89

2.7K 212 4
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*FOLLOW UP-TILL DATE post Via myWATTPAD*
*@SURAYYAHMS*
*Musamman wanda suke nema daga farko kuje chan zaku samu komai a saukake.thanks*


*Page▶89*



Jasmine kuka take yi ta rasa yadda zata yi musamman data ga hankalin zahida a tashe yake itama ba ta hayyacin ta ko kadan

Tsoron ta ma kar itama ta harbe ta ne yarda ta harbe kamal mercilessly.
Don haka ta cigaba da jero adduoi kala kala a bakin ta zahida batace uffan ba sai kuka take tana tuki da uban speed.

A lokacin zuciyan ta ya riga ya bushe yanzun zancen ya dawo sabowa bata ta kan ashraf

don ganin tania yau ya sa ta soma tunanin lallai akwai wani boyayyen al'amari game da su
Shiyasa ta ga dole me ma ta rike jasmine
Don dan tasan zai biyo ta kuma dole tasan gaskiyan lamarin sa.

Yau jamal ya diro nigeria bazata amma bai sanar da kowa ba sakamakon yana so yayi ma yan uwan sa surprise musamman ma ashween da ya sanar da shi matar sa yai zata tare.

Tun daga bakin kwana da ash ya dosu yake ganin taron mutane ga motar kamal a bude anyi cirko cirko ga ambulance.

gaban sa ne yayi wani irin faduwa ya kara sauri suka iso dai dai wajen, salma ne aka sa sai kuka take yi duk ta rude ana kokarin sa kamal a mota da gagggawa zasu tafi
asibiti

Wani sarawa kansa yayi a haukace ya yo kan kamal din ya soma kiran sunan sa cikin zafin nama'
Nan bada bata lokaci ba ya bisu asibiti shida jabieer aka yi  da kamal emergency

Da kyar Ashween ya ke iya tsayuwa don tsaban tashin hankali gaba daya ya kasa zama sai leke yake a operation room din ya ma kasa bin takan labarin meya faru.

An shafi kusan minti 40 a haka Can salma tace yaya har yanxu banga jasmine ba fa?sai ya juyo a hargitse ya kalle ta
Ya lumshe ido yana cewa innalilhhi wa enna ilahi rajiun,..

Jabir da tun tuni ya manne ma police report yana bin diidddigin labarin ai yana ji ance ba aga jasmine ba kuma eye witness yace mace ce tayi harbin a ransa sai  yace
Tabbas mrs hidayat ce ta ci nasara akan zahida ta gurbata mata tunani

Don haka ya sulale ya kama hanya bai sanar da kowa ba  ya nufi neman mrs hidayat a gidan ta don ya ci uban su ya karbo jasmine.

Zahida dake kukan fitan rai ta rasa ma me zatayi ma da jasmine din
Haka kawai ta ajiye ta kan kujera ta daure hannun ta da kafan ta tace zauna nan don in kika motsa sai na harbe ki...

Nan ta rufe ta a dakin tayi waje abun ta

Daga nan bata tsaya ko ena ba sai ta kama hanya gidan mrs hidayat anan ma ta gama buguwa da cocaine kanta ya dau chagi sosai...tayi rigingine akan seat din motar ta idon ta sun yi ja kamar garwashi
  Tace daga farko zan fara da wacce ta fara kawo matsala a rayuwa ta ni duniyan nan ya ishe ni haka.

Don haka Tana yin parking ta shiga gidan zaune ta samo mrs hidayat wacce daga ganin yadda zahida ta shigo take rawa da kanta tana jajjan iska tasan tana cikin radadin kunci da tashin hankali matuka

Mrs hidayat tace zahida lpya kuwa,
Ko amsa ta bata yi ba sai ta fito da bindiga tayi nuni ma kan mrs hidayat din anan ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciya..
Kafin Tace...ki sake fada min waye Ashween kuma meya kawo shi rayuwa ta?

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now