Normal su ka koma labari har su ka isa Zarian. Yana fidda Mata akwatin gate man in apartment in su ya zo ya shiga dasu. Nan meema ta gane ta iso Daman ita tun dazu ta iso. Fitowa tayi taran ta ta iske ta tsaye da Muhsin suna magana. Shi ya fara hango ta yace "Ah ah Amarya" sai lokacin Suhaila ta juya ta ganta. Da sauri ta karasa wurin tayi hugging inta tace "Ya meema amarya i miss you"
Gaisawa su kayi da Muhsin yana tsokanan ta da Amaryan Faisal. Kasa shiru tayi tace "Kai Yaya Muhsin Kai ma dai naga alaman kwanan za ka kara zama angon ai" bude baki yayi yana kallon ta speechless. Juyawa yayi yana kallon suhailan alamun neman karin bayanin. Dariya ta mai ta juya kanta. Ita dai meema sallama ta mishi ta shiga ciki.
"I tell her nothing" tayi saurin fada bayan meema ta shiga.
"Za ma kiyi bayani yarinya" dariya ta mai yace "Ni bara in wuce ban son yin dare" ya fada yana shiga motan
"Tou Shkkn, be safe"
"For you?" Ya fada yana kallon ta
Nodding kanta tayi tana murmushi yace "I love you Suhaila" blushing tayi this time sannan ta fara mishi waving.
Tana shiga meema ta fara Mata dariya tace "na rantse da Allah da ki yarda da Kar ki yarda Soyayya kuke da Ya Muhsin"
Bata fuska Suhaila tayi tace "miye na rantsuwan? Na Miki musu ne?" A tare su ka fashe da dariya meema tace "somebody is glowing from a new relationship"
Text ta ma Asmau tace "he confessed" alkawari ne ta dauka and she fulfil it.
Ba a dade ba Asmaun ta Kira ta tana tsokanan ta.
Yana isa Abujan ya Kira ta da azama ta dauka yace "Na Kira in ce wa yar budurwata na isa lafiya"
"What a name" ta fadi tana dariya
Yace "soyayya ce"
Dariya tayi tace "ka isa lfy? Ya hanya?"
"Lfy kalau, ya gajiya?"
"Bbu fa"
"Okay, let me take a rest. We will talk tomorrow"
"Tou Shknn, a huta lfy"
"Sai anjima, love you" da sauri ta kashe wayan ta na murmushi. Tunani ta ke yi Wai daman haka Ya Muhsin ya ke ko kunya baiji? Ta fadi a ranta. Namijin kenan, so free ba ruwan shi.
Ko da ta tashi washegari sai wurin ten ta shiga school. Ba laifi anyi lectures da ke second week in resumption ne.
Karfe daya da Yan minutuna ta fito lectures. Wayan ta da ta sa silent ta dauko domin ta cire Nan ta tarar da msg in shi
"Sorry i couldn't call you in the morning. Text me when you are done with the lectures. Luv you"
Wato he intend to always remind her of the love thing. Ita kam har yanzu jin abun ta ke da gaske. Masallaci su ka tsaya da wata course mate Inta su kayi sallah. Tana wurin printing in course form call in shi ya shigo.
Da sauri ta dauka tace "Ina wuni Ya Muhsin" shiru taji har za ta kara magana a hankali taji yana Fadin "na gaya Miki ban son sunan ko. Not anymore kuma. Ba haka ake yi ba"
Dariya tayi "Afuwa tou. Ya Abuja and conference"
"Lfy am done. On my way back... I want to see you." Jin yanda yayi sounding serious ya sa tace "sai kazo, safe journey"
Da Yamma lis ya iso Zarian. Direct apartment in nasu ya nufa, tun kafin ya iso ya Kira ta.
Wani smiling ke kwance akan fuskan ta sanda ta fito. Ta window ya ke kallon ta har ta karaso. Bude Mata kofa yayi yace "Bismillah Love" kallon shi tayi ganin yanda shima ya bude ido yana maida martani ya sa tayi saurin sadda Kai kasa cike da kunya.
BINABASA MO ANG
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...