Kanta a sunkuye har ta gama sauraron mahaifinta. Kaman ance ta dago su kayi ido hudu da Faisal yana shigowa falon nan take idea ya fado mata da sauri tace "Yauwa Ya Faisal kazo a daidai" bai gane mai ta ke nufi ba har yazo ya zauna kaman yanda aka umurce shi. Cikin dakewa ta ce "Yauwa Abbah daman Ya Faisal ne kadai mu ka daidai ta dashi yace zai zo ya same ka kuyi magana yau" siririn murmushi Faisal ya saki gane idan zancen ta ya nufa. Lallai yarinyar nan dole ya koya mata hankali "Hakane Abbah daman munyi da ita yau zan same ka" murmushi mahaifin nata ya saki cike da farin ciki...
"To ma Sha Allah ke daman kinsan Faisal ne kika tsaya kina ta mana yawo da hankali?"
Faisal in ne yayi saurin taran ta ganin tana kokarin yin magana yace "Ayi hakuri Daman ni na nemi na boye in saboda we already plan on sai year in da zata gama school"
Kallon su Daddyn ya ke kaman yana son gano wani abu amma ganin duk sun sadda Kai kasa yasa bai fahimci komai ba. "Kasanar da mahaifin na ka?" Girgiza Kai Faisal yayi yace "Aa Daddy zan dai fada mai Yau in"
"Tou Shknn kace ya nemi ni ko ta waya ne" yana magana ya tashi ya bar su a wurin shi yana mai hamdallah a zuciyan shi da ganin Faisal, bai da wani sauran tashin hankalin bincike ko wani dogon batu.
Mummy ce ta dago ta kalle Daddy da ya shigo dakin ta murmushi kwance akan fuskan shi yace "To Maman halima yau hankali ya kwanta ko?"
"Yar ta ka tayi abinda ta saba ko tun safe na lura da ita ai Daman" ta fada tana cigaba da abinda ya ke yi.
Dariya yayi yace "ke dai kin sa wa mama ta ido gashi kuwa ba ta bani kunya ba kam a yau domin kuwa sirikin ki yana can na baro shi a falo" a firgice ta daga tana kallon daddy "Amma dai Kai ka kawo shi ko?"
Girgiza Kai yayi yace "ita ta kawo abinta"
"Toh Daddy kun gama magana da yaron ne har ka amince ka barshi da ita"
"Ai da ke ma abun ya zo da sauki na gida ne"
"Ban gane ba Dan Abokin ka ne ko dan Dan uwan ka?" Girgiza Kai yayi yace "let me save you the questions. Danki ne Faisal"
Da sauri mummy ta Mike tsaye tace "Faisal kuma?" Ba ta tsaya sauraron amsa ba tayi hanyan kofa domin ganewa idon ta.
Zaune su ke a dinning arean kowa na harkan gaban shi. Tun da Daddy ya fita ba abinda ya kara shiga tsakanin su. Shi dai Faisal mamakin lever inta ya ke, ita kuma tunanin yanda za ta fahimtar dashi bukatun ta take ba tare da yayi wani tunani ba.
Ganin mummy akan su ya sa duk su ka juyo suna kallon ta. Dukan su biyun harara ta zuba musu "Can one of you explain lamarin da na samu yanzu?" Shiru ne ya ratsa na yan sakwanni kafin Meema tace "kiyi hakuri mummy i didn't get the chance to tell you ne..." Hararan da mummyn ta aika Mata ya sa ta yin shiru. Ganin haka ya sa Faisal in fara magana "mummy da ma ni na nemi mu boye saboda school inta nace mu bari sai ta gama" kallon su tayi dukkan su tana son tabbatar da Gaskiyan al'amarin.
Sai dai she sees nothing. Daman ta San Faisal ba mai hayaniya bane ita ko meema akwai zurfin ciki. "Faisal are you sure?"
"Very sure mummy"
"Do you love her?"
Nodding Kai kawai yayi Mata ba tare da ya amsa ba.
...
Kano, Nigeria.
Tunda Suhaila ta turo ma Muhsin numban prince in bai samu Daman Calling ba sai bayan la'asar.
Bayan sun gama gaisawa cike da girmamawa yace mai "Sunana Muhsin Abdulrahman Malumfashi"
Da sauri Prince ya ce mai "oh Muhsin ya dai? Its been a while gsky" da ke already sun San juna through friends in su.
"Lafiya kalau Alhmdlh. Jiya Suhaila ke ce min kunyi magana da ita za ka zo ganin Abbah"
Cike da kunya yace 'Eh tabbas munyi haka da ita. Daman jiran amsan ta na ke sai inje inga Abbahn"
"Okay, Mahmud since meye sa ba ka nemi ganin nashi ba naga kaman kun dade sosai tare ai ko?"
"Hakane Muhsin Amma da yake kasan komai sai Allah yayi. I wanted to but mai martaba ya riga ya ban Mata which i can't deny"
"Ayyah Allah ya sa albarka but sorry to disappoint you Mahmud. Abbah ya dade yana cewa Suhaila ta fiddo miji hakan ya gagara shi kuma hakan ya sa ya Mata miji. Fada ma ta ne kawai ba ayi Amma har an gama komai lokaci kawai ake jira a sa rana" wa'azi ya fara mishi duk Dan ya samu ya amince da bukatan shi.
Ajiyar zuciya mai karfi prince ya sake ba tare da yace komai ba Muhsin ya cigaba. "Shiyasa naga tun kafin kazo din gwara in gaya abinda ake ciki kaga kar ka Sha wahalan zuwa ko ya ka gani"
Da kyar Mahmud ya fara magana "A gsky Ina son Suhaila sosai kuma Ina burin ta zamo karkashin inuwa ta" wani irin faduwan gaba Muhsin ya ji ya Kama shi.
Mahmud ya cigaba "Nagode sosai Muhsin, zan so tayi biyayya wa mahaifin ta kaman yanda nima nayi ma nawa. Amma please i want to let you know that am always available don't hesitate to talk to me"
"Bakomai Mahmud Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi gare ku gaba ki daya. But please I need one favour. Don't reveal the issue to her saboda Abbah ya na so ya mata maganan da kanshi yanda za ta karbi zancen da hannu biyu"
Sallama su kayi cike da jimami. Nan ta ke Muhsin ya Kira Faroukh yana fada mi shi yanda su kayi.
Dariya Faroukh yayi yace "now go and hit on your girl"
"Faroukh ka sa nayi karya which ka San ba hali na bane shin in ya gano fa?"
Dariya Faroukh yayi "Kai kaji min mutumin nan, lokacin da na fada ma miyesa ba ka ki ba? Sai yanzu zan kazo kana kawo min kabali da ba'adi? Je ka nemi tuba kawai"
Shi dai Muhsin bai ce komai ba don gabadaya tunanin shi ya tafi gun yanda zai bullowa al'amarin. Bai so ya Kai kunne Abbah ko Mami kafin ya tunkari ita mai gayya mai aikin.
....
Da azama ta amsa wayan prince.
"Ya Kira ka ne?"
Dariya yayi sannan yace ma ta "lallai wannan kaunar ta ku ta gsky ce"
"Fada min mana me ke faruwa?"
Tsaf ya bata labarin yanda su kayi da Muhsin.
Shiru tayi kafin tace "do you think he is serious?"
"Ehmm may be, just wait and see. Kilan shi ne mijin"
Yanayin muryan ya tabbatar tsokanan ta mahmud in ya ke. "prince serious mana na fa San Ya Muhsin is so close to Abbah. Kuma he is not the kind that says things anyhow Anya ba ka ganin gsky ne?"
"It maybe true but ba ra in fada Miki wani abu. Ko shakka ba nayi Muhsin na son ki Suhaila. So you should just pray for the best"
Godiya ta mai kafin su yi sallama. Ita ta kira shi su ka hada plan akan ko ya Kira he should just act cool with it. Da alama Amina ta dau shawaran na ta ta jawo mijin ta a jiki domin gabadaya ya hakura da lamarin Suhailan. Taji dadin hakan sosai dalilin da yasa ta saki jiki sashi har su ke maganan Muhsin in kenan.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...