Da Yamma Umar ya kirata. Cikin motan shi ta iske shi a waje yana zaune don haka kai tsaye ta karasa wurin mai zaman banza. Tun ta karasa ya bude mata kofa yana mata murmushi. Kaman ance ta waiga ta hango Mukhtar ya fito daga gidan Baffa tare dasu Aliy. Da gan gan ta rike murfin motan tanawa Umar murmushi hade da fadin "thank you" sai da ta lura ya kulu tukunna ta shiga motan ta rufo.
"Asmau ke ce haka kusa?" Ya tmby cike da mamakin lamarin nata.
"Lafiya Ya Umar ni ce mana"
"You have changed a lot, I hope its for the best?"
Shiru tayi tana tunanin mai za ta ce mai. Shin tana ma Umar adalci kuwa? She is just using him to revenge on MK. Anya ba ta daukan hakkin shi kuwa? Har ga Allah tasan ba ta ji Umar a ranta sosai kaman da. Kawai dai tasan she can marry him in za a ajiye soyayya a gefe kenan.
Ganin tayi shiru yasa jikin shi yin sanyi. Ganin haka ya sa tayi kokarin kakolo murmushi. Ta window ta hango shi har yanzu yana nan tsaye hankalin shi na kan motan ya saka musu ido kawai yana kallo.
"Ya Umar please za ka iya kaini Gida zan dauko Abu"
"Haba dai muje mana"
"Zan biya gidan su Fareeda in amshi sako"
"Just don't worry princess ko ina kike son zuwa am taking you there"
"Let's get going" ta fadi a hankalin, idanuwan ta na waje tana enjoying fushin da taga Mukhtar ya shiga. Alkawari tayi sai ta rama and she succeed.
Har idan ba tace za ta ba sai da Umar ya kai ta, gashi a gidan ma ta dan dade. Shi ko mukhtar bawan Allah bini bini ya duba cikin gida ko ta dawo amma shiru, har fadila ya je ya tmby tace bata dawo ba. Gabadaya ya damu gashi wayarta har yanzu na hannun shi gashi kuma bai son kiran Umar kar ya zargi wani abu. Tun yana jurewa har ya kasa zaune ya kasa tsaye, zuciyan shi sai raya mishi abubuwa Mara kyau ya ke. Bisa tilas ya daure ya kira Umar ganin har
9:45 pm amma shiru basu dawo ba. Sau biyu yana kiran wayan ba a daga ba gabadaya hankalin shi ya tashi, a na ukun ne Asmau ta mikawa Umar wayan bayan ya shigo mota. Mr Biggs ya shiga domin siyo musu abubuwa."Mk ya akayi ne?" Ya fada bayan ya amsa wayan.
Ba ta ji mai mukhtar ya fada ba ta dai ji Umar na fadin "okay bari in tsaya in amso maka gamu nan ma dawo wa gidan ai" siririn murmushi Asmau ta saki sanin ba abinda Mukhtar ke so...
Suna parking tayi saurin fita domin ta shige gidan kafin su hadu da Mk. Sai dai tana shiga gate ta ji an fisgo hannun ta. A tsorace ta juya zata sa kara yayi saurin rufe mata baki hade da girgiza kai. Hannun ta ya ja direct har zuwa lambun da ke bayan gidan su. A harzuke ya ke kallon ta kaman Wanda ya ke shirin kifa mata mari hakan yasa jikin karkarwa. Har yanzu yana rike da hannun ta hakan yasa ya gane rawan da jikin ta ya ke amma sai ya sha mur "ina kuka je? Ba ki da hankali ne zaki bi namiji waje da dare kuma Ku dade" galala ta tsaya tana kallon shi "au tsargi na kuma yanzu kake" duk da tsoron da take ji ganin yanayin amma kuma hakan bai hana ta magana ba. "In nayi ma ai ba laifi bane ko akwai idan kika ji musulunci ya yadda ka kebe da namijin da ba muharammin ka bane" girgiza kai tayi sannan tace "tabbas babu amma ai ya yarda abokin wasanka ya rike ma ka hannu ko?" Saurin sake mata hannun yayi yana huci yace "bakomai Asmau ashe so laifi ne tunda har ya kai da shigan raini tsakanin mu ko?" Kaman diran mikiya zancen ya saukan mata a kai. Nan ta ke taji jikin ta yayi sanyi. A fili ta fara girgiza kai tana magana a zuci. No, ba raini tsakanin ta da Ya Mk, yafi karfin hakan a wurin. Yana da mahimmanci da kuma girma na daban a rayuwan ta. Ganin ya fara samun galaba akanta ya sa ya fara magana "Dan na miki abu shine zaki dinga musguna min kina ramawa bayan na baki hakuri? Saboda kinsan it will have effect on me ko? After all kinsan kishi ya sa nayi komai ko Asmy? Ban son ina matsa miki, ban son inga kin takura amma shin ya kike son inyi da nawa zuciyan? Kin tausaya min mana. Ko ba komai ai na kamaci tausayi da kulawa a gareki ko bakomai amma nagode" kaman jira ta ke ya rufe baki ta saki kukan da ya dade yana cinta. Rikicewa yayi gabadaya ya rasa abun yi da sauri ya sa hannun shi yana goge mata hawayen da ke fita daga idanunta "Ya salam! Ya isa haka dan Allah, I didn't meant to makes you cry Dan Allah kiyi shiru" kaman kara zuga ta yake, rike kan shi yayi yana jin zafin kukan nata har cikin zuciyan shi. Bai San sanda ya jawo ta jikin shi ba yana lallashi. Shesheka ta fara yi kafin hankalin ta ya dawo jikin ta ji hannun shi a bayan ta, da sauri ta fara mutsu mutsu kwace daga jikin nashi, sakin ta yayi yana fadin "don't cry again please ko kina so nima nayi kukan?" Girgiza kai tayi kaman wata karamar yarinya sannan tace "am sorry Ya Mk ba zan kara ba"
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...