Babi na biyu (02)

2K 121 2
                                    

A hankali ta ke tafiya kace dawisu, Dam! Ta ji gaban ta yayi wani irin bugawa sai dai tana dago idon ta su kayi four eyes dashi Yana zuba Mata harara ta gane dalilin faduwar gaban nata. Sum sum ko Kara Kallon shi ba tayi ba ta sa Kai ta wuce abinta domin in ma miskilanci ne to tabbas ita ma A ce. Ba Wai Mai Mata kwarjini bane kaman yanda ya kewa sauran Aa ta yadda he is charismatic sai dai Kuma ita ma self confidence inta ba zai bar ta taji tsoron shi ba.  Ko Kara Kallon sa ba tayi bata SA kanta cikin gidan bikin aiko ta ci karo da Suraj kanin shi yana ta faman Mata smiling. "Suhaila wannan irin kyau haka" murmushi tayi Mai kayatar

wa ko Bai fada ta San ta kwaso kyau domin ko Daman ita in Mai kyaun ce. "Thanks Suraj Mami na ciki ne?"
"Ehmm tana verandan Baffah (Alhaji Abdullahi)
  "Bara naje ta aika a kirani ne"
  "Emhmm Naga mutumin naki Hala ko gaisawa ba kuyi ba"
"Harara na fa ya dinga yi niko na dauke Kaine nayi shigowa ta nasan yanzu haka magana zai min akan gyale na"
"Ke dai da ya Muhsin rigiman ku sai ku, bara na bashi sako" ya fadi sannan ya karasa wurin Muhsin in da ke tsaye Yana Kallon su.

    Suhaila ya' ce a gun babansu Muhammad na dakin Uwargida Hajjah fati. Ita ce Yar fari tun wurin haihuwar ta Allah yayi ma Mahaifiyar ta rasuwa. Da Baba Muhammad da Yayan shi Abdulrahman gabadaya a kano su ke da Zama don Haka bayan rasuwar matar shi sai ya bar ma Mami saudah matar wanshi Suhaila, tayi farin ciki ba kadan ba Saboda Allah Bai taba Bata haihuwar Ya' mace ba gabadaya maza ne. Muhsin, Suraj, Yusuf sai auta Sabir.

  Ana gama daurin aure aka fara Shirin tafiya da Amarya gidan ta da ke Kaduna. Karfe Daya dai dai motocin Kai Amaryan su ka bar katsina cikin ikon Allah karfe hudu dai dai suna Kaduna, sai da aka fara zuwa gidan Yayarta Safiyya da ke zaman garin su kayi Sallan la'asar kafin aka wuce da ita gidan surukan ta sannan daga bisani ta karasa gidan ta da ke kinkinau. Baiwar Allah ta Sha kuka tare da Yan uwanta da su ka Taya ta. Da dare aka shirya dinner da ya samu halittan manyan mutane sosai da ke angon ma Dan manya ne, shima asalin shi dan katsinan ne su ke Zama a Kaduna.

Ranar Sunday gabadaya aka watse kowa ya Kama gaban shi aka bar Amarya daga ita sai halin ta.

Fadila matsawa tayi sai ta je gidan Ya Najib don da mamaki taji shiru haka bai Zo bikin ba. Da farko su Meema kin zuwa su kayi sai da tayi ta rokon su sannan su ka tafi. Anty Sumayyan ce kawai a gidan sai babyn da Yar wata bakwai sannan masu aiki. Ba yabo ba fallasa ta tarbe su ta sa aka kawo musu abin Sha sai dai ba wanda ya dauko sai Fadila, Kuma ita ma fadilan kawai ta dinga ja da Hira "Fadila kwana biyu ko waya Koh?" Murmushi kawai fadilan tayi don da suna yawan waya daga baya abin ya yanke. Shiru ba ta ga Ya Najib ya sa ta kasa shiru ta yi magana "Anty Sumayya ya Najib fa?"

"Najib ba ya Nan yayi yafiya Yana Dubai kwanan sa Uku kenan a can"

"Au Allah sarki ai ko ba mu ji labari ba"

"Ehmm da ke tafiyan ta zo a kakkauce ne"

"Arif fa?"

"Wai Arif ai yayi 2 weeks a gidan sister da ke Abuja na Kai shi ya ga yan'uwa ne wlh kinsan in yaro bai shiga cikin yan'uwa sai kiga ya taso bai San su ba to me aka yi kenan"

"Ehmm gsky da ke wasu basu dauki Yan uwa da mahimmanci ba ai bayan Manzo Allah sosai yayi magana akan zumunci. Duk wanda ya yanke zumunci ba ya tare dashi ko. Sai kiga wasu sun yi preferring wasu akan wasu alhalin duk Dan uwanka ne" Da biyu meeman ta yi maganan Kuma gabadayan su sun gane.

Ba su wani Dade ba su ka tashi za su wuce kasa shiru Asmau tayi "Anty Sumayya ba ki tambaye mu biki ba ba ki samu zuwa ba" maimakon ta ji kunya Aa Sai Fadila ma ce ta ji Mata. "Ehmm fa Aminatou ta yi aure ance Nan garin aka kawo ta ko?"

"Ehmm" kawai Asmau ta amsa.

"Kinga ita ma sai a dinga Kai Mata Arif ya ga yar'uwar shi tunda tana kusa" Meema ta Kara Fadi. Ita dai Suhaila magana daya tayi "a gaida Arif na kawo mishi chocolates baya nan baby Kuma she is young Dana bar Mata"

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now