7

2.7K 263 1
                                    

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Salam sisters*
'''Kullum ki kasance bayan kowani sallahr farillah kina karanta kulakulan nan guda uku(surah nas,falaq,da nas)
Babban kariya ne daga mahassada daga cikin mutum ko aljani,makiya,mugaye, sannan kana cikin gadin malaikun tsaro daga duk wani cutar wa da zai shafe ka''' ,

*Yadda ake yi*

'''Sallahn safiya wato fajr da magrib, zaka karanta ko wanne sau uku uku,

Sauran (zuhr,asr da ishai)kafa daddaya

Allah ya taimake mu baki daya ameen'''




*Page▶7*



Bori sosai jasmine ta shigayi, ita kanta tasan harda fushin abun da take ji a ranta ta hada take ma salma
Wacce tuni ta gama fahimtar ta
'to jasmine in magana bai kare kema sai ki rama  tunda duk hakurin dana ke baki baida ma'ana awajen ki

Shiru tayi ta kau da kai

Nan itama ta mike da niyyar barin waje
Da sauri ta damke ta
Ta shaqwabe fuska tana dada marairacewa

Salma tayi "msww tace,
Iskanci
To meye kuma? ba fushin zaki cigaba da yi ba

Ah ah..tace" sannan ta kalle salman a sanyaye
Amma kun ganni lokacin da muka shigo da yaya ?

Gyada kai salma tayi alaman eh'"

Kuma kinga
Wacce tazo daga baya ta same mu?
  Eh mana salma tace tana kallon ta

Dan shiru tayi tana sake sake aranta  "can tace  Uhhm na tambayeki mana salma'
   Zama salma tayi kafin tace ena jin ki '
Ki fadi tsakani da Allah
Dani da budurwan yaya wayafi kywu ?

  Wani boyayyen murmushi tayi na mamaki tace
Are you ok? Lpya kike wannan tamvayar jasmine

Ni dai kawai ki fada min.. Tace fuska a shake

Tabe baki kawai salma tayi
Ganin yadda jasmine ta daure fuska snnan tace"
" tsakani da Allah  aunty tania tana da kyau sosai .

   Harara masu zafi ta watsa  ma salma bazata ta Kau da kai gefe tun kan ta sake cewa wani abu
" wacece kuma aunty tania ?
Salma ko  Kamr bata san meta keyi ba
Ta sake cewa girlfriend din yaya ash mana

Dum taji kanta ya sara
Sai ta yi shiru batace komai ba
  Itama salman shirun tayi tana binta da kallo
Cikin kula ta kamo hannun ta
"jasmine' kywu irin naki ba za a hada da nata ba..ke ta daban ce"
  Kin gan ki kuwa da kuka shigo tamkar wata angel kowa ke yake kallo
So its obviius kin fita kyawu ki dena hada kanki da ita  ..
Duk maganan da salman take 
Ji take kamar karya ne
Don gaba daya taji
ta tsani komai a lokacin
Ga zuciyan ta sai maimaita sunan tania yake idon ta kuma yaki dena nuna mata smiles din da suke
Xchanging da yaya ash dazun

Dan buga table a hankali salma tayi "ke,  Ohhh kin tambaye ni na baki amsa kin wani share ni ko
Ba laifin ki bane jasmine ni kinga tafiya ta ma .
Tsaye ta muke zumbut itama kamr mai jinnu

Sai yanzu salman ke lura da yadda idanun ta suka sauya sosai
kallo daya zaka mata kasan tana cike da damuwa '

  Zauna jasmine  ta fada a sanyaye
Ruwa ta tsiyaya mai sanyi 'ta mika mata' ga shi pls take

Ba musu ta karba ta sha
  Tana ajiye cup din ta sauke numfashi a hankali ta kife kanta kan tebur
Whts wrong ?
Salma ta tambaye ta cikin kulawa
Tana dafa ta

SO MAKAMIN CUTAWhere stories live. Discover now