Da kyar da sudin goshi Abbah ya sauko ya bar Suhaila ta koma makaranta, duk ta rame tayi wani iri, magana ma da kyar ta kanyi daman can ba gwana bace. Sai da Mami ta je ta sako Muhsin a gaba akan dole ya je ya lallaba Abba ya bar Suhaila ta koma makaranta tun shi ya ja komai. A cewar Mami in da daya ganta shi ya mata fada ya maida ta makaranta da duk hakan bai faru ba. Muhsin in ya yarda zai ma Abbah magana amma sai da sharadin za ta rabu da friends inta sannan kuma za ta koma ta zauna da su meema in ba haka sai dai a fasa kuma zai sa a sa mata ido a gani. Ba yanda mami ta iya hakanan su ka amince, sannan fa muhsin in yaje ya lallaba Abba. Duk Muhsin da ne ga Abbah amma Abbahn na matukar ganin girman shi kasancewar mai gujewa sabon Allah ba kamar sauran Yan'uwan shi ba. Sau dayawa Abbah na gani Muhsin baiwa ne daga Allah shiyasa ya ke mishi lakabi Kyauta daga Allah. Sarai ya San da halin Mami na kiyaye ka'idojin boko fiye dana addini tun kafin ya auro ta sai dai kash a lokacin so ya riga ya rufe mishi idanu, yana ga kaman zai saita ta bayan sun yi aure. Wanta abokin shi ne tare
Su kayi sakandiri da ma jami'a. Sun shaku sosai hakan ya say har Gombe yana zuwa gidan su shima haka har katsina yana zuwa, yar zumunci su ka kulla tsakanin iyayen su. Abin mamaki gidan su Mami gida ne na mutunci mai matukar tafiya da addini sai aka samu cikas Mami ta fita daban a gidan, ba don komai sai zurfi da tayi a karatun ta sosai hakan yasa ta ma boko mummunar fahimta, ta ke ganin kaman abubuwan da ta daura yaran ta akai shi ne wayewar. Abbah yayi takaici, ya nuna mata amma ina Mami fa tayi nisa sai dai addu'a.Muhsin in da kan shi ya Kai ta Zaria, ya sa aka kwaso kayan ta gabaday ta bar gidan ta koma wurin meema. Ko da can su na da wurin ta ba dai ta ga daman zama da su bane kawai. Dakin meema ta tare sanin Sarai za aji su day Asmau domin ko ta su ba wani zuwa daya tayi musamman yanda Asmau ta gano halin ta ta ke son daura ta kan hanya. Ita sai a ganin ta zaman takura kawai za tayi, Muhsin ya daura ma ta takunkumi dayawa.
"Zan tafi, saura kuma naji wani abu sabanin alkwarin mu kin San me zai biyo baya" harara ta wulla mishi sannan ta kauda kanta tace "ban fa son sa ido malam"
Siririyar dariya ya saki yace "I know mai hali ba ya canja halin shi amma ki sani ni Muhsin Zan matukar ba ki mamaki wannan karon" banza tayi dashi ta wuce ciki ta barshi a nan. Kwafa yayi a ranshi yana fadin "yarinya nasan maganin ki"
...
Kaduna, Nigeria
Kaman yanda Asmau ta yi alkawari weekend na zuwa ta nufi kaduna. Ita kadai ta tafi sahoda meema na zuwa practical asibiti har weekend, Suhaila kuwa kowa harkan shi ya ke tsakanin sai dai abin da have rasa ba. Bayan haka ita kanta suhailan ba za ta je ba Sarai ta san Muhsin ya sa an sa mata ido duk abinda ta yi to yana kunnen Abbah. Shiyasa ko school ba ta cika zama ba gudun friends su gano an sa mata takunkunmi su raina ta, lectures kawai ta ke zuwa Amma ko karatu a gida ta ke yi.
Ranar Asabar Asmaun ta je Amma kuma Najib bai na ya je Lagos wani aiki, Amma yaran suna nan su ita kanta Fadilan ba za ta ce ga dalilin da yasa ba a Kai su ba, su dai ko a jikin su. Kallo daya Asmau ta was kawar ta tasan ba lafiya, cikin siyasa ta sa Fadilan sanar ma ta wasu abubuwa da ke damun ta. Shawarwari ta ba ta sosai game da fada mata ta yawaita addu'a in Sha Allah komai zai zo karshe haka kuma kar ta gaji ta cigaba da kyautata mishi da yaran gabadaya, watarana da kan shi zai gano hakan.
Kallon ta Fadila tayi sannan tace "Ya kuka kare da Ya Mukhtar" murmushi mai ciwo Asmau tayi "You know it won't work out Fadila, na bashi hakuri mun dawo kaman da"
"But you love him" hararanta Asmau tayi "it doesn't matter, its over kawai"
"Tou Allah ya sa hakan ya fi alkhairi, Ya Umar is so nice you know"
"Nasani" ta fadi cike da son a basar da zancen. Hiran su ka koma, sannan su kayi girki. Zama da su Areef ya sa Asmau jin son Yara a ranta, yaran akwai shiga rai ga saurin sabo barin ma Areef.
Washegari Sunday kafin ta koma sai da ta je ta gaida Anty meena da kuma gidan su Faisal.
...
An sa ranar auren Muhsin da Rahmar sa 3 months, Asmau da Umar 7 months bayan ta gama 100 level kenan sai na abokin mukhtar Yusuf tsakanin su one week ne na Yusuf in zai riga.
Asmau dai ganin abun ta ke kaman wasa sai dai zuwan ta katsina ta tabbatar da ba wasan bane ganin yanda Mama Aisha da Ummi su ka fara shirye shiryen bikin gadan gadan. Ita dai duk tayi sanyi, ba laifi ta sake wa Umar in suna hira har zuwa wurin ta ya kan yi. Mukhtar ma su kan yi magana Amma kuma kaman yanda yayi alkawari ba wani abu da ke shi tsakanin su da ya wuce na tsakanin Ya da kanwa.
Suhaila har yanzu su na tare da prince Mahmud duk da dai ba wani sake mai ta ke ba Amma ba ta son wulakanta shi. El-mustapha kuwa suna na nan daram dam duk da ba Wai son shi ta ke ba Aa a ganin ta da irin shi ta dace Amma kuma duk takunkumin da Muhsin ya sa mata bai sa ta daina abubuwan da ta ke ba, sai da fa cikin basaja. Tana nan da friends inta. Rahamar Muhsin ko ji ta ke kaman ta kashe ta ba ta taba haduwa da mutum ya tsaya mata a rai ba irin ta, gashi dai kowa yabon ta ya ke ita ko ta tsani ta shiga hostel ta ganta. Murmushi Rahman ke ma ta ta daga mata hannun sanin alakar su da Muhsin duk sanda su ka hadu yake kawai ta ke Mata amma ba ta son ta.
A haka su ka fara Exams in semester, inda kowa ya maida hankali ga karatun shi. Ga Fadilan ko abun gabadaya ba sauki don ma ta na maida hankali a lectures shiyasa abun ya zo mata da sauki.
Kaman wasa ranar ta fito Exams in karshe ta ji jiri na diban ta, saurin dafa bango tayi ta samu wuri ta zauna. Wata yar class insu Zahra ce ta lura da halin da ta ke ciki, kusan duk hall in su biyu kadai ne su ka fito. "Lfy kuwa Fadila Kabir" da mamaki Fadila ta dago tana kallon ta, ba tayi tsammanin yarinyar ta san sunan ta ba saboda ba ta shiga harkan yan class insu to haka zahran ta ke har ana mata sheden girman Kai. Murmushi ta kirkiro tace "ban jin dadi ne wlh shiyasa na dan zauna"
"Sannu ko, xa a zo daukan ki ne?" Girgiza Kai Fadila tayi, Najib bai gari a Napep za ta koma. "In ba matsala mu je in sauke ki mana to"
"Sai in baki wahala kuma?"
Murmushi yarinyar tayi tace ma ta "Ai layin mu daya da ke na san baki sani ba, muje ki gani" ba musu Fadila ta bita sabods ba ta ga alamun cuta gun yarinyar ba. Ai kuwa layin su daya da ta sauke Fadila gidan ta ta nuna mata gidan su ashe ma gidaje biyu ne kadai tsakanin su.
BINABASA MO ANG
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...