Babi na Saba'in ( 70 )

1.6K 116 33
                                    

Ana idar da sallan magreeb.
Su mummy da Anty Mimi ne (Sister in Anty Mummy mahaifiyar ta) su ka dauke ta zuwa side in Abbah da ke zaune da sauran Yan uwan shi. Kanta a kasa har kowa ya gama fadin albarkacin bakin shi bayan sun gama sa Mata albarka tare da Mata fatan alheri. Baban ta dai bai ce uffan ba daga shi har Abbah sai dai baba kabeer ya kalle su yace "ba kuce komai ba?" Abbah ne yace "Ni ai Ina ga ba wani abunda zan kara cewa domin na Mata dukkan wani nasihan da ya dace." Kallon mahaifin ta yayi yace "Muhammad, dole fa ka sauke nauyin nan"

Daga ita sai mahaifin ta su ka rage a wurin. Dago yayi ya kalle ta sannan yace "Suhaila nasan duk abinda zan fada Miki iyayen ki sun riga sun fada Miki." Dan shiru yayi sannan yace "hakurin Nan dai da zakiji ana ta fadi shine dai jigon zaman tare. Mahaifiyar ki har ta koma ga mahaliccin mu ina mai alfahari da ita. Mace ce mai juriya, hakuri, sanin ya kamata, most importantly addini." Yanayin yanda ya ke maganan kadai yana murmushi ya isa tabbatar maka mahimmanci wanda ya ke magana a gare shi. "Saboda haka Ina fatan za kiyi koyi da ita. Kar kiyi wasa da addini sannan ki kasance mai yawaitan karanta alqur'ani shi ma kadai kariya ne. Allah ya tabbatar da alkhairin sa a gare ku. Tashi ki je ana jirin ki, Allah ya Miki albarka" yana rufe baki ta tsince kanta da daura kanta akan cinyan shi. They weren't really close Amma yau wani soyayyan shi taji yana ratsa ta. She really do loves him.

Da aka Kai ta gun Mami ko bayan yan uwa sun gama Mata nasiha, fadawa jikin mamin tayi tana kuka mai cin rai. Ita ma mamin kasa jurewa tayi sai da ta koka. Da kyar aka raba su domin kasa Mata wani maganan kirki tayi. Da ke ma mamin ta Sha sa ta a gaba tana Mata dukkan maganganun da ya danganci zaman aure. Ba wani duties na mahaifiya da Mami ta bari ba ta ma Diyar ta Suhaila ba. She is more of Suhaila's mother than Muhsin's. Shi ya sa ya kan tsokane ta da Yarinyar Mami ita ko tace Kai kuma Yaron Abba koh.

Gidan Amarya.

Kanta a kasa da addu'a a bakin ta su ka shiga gidan. Ba ta wani kallon gaban ta a haka aka karasa da ita dakin da ya ke mallakin ta. Kan gadon ta zauna tana jin mutane na ta shiga da fita da Ma Sha Allah a bakin su. Gajiya tayi jin abin ba na kare bane. Friend inta Khadija da ke gefen ta ta taba. Da ke duk sun natsu ganin oga tar su ta daina biye musu. Matsawa tayi sosai kusa da ita tace "Dan daga min abin nan na gaji wlh" Asmau da taji tane tace "Ai Khadija ki cire ma ta laffayan ne gabadaya ta huta ai yana da nauyi" wani relief ta samu bayan an cire in. Idanuwan ta sunyi ja jawur tsabagen kuka.

Sai da mutane su ka fara ragewa sannan su ka fara kimtsa gidan duk da daman an gyara komai an yi mopping. Sai da kowa ya watse ya rage ita da friends inta da su meema sannan ta baro dakin ta na duba gida. Dakuna uku ne a gidan manya manya kowanne da toilet a ciki. Sai parlor da dinning area gabadaya in ash. Ga mamakin ta harda guest toilet a parlon. Ta dinning arean akwai kofan kitchen though akwai wani ta gaban dakuna biyun da ke kallon juna. Kitchen in babba ne ya Sha kaya kam, harda karamin dining table a ciki. Ta kitchen in akwai kofa da zai yi leading inka to backyard in gidan. Shukoki ke wurin sai gefen laundry. Sannan ta gaba ma akwai parking space dayawa. Architectural building in gidan ya burge ta sosai. Ba unguwa daya ya ajiye ta da Rahma ba. Ita Sharada ta ke phase ll Rahma kuma gidan ta na Jan bulo.

Wasu kayan akwatunan ta na lefe aka fiddo suna jera Mata a drawers. Sai lokacin ta samu ganin lefen da kanta bayan labarin da ake ta bata. Komai yayi ma Sha Allah. Akwati daya ta gani gabadaya Abayas ke ciki. Wani irin farin ciki ne ya ratsa, he knows her love for them, shi yasa specifically ya siye su dayawa.

Suna gama kimtsa gidan su ka sa turaren wuta nan da nan ko Ina ya dau kamshi. "Amarya a tashi a shiga wanka koh" Fadila ta fada.

"Wanka kuma? Wai sau nawa zanyi wanka yau? Sai dai kace wata kifi" dariya Asmau da meema su ka saki suna fadin "Yarinya ba ki ga yawan wanka ba ma tukunna"

Fadila dai share su tayi ta shiga bayi tana kokarin hada Mata ruwan wanka. Tana fitowa ta dauki jakan ta tace "To Amarya Ni kam zan tafi na bar Yarinya a gida"

ABINDA KAKE SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora