,

tana kau da kai kansa ganin wa zai sake shigowa
Sai Zama ya gagara ta mike tsaye cikin wani razanannen shocking tana bin zahida da kallo,
Ga jamal ,ga kuma jabeer tafe.

Take fuskan ta ya tsatssafo da zufa zuciyan ta yayi bugun tara tara , ta rufe ido gam tana dan bubbuga  kai a hankali ko zata tashi a mummunan mafarkin da take

Su kuwa Haka suka zo suka wuce ta gaban ta ba wanda ya mata kallon arziki
Kowa ya zauna aka barta a tsaye durus tana kan waswasin abun

Jin anbuga akalar sharia za asoma ya sa ta dan razana Ta zauna tsuliya a zage .

Gaba daya sai taji gwiwan ta suna karkarwa  hankalin ta yakai makura wajen tashi, jamal, jabir zahida ? Kai wannnan ba alheri bane.tace ma kanta.

Ba  bata lokaci aka soma shari'a
Sai gashi Tun kafin sharia yayi nisa, notin kan mrs hidayat ya soma kuncewa ta fara hauka.
musamman da aka kawo shaidan cewa tunda lailah ta mutu ,akwai lateef sannan bata da shaidan cewa yana raye ko ya mutu don haka anyi invalidating case din su lateef har sai an samo gaskiyan lamari in aka tabbata ya mutu shima sai azo ayi magana,kotu ta buga wannan,

Nan ma Ta hadiye yawu da kyar tasan wannan ya kubce mata kenan har abada ,

Sai aka cigaba anan aka dago na hanan hrnandez
Nan ne fa lawyer mai tantacewa ya bada korafin Hrod tana da will a karanta a kotu aga arzikin ma waye ne ,

mrs rod bata so haka ba,
Amma kasancewar akwai original will din Hrod a hannun lawyer wanda zahida ta bayar sai ta dakata dan dolen ta aka karanta.

SO MAKAMIN CUTATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon