Babi na talatin da biyar ( 35 )

950 94 6
                                    

Ba laifi zaman nasu da Suhaila, suhailan na matukar taimaka mata da abubuwa da dama haka kuma in Yan maganan na Kai su ka dan taba hira. Ta warware Amma still Najib bai barin ta tayi aiki dayawa. Zuwan Suhaila Zahra ta hakura ta tafi Gombe, Amma Dan zaman da su kayi tare ba laifi jinin su ya hadu da ke dukkanin su akwai miskilanci.

Kwanan Suhaila goma a gidan, da weekends ta ga musu girki kenan ta fito falo ta iske Fadila ta fito daga dakin ta "Antyn na an tashi kenan" hararan ta Fadila tayi tace "Wai Suhaila me ye sa kike min haka? Sai ki ki tashi na ko?"

Murmushi suhailan tayi tace "rufa min asiri, dana yana hutawa ki sa in tashe shi?" Ilhama ce ta taho da gudu ta shige jikin Fadila tana boyewa Arif. Dukawa Fadilan tayi ta daga ta sama tanawa Arif da ya biyo ilham in dariya.

"Yanzu wannan katuwar yar kike dakawa Faddi? Kar fa ki ja mana matsala" Suhailan ta fadi cike da tsokana. Fadilan za ta tanka ringing in wayan Suhaila ya katse ta. Ya mutsa fuska tayi tace "oh my God! Wai duniya ya zanyi da prince ne?"

Fadila ce ta bata amsa "Marry him kawai sai ki huta"

Da sauri Suhaila tace "tabdijam as second wife? In fact i can't even marry him ne ma kawai"

"Then let him go"

"As if i didn't try to, yanzu haka he is insisting to come and see me, nasan yanzu haka locating ina yayi ya zo nan" gama maganan ta kenan ya turo mata text yana kofan gidan, dole hakanan ta fita ta iske shi a mota.

Sun fi 30 minutes suna magana, ta rasa gane matsalan shi gabadaya, sai dai kallam son da prince ya ke mata kadai ba zai bari ta aure shi ba, sanin cewa she will just be hurting him.

Fitowan ta daga motan kenan ta hango Najib da Muhsin. Fuskewa tayi kawai ta nufi cikin gida. Kasa daurewa Muhsin yayi sai da ya tanka "Najib ta ya za ka sa mata ido tana abinda ta ga dama"

Murmushi Najib yayi sannan yace "rigiman ku da Suhaila ta fi karfi na Muhsin but if you can believe me tun da ta zo ban ganta da wani ba sai wannan. Ka sani ko shi din da gaske ya ke?" Muhsin bai San lokacin da ya aika mai harara ba yace "in da gaske ne ashe da ba zaka ganshi wurin ta ba Kai tsaye ai ya san hanyar kano ko? To kafa na kafan ta yau tare zamu koma kano" Najib bai tanka shi ba har su ka karasa cikin gidan.

Da ke daman Fadilan ta san sa zuwan su. Kwanan Muhsin biyu kenan a kaduna yazo yin abu a KASU, dawowan Najib daga Adamawa kenan ya mishi ya dauko shi a airport shine su ka karaso gidan tare.

Ba su cika awa daya a gidan ba sai ga Asmau da meema. Wani irin hamdallah Muhsin yayi Dan ko yau ba abinda zai hana shi tafiya da Suhaila Kano, Dan kwata kwata bai aminta da zaman ta a gidan ba.

Sai bayan la'asar yayi haraman tafiya. Kai tsaye ya kalle ta yace "ke dauko kayan ki mu wuce ko" sakin baki tayi ta na kallon shi, tabe baki tayi, tayi saurin dauke idanuwan ta. A ranta tana fadin sauranta da gadaran ka ba zai kare a kaina ba.

"Kar ki bata min lokaci" ya fadi hade da karasa wa waje. Ba Wanda ya tanka su har Muhsin in ya fita gabadaya. Sanin halin Suhaila ba tashi za tayi ba yasa Najib ya tashi ya riko hannun ta su ka nufi daki. Da kyar ya samu ya lallabo ta ta amince da tafiyan. Ko bakomai ta yi missing mamin ta da kuma su suraj Amma wlh ta so nuna wa Muhsin iyakar shi.

Karamin veil in ta ta dauko ta yafa, Najib ya dauko mata akwatin ta su ka nufi motan. Su meema har motan su ka rakata, shiga tayi ta buga motan sannan ta dauko wayan ta ta fara danne danne. Shi dai Muhsin kala bai ce mata ba har su ka fita kaduna. Sanin in ya mai da ta ta canjo gyale ba za ta dawo ba yasa ya tamke bakin shi. Ba karamin gudu ya ke shararawa ba.

Kaman daga sama ta ji ringing in wayan sa, earpiece ya sa ya dauka. Yanda ya ke magana cike da natsuwa kuma a hankali kadai ya isa tabbatar mata da wa ya ke magana. Kaman an caka mata kibiya a zuci haka ta ki wurin ya fara mata zafi kafin kace mai wani zufa ya rufe ruf. Muhsin ko da bai San halin da ta ke ciki ba sai kara kwantar da murya ya ke yana fadin. "Am very sorry dear nima na so ganin ki but na yi dare sosai kuma ban son tukin dare Amma kuma in kince in zo ai sai in zo koh" ba tasan mai Rahman ta fada ta dai ji yana dariya yace " to menene a ciki dan na wahala akan ki? Kin Manta ance ABINDA KAKE SO shi ke wahalar da Kai" kawo i yanzu Suhaila gabadaya ta kawo wuya. Da sauri ta makala ear piece tana sauraron wakan Senõrita na Shawn mendes da Camilla Cabello. Nan ta ke ta fara relating wakar da rayuwata da ke tayi believing samun peace of mind a wurin tuni ko ya saukar mata da duk wani damuwa. That is what music do to her, she finds peace and comfort there, she feels every inch of the lyrics...

Tafiya tayi tafiya kawai sai dago kanta tayi ta ga mota ya tsaya bai tafiya. Sai dai abinda ba ta gane ba shine parking Muhsin in yayi ko kuma matsala ta samu. A hankali ta Kai duban ta gare shi, four eyes su kayi dashi, yarrr! Abinda ta ji har jinin jikin ta kenan da sauri ta dauke idanun ta hade da runtse tana fadin My God! A zuciyar ta. Muhsin ko tsaki ya ja na bin ta da harara yace "Allah ya wadaran na ka ya lalace, wato i should dealt with it right?" Sai lokacin ta fahimci moton ne ta samu matsala. Yatsun hannun shi ya hade wuri daya yana fidda huci mai zafi. Tayan da yayi faci ya dubo. Karfe taran dare ya San da wuya ya samu mai faci, da ma sun isa Kano ne to da sauki, Amma a wannan kauyen ina da sake. Ya San ba komai ya jawo mishi abun ba sai go slow in da ya tarar tsakanin  kaduna da Zaria a sanadiyar gyaran da ake a hanyan.

Duk da gudun da yayi da ga baya dole ya tsagaita gashi dole zagaye yayi ta wani kauye duk gudun bin hanya Amma duk da haka bai tsira ba. Nan take kuma ya samu kanshi da godiya ga Allah samun labarin accidents in da aka yi a hanyar zarian, sai dai kawai muce Allah ya ji kan wadanda su ka riga mu gidan gaskiya.

Ganin zama ba abinda zai kara mai ya sa shi neman mafita Kai tsaye cikin kauyen ya nufa. Ganin haka da sauri Suhaila ta bude motan ta bi bayan shi ba Wai dan tana tsoro ba Aa ta dai San is not safe zaman ta a motan ita daya ne. Ko da ya waiwayo ya ganta kala bai ce mata ba ita ma hakan. Tafiya su ka dinga yi kafin ya samu da tmby da kyar su ka gano wani mai faci. Wata sabuwa, Sam mutumin ya nace shi fa in dare yayi bai aiki duk ko kudin da za a bashi. Kasa magana Muhsin yayi dan takaici ga dukkan alamun yaron akwai taurin Kai, gashi ance duk garin shi kadai ne. Mahaifin shine ya ji sa'insa da ke afkuwa ya zo ya sa baki. Shima fa mahaifin murdaden mutum ne kusan shi ya daure ma yaron gindi. Amma ga mamakin mutane sai su ka ga yana umurtar yaron ya je ya mai, kodan kamala da mutunci da ya gani a fuskar Muhsin ne? Aiko tsohon ya fada yace "duk rashin kirki na na kasa maka saboda natsuwa da hankali da na gani dangane da Kai sannan ko bakomai kana tare da mace Kai abin a taimkawa ne" godiya Muhsin ya mai sosai hade da yi mishi ihsani. Ita dai Suhaila tana gefe ko uffan burin ta kawai ta jita a gida. A na gama gyaran su ka hau hanya. Nan da nan sai gasu a kano, gidan mamin su ka wuce, ita kanta Mami ba ta son da Suhaila ba sai da ta ganta. Ta ko ji Dadi sosai ko bakomai yau daya Muhsin ya dan faranta mata.

ABINDA KAKE SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang