Babi na ashirin da uku ( 23 )

902 89 0
                                    

  Washegari, tun da Asuba da Fadila da meema su ka farka ba su koma ba. Asmau dai wasu hidimomin su Fadila ko a tsorace ta tsinci ranar don haka ta dauka Qur'ani tana ta karanta wa. Bakwai na safe Asmau ta hadawa Fadilan ruwan wanka sannan ta bukaci ta shiga tayi sannan ta fito su karya. Lokacin Meema ta farka sabanin sauran da su ke ta kokarin baccin su, a tare su ka wuce can gidan Baffah su ka iske ana shirin kai musu breakfast don haka su ka nufi gidan baba kabeer bayan sun gaida kakannin su. Suna shiga su ka iske Mukhtar da Faisal su ma da alamun shigowan su kenan tsaye su na magana da Ummi.

"Ku kuma mai ya fito da Ku da safen nan" Ummi ta fada tana kallon su.

"Ummi munzo gaishe ku ne" meema ta ba ta amsa tana murmushi sabanin Asmau da ta lura Mukhtar ya kafa mata ido ko kunya bai ji ba hakan ya sa ta jin duk wani iri.

Daburcewan da tayi yasa Ummi dago su, harara ta zabga musu dukkansu sannan ta fada tana kallon Asmau "mun gode da gaisuwan in abu kuka zo dauka maza Ku dauko Ku zo ku tafi" da toh su ka amsa sannan su ka karasa cikin gidan. Kallon gargadi Ummin ta aikawa Mukhtar kafin su ka cigaba da maganan da su ke yi.

Ko da su ka fito sun iske sun shiga mota za su wuce, Faisal ke driving saurin tsaida shi Mk yayi sannan yace musu "ku zo mu sauke Ku" table baki meema tayi ganin yanda mutumin nata ke ta cin daci tace "Ya Mukhtar kuyi tafiyanku za mu karasa ai ba nisa" Mukhtar zai kara magana Faisal ya fisge mata hade da bide su da kura. Siririn tsaki meema ta ja tana fadin "kaji dashi mai bakin hali Kaine bakon mota" ita dai Asmau dariya tayi sannan su ka koma gidan. Fadila har ta gama shiryawa nan da nan su ka hau karyawa ana hira ana ta nishadi amma fa banda Suhaila da Safiyyah kusan su ne karshen tashi don haka karyawan su daban su kayi. Ita dai Asmau yarinyar ba ta wani mata ba sai dai ta ga Yar uwarta Suhaila na matukar yi da ita.

Karfe goma sha daya safe aka daura auren a nan babban masallacin gidan Baffah. Baiwar Fadila ta sha kuka har ta gaji Asmau taya ta tayi su meema ne dai ke rarrashin su. Ana idar da Sallahn azahar aka faa shirin kai Amarya gidan ta da ke Kaduna saboda da gudu yin dare. Har aka gama mata nasiha kuka ta ke sosai, da kyar aka rabata da Ummi it a kanta ummin said da ta koka ganin za ta rabu da babbar yar ta da suka yi matukar sabo. Motoci kusan bakwai aka yi zuwa Kaduna da ke ma mutane dayawa sun tsaya saboda dayar Amaryar da za a kawo musu. Mukhtar ke driving motan da Amaryar ke ciki, Asmau na gaba sai ita, Mummyn Meema da Maman su Faisal a baya. Har ta gaji da kukan tayi shiru. Mukhtar dai mamakin su ke bashi daga Fadila Har Asmau ganin yanda su ka dage suna kuka.

Asmau na kirge sau uku Mk na waya da Safiyyah. Hakan yasa don haushi ko tanka shi ba tayi ba duk da yana so ya mata maganan sai hade rai tayi. Sarai ya fahimce ta daga baya ma bacci ne ya kwashe ta. Shidda da mintuna su ka isa Kaduna amma ba su isa gidan Amaryan ba sai kusan magreeb, hakan yasa nan da nan mazan su kayi shirin tafiyya masallaci. Da wani Sabon kukan Fadila ta shiga gidan ta bayan an umurceta da yin addu'a sannan kuka ta shiga da kafan dama.

Ma sha Allah gidan Amarya ya dau kaya yayi kyau duk da bai kai tsohon gidan shi girma da kyau ba wannan in ma mawadaci iya zaman mutane kadan. Master bedroom ne farko a side da ka shiga hade yake da small parlor nashi sai kuma babban parlor in yana dauke da 2 bedrooms sannan akwai kitchen da store a gefe. Tsakar gidan kuma zai iya daukan motoci biyu zuwa Uku. Suna shiga aka hau haraman Sallah kafin aka gabatar da Abinci wanda Maman Faisal ce ta sa aka yi shi daga gidan ta. Sun karawa Amarya nasiha kafin daga baya manyan su ka watse zuwa gidan su Faisal aka bar Amarya da kawayen ta. Anty meena ce last in tafiya, ta tashi tana hada kayanta Suhaila ta tsokanota "Maman baby tafiya zaki yi ke ma na dauka a nan za ki kwana" hararan ta banka tace "miskila kin fi mahaukaci ban haushi yau kuma maganan ake ji ne? In kwana a nan in muku me? Bayan ga gida na can yana jira. Kin taba ganin inda uwa ta kwana cikin yaranta ai ba zai yiwu ba na ta barin miji na cikin maraici bawan Allah Dan ma yanda da hakuri" siririyan dariya meema ta yi sannan tace "Ai ai ga riban hakuri nan mun gani a jikin ki" dariya ta ke tana nuna cikin da ke jikin Anty meenan. Duk da halin da su Fadila da Asmau ke ciki sai da suka dara. Tsaki ta ja tana fadin "Yaran sun fara aure dole Ku raina ni, kyautar Allah kuke wa dariya" da sauri meema tace "mu a wa? Rufa mana asiri muma Allah ya samu a danshin ki" mikewa Suhaila tayi da ke yau yan mutuncin na kanta tace "Anty na share su kinji mu je in raka ki, Yar uwa ta so ki raka ni" Tare su ka fita gate har ta shiga motan ta tada ita da Mutane ukun da suka bita za su kwana a gidan ta.

A kofar gidan su ka hadu da Angwaye wai sun zo siyan baki saboda washegari ba sai an sha wahala ba kowa ya watse kawai a bar ma'auratan da halin su. Najib ne da abokanan shi uku sai kuma su Muhsin, Mukhtar, Faisal da Yusuf da su ke waje. Komawa cikin gida Suhaila ta yi ta sanar dasu. Kememe Muhsin da Faisal su ka ki shiga, a cewar su kannen sune fa wani siyan baki za su je? Su ba sa son raini.

Ba tare da wani bata lokaci ba su kayi abinda ya kawo su Wanda duk yawancin Amarya da Angon aka yiwa nasiha sannan su ka ajiye musu kaya da kudin siyan baki da suka kawo.ba tare da anyi ciniki ba. Yawancin maganan abokanan Najib in ne su kayi. Mk ne karashen fita ga mamakin ta gani tayi ya yafito Safiyyah da hannu ita kuma ta tashi ta bishi, tana kallon yanda zainab ke binsu da harara ta kara kulewa. Ba tagama takaici ba taji zainab na tambayan ta "Asmau Wannan ce budurwar Ya Mk in da kika fada min" bata rai tayi ta yi kaman ba taji ba dole zainab ta kyaleta. Meema kam da kyar ta ke danne dariyarta. Suhaila sarai ta gane abinda ke faruwa sai dai ba wai harkanta bane dan haka ba za ta shiga ba.

Sai 10:30 Safiyyah ta shigo da ledoji a hannun ta. Suhaila ta fara mikawa daya "Yar uwa ga sakon ki" murmushi suhailan ta mata hade da fadin "Thanks" sauran gabadaya Asmau ta mikamawa "Wannan na Amarya ne please a ajiye mata" ta fada tana nuna ledoji biyu. "Daya Ango ya aiko daya kuma matar friend insu Ya Mk" tabe ba ki Asmau tayi ta amsa ta ajiye gefe ganin duk ba abin ci bane
 

ABINDA KAKE SOTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon