"Mutumin banza mutumin wofi, ni zan dauki aure na baka ka wofintar dashi? Ance maka ita yarinyar son ka ta ke ta aure ka? Banda iskanci an wulakan ta ka anci maka mutunci na dauki yarinyar na baka don in share maka hawaye ashe ashe duniyan ci zaka mun. To wlh Uban ka ma bai isa ba, in kuma iyayen na kane su ka daura ka akan hanya ai to gasu nan su min bayani" ta inda baffah ke shiga ba ta nan ya ke fita ba, ba mai daman ba da hakuri domin ko cewa zai yi dashi aka hada baki aka ci amanar yarinya ba su ma yi maganan ba ya hada ya zage su tasss balle kuma sun tanka.
Baba Muhammad ko irin kallon da ya ke aikawa Najib kadai ya isa ya tabbatar mishi ba lafiya ba, alamu ne na ya gama shan na wuri baffah ya zo ya same shi.
Tun Najib na sauraren Baffan har ya daina fahimtan abinda ya ke nufi "tashi ka bani wuri mutumin banza kuma Kar ka sake dawo min nan sai da takardar sakin auren da na baka." Abinda ya ji kenan a kunnen shi, ai bai San sanda yayi kasa yana rokon Baffah ya mishi aikin gafara kar ya raba shi da matan shi ba. Hade rai yayi ya banza dashi Amma yana lura da yanda gabadaya ya rikice yana neman fita hayyacin shi, lura da yayi idanun shi sun kada ne yasa yace mai "tashin ka ban wurin zan neme ka gobe" sidif sidif ya fita daga falon, side in goggo Fulani ya nufa domin ya tabbatar akwai shawarwarin da za ta iya bashi.
Bayan fitan Najib Baffah gabadaya ya hada su ya musu tatas, da abinda laifin su ne da Wanda ba nasu bane. Bayan ya sallame su ne ya bukaci Abbah Abdulrahman ya tsaya. Kallon shi yayi sannan yace "Abdulrahman ba sa Kai dane na gari kuma na maka tarbiyya dai dai gwargwado Amma kuma sai aka yi rashin saa ba kiyi dace da mace na gari ba ko kuma ka kasa daukan mataki akan ta. To Ina so in sanar maka na gaji da rade raden da ake yi game da yaran gidan ka gabadaya in aka cire Muhsin. Umurni na ke ba ka ba shawara ba duk yanda za kayi ka bi hanyan da ya dace in saurari canji daga gareka." Godiya Abbah yayi cike da takaicin Mami, har ta Kai da yau mahaifin shi ya zaunar da shi akan shi, sani ko duk an wa gidan shi akan rashin tarbiya, to fa mataki kam dole ya dauka.
Dariya Goggo ta wa Najib bayan ta gama sauraron abinda ya kawo shi tace "Amma dai wlh anyi ragon Namiji, Kai yanzu akan mace ne duk ka rikice haka. To bara in gaya maka ba abinda ya Kai mace saukin tafiyar wa sai dai ko in ba ka iya wa sha'anin su ba. Kace Matar ka ba ta son ka ko? Shin kana Mata abubuwan da zai sa hankalin ta ya karkato gare ka? Haba Kai ko to ai ko mazan zamanin da ba suyi karatu ba ba haka su kayi ba. Ita fa mace wuyar ta ka gano lagon ka dana Mata son ka shikenan an wuce wurin" dariya yayi yace "danawa kuma Goggo sai kace wani kunama?"
Hararan shi tayi tace "to ai soyayyan da namiji a zuciyan mace wani sa'in yafi harbin kunaman dafi. Ka kyatatawa matar ka, ka San damuwan ta ka ririta ta ka zauna kayi hira da ita sannan ka nuna Mata duk duniya ba fa macen da tafi ta yanda kaga sarauniya haka za ka kula da ita ina mai tabbatar ma ko sai ta zamo kaman baiwa a gareka domin duk abinda za tayi ta faran ta maka za tayi shi ko da kuwa itan za ta cutu, mu Mata da kake ganin mu Allah ya halicce mu da zuciya mai rauni. Amma fa duk abin nan ka zama mai fada aji a gidan ka bance ka dauki raini ba bance kuma kayi tsauri dayawa ba." Murmushi kawai ya ke yana kallon Goggon ji yake kaman ta yaye mishi dukkan damuwan shi, ya dade a wurin ta suna hira har lokacin da Baffah ya shigo side in.
Najib na ganin shi ya shiga taitayin shi. Tsoho kenan mai ran karfe Sam ba ya daukan wargi "Mai ragon Namiji ke min a wurin Mata?" Sadda kan shi Kai kawai yayi kasa.
Goggo ce tace "a toh nima fadan da na gama mishi kenan wanna ai ragon ci ne"
Murmushi Baffah yayi yace "in ko ba kayi wasa ba Mata sun zame maka matsala kenan don haka tun wuri kasan mai kake yi. Gobe goben nan ka dauki matanka ku wuce in kuma na kara jin wani abu to tabbas ni da Kai ne a cikin garin nan." Sai a lokacin ya saki murmushi mai kayatarwa yace "nagode Baffah Allah ya kara girma" zai fita Baffan ya kara Kiran shi yace "Kai zo Nan" dawo Najib in yayi yace mai "Ina Mai ma kashedi da babban murya akan zumunci, wannan ba hurumi na bane fadin manzon Allah ne (S A W) yace duk Wanda ya yanke zumunci bai tare dashi, ka ga ko karshen tabewa kenan. Don haka ka gyara, yaran ka dangi ba su San su ba sai da matsala ta afku haka kuma aka aura ma ka yarinya ka dauke ta kayi gaba ba ka tashi kawo ta ba sai da lamarin nan ya afku, ance maka ba ta son ganin iyayen ta ne? Kai ba ka San kawaici ba ko?"
"Kayi hakuri Baffah in Sha Allah zan gyara"
"To a gyaran" abinda Baffan ya fada kenan kafin Najib in ya fita.
Nan kuma ya je ya sake iske Mahaifin shi. Da farko fada ya mai sosai sannan ya gangaro nasiha, shi Daman Najib bai jin shi domin ya San shi mutum ne Mai sanyin zuciya, haka kuma Yana matukar tausayin su daga shi har Suhaila wannan kuma Yana da hadi da soyayyan da yake wa mahaifiyar su ne. Yana da mugun kawaici akan su duka biyun shiyasa ko wani hukunci ake musu bai cika sa baki ba sai dai ya ja su gefe ya musu nasiha.
Su baba kabeer ma da Abbah sun Mai nasiha sosai, karshe gidan Ba Usman ya shiga wanda aka yi auren su rana daya. Ga mamakin shi lafiya kalau su ke zaune da matar tashi, yanda su ke tafiyar da junan su kadai ya tabbatar mishi akwai so Mai karfi tsakanin Ma'auratan.
Text ya turawa Fadila Dan bai jin zai iya kara haduwa da ita a ranar. Yana da labarin Kiran ta da Baffah yayi ya bata hakuri da nasiha sannan ya tmby ta za ta iya komawa gidan Najib in. "Bakomai Baffah zan koma ko bakomai ai dan uwa nane" shin wani irin adalci ne Fadila ba ta mai ba a rayuwa? Tausayin ta ke jin Yana kara ratsa shi, Tabbas ya jinjinawa Baba kabeer da Ummi, sunyi matukar kokari gun inganta tarbiyyan yaran su.
VOUS LISEZ
ABINDA KAKE SO
Roman d'amourCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...