Babi na arba'in da hudu ( 44 )

975 93 4
                                    

Kaduna, Nigeria.

Tabbas zama ta sauya salo a tsakanin ma'auratan biyu. Ita kanta Fadilan ta gano ta na da laifi a al'amarin kaman yanda shima mai gayyan wato Najib ya gano nashi.

Daman dai gidan ta kullum tsaf tsaf ne sannan kuma girki ba fashi haka ita ma kuma ba ta zama da kazanta kullum tsaf za ka ganta ita da yaran. Amma kuma mai? Duk da haka sun samu matsala domin wadannan abubuwa ba su kadai bane abun bukata.

To yanzu kam tabbas ta fara aiki da shawarwarin mama Aisha da kuma na kawarta Zahrau Wanda yanzu su ka tamke sosai su ke amintakan. Zahrau yarinya yace ba kaman sauran Yan Mata masu rawan Kai ba domin ita akwai kamun Kai ga sanin ya kamata, tabbas ta Kai ta ga hanya na kwarai. Misali, Mamaki Najib ya shiga bayan dawowan su kaduna saboda yanda ya ke samun tarba duk sanda ya dawo aiki, tarba ya ke samu na musamman. Tun daga bakin kofa ta ke taro shi, ta mishi sannu da zuwa sannan ta amshi jakan shi. Tun daga nan ta ke zama abun kallo a gareshi saboda dressing inta ma ba kaman na da bane da kullum ta ke sanye da atamfa ko abaya. Shiga take na kananan kaya Wanda ya ke matukar tafiya da imanin shi, har kanta ado ta ke mishi ga Jan lalle da ba ta rabo dashi. Yana iso wa zata hada mishi ruwan wanka, kafin ya fito ta ciro mishi kaya hatta abinci yanzu ita ke serving in shi suna ci yana janta da hira haka kuma idanuwan shi ba sa barin kallon ta. Tabbas yanzu ya San Fadila ta samu gurbin zama a cikin zuciyan shi da ma rayuwan shi gabadaya, har bai so tafiya ta Kama shi ya dinga jin wani iri kenan. Bayan ya tafi waya ko an dinga yin shi kenan.

  Zaune su ke a parlor ita da friend inta Zahra suna hira, Zahran na nuna mata abubuwan da ta fara shiryawa game da bikin ta.

Unexpectedly ta ji ana bude gate ko kafin ta duba ko shine ta ji su Arif sunyi wurin motan da gudu suna fadin "oyoyo Daddy"

"Bara na tafi gida ma karasa hiran ta WhatsApp tunda mai gida ya dawo" murmushi tayi tace

"He didn't even tell me he is on his way"

Hararan ta Zahra tayi tace "don't tell me you haven't change completely mana, don't you Know suprises. Please je ki tarbi mijin ki ni da ban yi aure ba ma na fi ki sanin romantic abubuwa"

Kafin tayi magana sai jin muryan shi tayi suna gaisawa da Zahra.  Tsayawa tayi tana kallon shi tana smiling ta ma rasa abun yi gabadaya. Zahra na fita ya jawo ta yana fadin "you are you not happy to see me? Don't you miss me?" Sadda Kai kasa tayi cike da kunya tace "so much"

Dago kanta yayi yana mamakin kunya irin na Fadila da har yau ya ki karewa. "Really?" Nodding kan tayi. "Then show me"
Hugging inta yayi sosai a jikin shi yayi pecking in ta a cheeks. Hannun shi ta ji cikin rigan ta yana shafa kasan maran ta "how is my baby? Two days ba mu gaisa ba" cike da kunya ta boye fuskan ta a kirjin shi. Dago kanta yayi yana fadin "Wai wannan wani irin kunya ne love? Seriously its have to stop, Amma bakomai na San maganin ki"

Sakin ta yayi yana fadin "to hada min ruwan dimi in wanka ko gajiyan Nan ya tafi"

"Eyyerh sannu" hararan ta yayi yana fadin  "don't act like you care just show me mana" siririn dariya tayi ta tafi hada mishi ruwan. Dan neman rigima sa ta a gaba yayi yana fadin "am damn tired baby, ba zan iya komai Allah. You shall help me take the bath" kaman ta sandare a wurin haka ta tsaye, sai dai fa shi kam gogan na ta da gaske ya ke.

Ganin za ta bata mishi lokaci ya sa ya gun ta gadan gadan. Hulan da ke kan ta ya fara flinging dashi yana fadin "Ke yar kauye ce Allah, wa ya gaya Miki har yanzu ana wannan kunyan? Ki tsaya Nan Yan Mata su kwace Miki miji a waje" ba ta San lokacin da ta zabga mishi harara ba. Dariya yayi yace "iyyeh ashe dai ana kishi na" bai tsaya wata wata ba ya dauke ta cak ya jefa a ruwan wankan da ta hada mai. A bisa dole ta hakura ya cire ma ta kayan da ta ki yadda da. Wasanni ya fara Jan ta dashi tun tana janyewa ba ta San sanda ta fara ba da Kai bori ya hau ba. Ta kan zama musamman ta yi ta mamakin irin soyayyan da kulawan da Najib ya ke nuna Mata a Yan kwanakin Nan. Da ya ke ya San ba ta San da dawowan shi balle ta aje mai abinci. Shiryawa ya sa su kayi daga ita har yaran su ka nufi haddaden eatery. Varieties kala kala su ka ci a wurin sai dai ko kadan bai yadda anyi almubazzaranci ba. Domin shi a tsarin shi if you order for something you must finish it all.

...

Watanni da dama sun shude, zuwa yanzu cikin Fadila yayi girma sosai duk da watan haihuwar ta bai riga da ya tsaya ba. Duk wata kulawa da ya kamata ba Wanda Najib bai nuna  Mata, abu ko ba Sai tace tana so ba ya ke kawo ma ta. Yanzu kam ta tabbatar da soyayyan shi gare ta kaman yanda itan ma ta ke jin shi sosai. Sun riga da sun zama tsintsiya madaurin ka daya, duk wani matsalolin su tare su ke zama su warware. Game da su Arif kuwa tuni ya riga da ya sakan Mata koman su kuma ya amince da irin tarbiyyan da ta ke basu.

A bangaren Muhsin da Suhaila ko wani irin shakuwa ke kara shiga tsakanin su. Duk wanda ya San ta a da to fah kallo daya zai Mata ya San ta canja in ka cire miskilanci ta da ado, Wanda su kam a jinin ta su ke. Ba Suhaila kadai ba hatta Mami da Abbah ya tsaya akan ta gadan gadan har kusan rabuwa su kayi. Dole ya sa ta ta natsa ta shiga taitayin ta, ta fara koyi da hanyar Gaskiya tun tun can Daman ba Wai ba ta sani bane Aa a tunanin ta wayewar xe ta zo da haka. Allah ya mu dace, Amin.

Zuwa yanzu sosai tayi nisa a karatun da su ke, ta ga kuma fa'idar abun ba kadan. Duk da tun can daman itan mai basira Amma yanzu abun ya kara yawo. Ba wani matsala tsakanin su da Asmau a yanzu. Sai ma shawarwarin da su ke ba ma juna. Abu daya da Asmau ke fadi Mata a kullum shine tabbas Muhsin yana sonta, sai dai ta kasa gasgata hakan la'akari da yanda ya ke ji da Rahmar sa. Hakanan weekend za suje su gaishe ta ko kuma itan ta kawo musu ziyara. A hankali ta fara aiki da shawarwarin da Asmaun ta bata...

A bangaren Asmau kuwa, sha'anin biki ya taso ta gaba gadan gadan. Ita dai ba wani maraba ta ke da abun balle ta dage wurin ganin komai ya tafi dai dai. Su meeman dai dole su suka tsaya Mata ake komai. Tana iya kokarin ta taga komai ya daidai ta tsakanin ta da Umar sai da lokaci da dama hakan ya faskara. Mukhtar kuwa kwata kwata komai ya daina shiga tsakanin su, hukuncin kenan da ya yanke musu. Tun tana bin shi da mssg da call ta ga kaman she is not welcomed, dole ta hakura ta daina. Sai dai ta kan ga kaman da gangan ya zo ya sa Mata soyayyan shi sannan yanzu yazo ya guje ta duk da ita ta fara neman hakan a farko. In ta dage da addu'a ta kanji saukin abun amm fa kuma zuciyan ta ya riga da yayi nisa a tarkon shi.

A haka dai biki ya karaso, 2 weeks to bikin ta tura mishi mssg "when are you coming?"

As expected "in 1 week time" shine kawai amsan da ya turo Mata.

Duk wani gyare gyare da amare ke yi ta nayi ne kawai ba Wai da son ranta ba. Abu daya ta ke da tabbaci shine ta nemi zabin Allah, toh fah ta San Allah ya zaba Mata abinda ya fi zama alkhairi a rayuwan ta.

A gun Ummi ta samu labarin isowan shi Abuja. Kaman a mafarki ranar da dare ta ga call in shi, she couldn't pick duk farin cikin Kiran nashi da tayi. A ganin ta riga da tayi salama, magana dashi zai you destroying duk wani tanadi da tayi akan shi. Saboda she ought to avoid him har zuwa time din da za a daura auren ta.

ABINDA KAKE SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin